NI AYS NAKE SO Part 4

������
      �� *NI AYS NAKESO*��
                 ������

.

*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
_We dont just entertain and educate we also touch the herts ƙf readers_

.

.



_WRITEN BY Princess Eshat Aysm_

.

.

In Dedication to *ABDULLAHI YAHYA SA'AD ZARIYA*
A.Y.S



Page 4

.




.


Gaisuwa ta musamman gareku
*HALIMA BICHIKI*
*HAJARA 'YAR LUKUTA*
_ONE LOVE *ILYSM*_❤



.
.

*my blog*
www.Eshataysm.tk















.




.






.



"ya zanyi da rayuwa ta, Allah ya jarabceni da soyayyar wanda bansan shi ba, waye shi".
Ita kaɗai take juyi tana sumbatu, "ko bacci nayi sai nayi mafarkin shi, me hakan yake nufi, zanbi shawarar Sadiya, yau zan mishi magana".
Pillow ta jawo ta rungume tana karanta post ɗin shi har bacci ya kwashe ta, kamar dama baccin jiranta yakeyi ta fara mafarkin da takeyi, Mutum ne tsaye a gabanta amma bata gani fuska, cikin wani kasalalliyar murya ya ce "Nine Abdul, inasonki kada ki canza ra'ayinki akaina.... Yana gama faɗin haka yaja hanun ta sukayi sama kamar iska.

A ruɗe ta farka tana salati, agogon dake manne a ɗakin ta duba, k'arfe 1:5am, tayi ajiyar zuciya ta ciro wayarta a caji ta haura fcbk, ko sunan shi taji zata samu kwanciyar hankali, jin mafarkin takeyi har cikin jikin ta.

.


.


Abun mamaki yananan online, "to kodai aljani na haɗu dashi".
Kawar da wannan tunanin tayi, tunanin ta yatsaya akan tayi masa magana koda sallama kaɗai.
Sakwanni biyu dayin Sallamar ta ya maido mata da martani, rasa abunda zata faɗa mishi tayi
Sai kawai ta ce "Dama gaisuwa ce".

"nagode da gaisuwa".
Abunda ya faɗa kenan.

Shiru tayi ta zubawa sak'on ido, can dabara ta faɗo mata.

"awani gari kake"?

"kiyi hak'uri bangane wacece ba".

Kamar bazata bada amsaba ta daure ta ce "Baka ganin sunana a rubuce, ko me kake nufi"?

"ina gani, a zaria nake".

"ok baka bacci ne"?

"yanzu garina ya waye, ke a wani gari kike".

Dariya tayi aranta tanajin wani sanyi yana ratsata.

"manta da wannan tambayar taka, banida gari, inajin bacci, Gudnyt".



Tana turawa ta sauk'a.
Batasan iya adadin data ɗauka tana tunanin shiba, bacci ɓarawo ne ya sace ta.



.

.

Tana Sallahr asuba kamar masifa ta haura fcbk, ta matsu taga sak'on da ya turo mata.
"ok".

Shine kawai abunda ya rubuta, haushi ne ya kamata taja dogon tsaki.

Har tayi jifa da wayar ta ɗauko ta tura "morning".

Kafin ta ajiye taga ya turo "mrng dea".
Daɗa gyara kwanciya tayi, ta manta da wani karatun da sukeyi da asuba.

Ta ce "mutane suna sonka da yawa, meyasa".

Saida yayi dariya ya ce "Babu wani dalili".

Tace "yayi kyau, wannan love msg ɗin dakake turowa, yanamun daɗi, mawa kake turawa"?


Nanma dariya yayi yace "banida budurwa ai, turawa kawai nakeyi, bakiga sunan
Group ɗinba".

Uhm "Babba dakai bakada budurwa, inaganin chrtn ɗin 'yanmatan naka a group ɗin, bana maganane kawai, ko in lissafa su".

"topah, inada masoya dai, amma banida budurwa, yarinya ɗaya na taɓa so, kuma tayi aure, tundaga kanta bansake soyayyaba, sunanku ɗaya da ita".

cikin tausayawa ta ce "ayyah Allah ya kawo wacce tafita".

Hira suke sosai, lokaci gudu ya bata labarinsa, anan tasan Abdul ɗin nata shine *AYS*
Sallama yamata zai sauk'a, sai a lokacin ta kalli agogo, k'arfe 9 ta gota, a zabure ta mik'e tayi waje, tana tafiya tana tunanin me yahana azo a tasheta.

Tana isa k'ofar kitchn sukaci karo da Sadiya, tun kafin tayi magana ta ce "Abbah fa ya tafi kike ta rakuɓe2, shi yace kada a tashe ki bakida lafiya".
D'an murmushi Aisha tayi tawuce wajen Ammi.

Tundaga ranar ta manta da wani futan asuba, dai2 wannan lokacin suke shan hiransu da AYS, cikin kwana biyu suka saba sosai, kusn sati rabonta da haɗuwa da Abbah, hankalin ta yakasu kashi biyu, tafi zama a ɗaki ita kaɗai.



Yau takasance Asabar Abbah yana gida bazai futa ba, bayan sun gama karatu yacewa Hajara "Me yake damun mamana ne, har yanzu kanta bai bar ciwo ba"?
Hajara ta kalli Sadiya ta ce "Aunty bata warke ba ko"?
Abbah ta kalla itama ta ce "a k'irata ko Abbah".
Jafar yayi caraf ya ce "wallahi Abbah lafiyan ta k'alau".

Abbah yace "je ka k'iramun ita".

da gudu ya tafi, tura k'ofar kawai yayi ya shiga, ganin shi  tayi ya tsuguna a gabanta, da sauri ta ɗago tana k'ok'arin ɓoye wayar, amma ina har yagani, harara ta zuba mishi ta ce "me ya kawoka ɗakina".
Da dariyar shi ya ce "Aunty ansai miki wayane, don Allah bani nayi Game".
Kunnenshi ta kama ta murɗa da k'arfi, "kana jina ko, idan naji kafaɗawa Abbah ka ganni da waya sai na yanka kunnem ka".
Yaji zafi har yana hawaye ya ce "bazan faɗa ba". Kaɗa kai tayi ta ce "kama faɗa".
Harya mik'e zai futa yadawo ya ce "Aunty Abbah yana k'iran ki".

Ta ce "tsaya muje tare".




Kusa dashi taje ta zauna ta gaishe shi, yace "Mamana har yanzu baki warke ba"?
Kaɗa mishi kai tayi, Jafar ya marairaice fuska yace "Abbah nima kasiya mun waya nayi Game".
da sauri Aisha ta watsa mai harara, su Hajara me zasuyi inba dariya ba, Abbah ya ce "kai kuma waya kake so? Zan siya maka amma sai kayi karatu".
Kallon Aisha yayi ya ce "Aunty na faɗa"?
A ruɗe tace "kafaɗi mene, nifa banason sharri....
Abbah ya katseta, "faɗamun yarona".


Jafar yace "Aunty ma naganta da waya, irin nata zaka siyamun, ammafa ta murɗamun kunne tace kada nafaɗa maka".

Lokaci guda fara'ar dake mak'ale a fuskar Dady ya ɗauke, binta yayi da kallo na tsawon lokaci me cike da takaici, yasan Jafar baya k'arya, duk abunda ya faɗa to babu kokonto.

"Bani wayar".

Bakin ta na rawa tace "Abbah k'aryafa yake mun".

Mari ya tsinka mata har sau biyu, wani walk'iya ta gani kafin idon ta ya buɗe, cikin masifa yasake cewa b
"bani wayar".
Da sauri ta ciro a cikin zanin ta ta mik'a masa.

"waye yabaki waya"?

Cikin in'ina ta ce "siya nayi".

Baice komeba ya mik'e yayi ɗaki, da sauri k'annan nata suka nufota, Al'ameen har yana kuka, suma kamar zasuyi kuka, Sadiya ta ce "kiyi shiru Aunty, kukannan zai saka miki ciwon kai".

Kallon su tayi dukan su kafin ta ce "Ba Abbah ne damuwata ba, AYS nake tunani gashi ko numban shi banida shi".

Hajara tsaki taja "Aunty wallahi bakiyi ba, baki tunanin abunda Abbah zai miki ma".
Kukan ta taci gaba dayi, dak'yar suka jata sukayi wajen Ammi, fuskar Aisha duk ta kunbura, shatin wajen da Abbah ya mareta abunka da Farar mace, Ammi tana ganin ta tahau salati "ko ban tambaya ba nasan laifi kikayi, kece babba amma kullum kece me laifi, anya kanki ɗaya kuwa"?
Jafar dake laɓe a bayan Ammi, tun lokacin da yaga an mare ta ya gudu wajen Ammi, shi yafaɗa mata abunda yafaru "Ammi kuma ya kwace wayar".
buge bakin shi Ammi tayi "saina saɓa maka akan wannan surutun naka".
Faɗa tayi ma Aisha sosai ta gargaɗe ta da kada ta k'ara ganin waya a hanun ta.







.

.



.




Bayan kwana biyu
*GARIN ZARIYA*

.

.

"Abdul me yake damun kane jiya da yau, gaba ɗaya ka canza".
A kasalance ya ce "Umma babu komai, ban samu nayi bacci bane".
Shafa kanshi tayi ta ce "yakamata kaje kayi bacci yanzu, idan kun rik'e waya kamar baku duniya tayaya zakayi bacci kana kwana danna waya".
Murmushi yayi "to Umma zanyi yanzu".

tunda ya koma ɗakin yatasa waya agaba da kallo, "Ina wannan yarinyar ta shiga, bansan na saba da ita hakaba".
Hanu yasa ya kama kanshi, yanajin yanda yake sarawa, "yaya kamannin ta yake oho,".
Hirar tasu yayi ta karantawa, shi kaɗai yake sashi jin ɗan sanyi aranshi, bai taɓa kewar mace hakaba, ko ba'a faɗa mishi ba yasan soyayyar ta ne yakamashi


Comments

Popular posts from this blog

Australian Visa Application information: Visa Types & Requirements

[Sunnah] What Muslim Should Observe On The Day Of Eid

Canada Immigration: How To Apply For Canada Permanent Resident Visa