NI AYS NAKE SO Part 3
��
�� *NI AYS NAKESO*��
������
.
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
_We dont just entertain and educate we also touch the herts ƙf readers_
.
.
_WRITEN BY Princess Eshat Aysm_
.
.
In Dedication to *ABDULLAHI YAHYA SA'AD ZARIYA*
A.Y.S
Page 3
.
*ZULI ILYASU*
Naga sak'on ki, _hhhhhhh ai wannan yafi shimfiɗar mijina daɗi, kuma abubuwan da suke ciki yafi wancan, idan kika bari kikayi missin baki karantaba ba ruwana, lolx_
*WANDA YAKE NEMAN BOOKS D'INA DUKKA ZAKU SAMU ANAN BASAI KUN MUN MAGANABA*
http://Eshataysm.tk
http://Eshataysm.tk
.
http://Eshataysm.tk
.
.
.
Tana shiga wajen Ammi suka tuntsire da dariya, Ammi ta ce "oh ni Amina Allah yabani 'ya, yanzu ɗaurin zanin ma sai kin tikuikuye shi, wannan ai abun kunyane ma".
Zunɓura baki tayi saura k'iris tafara kuka, Sadiya tana dariya ta ce "Ammi wannan ɗaurin zanin ai yayi".
Duk haɗiye dariyan su sukayi, yanzu sai ta cika musu gidan da kuka babu gairi babu dalili.
.
.
Sun gama cin abinci sunyi Sallah Abbah yashigo, da nutsuwa ya dube ta ya ce "Nafara wasa dake ko, duk ranar da kika k'ara shiga motar wani zakiga yanda zanyi dake, sai kin gwammaci ruwan yayi miki duka".
Ammi ta ce "me Maman taka tayi, yau dai anji kanku".
Murmushi yayi baice komai ba ya nufi ɗakin shi.
"Ke kuma motar wa kika shiga"?
Ammi ta tambaya,
"Ruwane zaimun duka....
Tsawa ta daka mata, "ki rasa wajen fakewa sai motar wani, kedai kin ɓata wayonki, natabbata Hajara bazata iya haka, tsaya ma kiji, idan bakiji tsoron Allah ba zakiji tsoron abunda zai miki, aduk lokacin da mace dana miji suka keɓe to dole akwai sheɗan a tsakanin su, kin tabbata babu abun da yayi miki".
idon ta narai2 ta ce "Wlh Ammi baimun komai ba".
"to kada kisake, kuma azamanin nan idan da kin haɗu da ɗan yankan kaifa, Allah ya kiyaye".
Tsoro duk yakamata, tayi alk'awarin bazata sake wannan kuskuren ba, har magriba suna zaune Ammi tana musu wa'azi.
.
.
koda dare tayi ɗakinta ta wuce tanaso ta kwanta, tunda ta ɗau wayar ta aɗakin su Hajara taje tayi kwanciyar ta.
Harta fara bacci ta tuna da Abdullahi, tashi tayi ta zauna ta ɗau wayar ta.
Still bataga post ɗinshi ko ɗaya ba, tsaki taja "to wai ina ruwana dashine".
Latse2n ta tagama taja bargo ta kwanta, dak'yar ta samu tayi bacci, da asuba tana sallah ta sake hawa, wani ajiyan zuciya tayi me k'arfi, sunan nashi tagani yayi post masu yawa, duk saida tabi ta karanta su, daɗine ya kamata, ganin sunan kaɗai yana sata farinciki, bata ankara ba taji ana buga mata k'ofa, da hanzari ta ɓoye wayar, ko ba'a faɗaba tasan Abbah ne, "yauma nayi laifi ban futa da wuri ba kenan".
Ta faɗa a ranta tana k'ok'arin buɗe k'ofar, shiɗinne kuwa, kallon ta yayi naɗan sakwanni ya ce "Mamana yau bakiyi karatu ba".
Ta langaɓar da kai ta ce "Abbah na kaina ne yake ciwo".
da tausayawa ya ce "muje kisha magani".
A falon Abbah duk k'annan nata suna ciki kowa da Qur'ani a hannun shi, duk suka gaishe ta, ta amsa tana ta kalan tausayi kada Abbah ya gane lafiyan ta k'alau, zama tayi a kusa da Sadiya Abbah kuma yaje ɗauko mata magani, ɗan dungurin ta Sadiya ta yi tace "kedai Abba yana biye miki, da wanine da yanzu yasha duka".
ta ce "ke nifa kaina ke ciwo, magani yaje ɗauko mun".
"yaushe kan naki yafara ciwo, to idan kikasha magani ciwon gaskiya zakiyi".
Ta zaro ido "da gaske kikeyi, to lafiya ta k'alau nikam".
duk suna jinsu suka kwashe da dariya.
.
.
Saida suka gama aikin gidan tas suka nufi wajen Ammi, gaishe ta kawai sukayi suka nufi kitchn.
Aisha ta ce "Abdullahi yahau fa".
Dukkan su suka washe baki, "me yahana shi hawa jiya"?
Hajara ta tambaya.
"ina zansani, ni bantaɓa magana dashi bafa, ko grup ɗinma basu san da wata Aisha ba".
Ta faɗa tana dariya, suma dariya sukayi, Sadiya ta ce "Amma ke ɗinnan.... Ki misi magana kawai".
Hajara tayi caraf ta ce "me zatace mishi, kawai munsan yana burgemu basai anmishi magana ba, yaje ma ya
raina mana ke, shareshi kawai".
Tace "wallahi kuwa".
ɓata rai Sadiya tayi ta ce "kuma idan baki ganshi ba kada kisake mun maganar shi, wannan ma girman kai ne".
"ke ni nake girman kan".
"kiyi hak'uri".
Bawanda yasake magana suka ɗaura girkin rana, *HAD'IN SALAD* Suka farayi, suka yankashi da albasa, tumatir, gurji, karas ɗin kuma suka kankareshi suka haɗa waje ɗaya, mai suka ɗan yaryaɗa masa sai magi, suka juye suka kai wa Ammi.
Kafin taci abincin rana shi take ci, yana k'ara lafiya, yana saita ciki, me hawanjini ta yawaita ci zata nemeshi ta rasa, kuma gashi bawani kuɗi zaki kashe ba.
Zaki iya yin na zogale kuma zaki iya coslow duk yana k'ara lafiya da ciko da mace.
Jalof ɗin shinkafa da kwakwa sukayi suka juye a flask suka shiga wanka, komai tare sukeyi babu abunda Ammi bata koya musu ba, idan ana hutun makaranta ba ruwanta da aiki.
.
.
.
.
Iskane yake kaɗawa ga wani k'amshin k'ada dayake tashi, dayake garin damuna ne, Abbah yana kishin giɗe yaji ana k'wank'wasa musu k'ifa, Jaridar hanunshi ya ajiye ya futa.
Faruq yagani tsaye a wajen, yasha manyan kaya harda hula, fuskarnan sayau ga fara'a a tattare dashi, kallo ɗaya Abbah ya mishi ya gane shi, hanu ya mik'a mishi su gaisa amma sai yaga ya tsuguna har k'asa yana gaishe shi, Abbah yayi murmushi ya amsa cikin sakewa.
Faruq ya susa kai yace "nazo wucewa ne nace bari na tsaya mugaisa".
Abbah ya faɗaɗa fara'ar sa ya ce "ka kyau ta, Allah yayi albarka, nagode sosai, a garinnan kakene"?
sunkuyar dakai yayi yana murmushi "muna ɗan bayanku kaɗan, gidan Alhaji Muhammad Buzawa".
"au wanda yarasu ko, kaine UMAR FARUQ kenan, nasanshi sosai abokina ne".
shidai Faruq murmushi kawai yakeyi, burinsa yaga Aisha don ko bacci be iyayi ba yana alla2 gari ya waye yazo ya ganta, wannan dattijon kuwa bai isa yace wajen ta yazo ba, gara ya lallaɓa shi su saba a hankali...
tunanin shi ne ya katse jin Abbah yana cewa kashigo daga ciki nanma ai gidanku ne".
ya ce "idan nadawo zan shiga yamzu ana jirana".
daganan sukayi sallama ya tafi.
http://Eshataysm.tk
hahaha thank u dear
ReplyDelete