SONE AJALINA 7 to end

🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈
*SONE AJALINA*
🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
By 💅AISHATU SALIHU BICHIKI💅
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Page 7
.
.
.
.
.
Komai aka sanyawa lokaci to fa zai zo har ma ya wuce, domin yau da gobe babu abunda ya bari.


To haka abun yake su Hafsat anyi candy inda ta karb'i kyautuka da dama haka Haulat ma, suka dawo gida cike da farinciki, haka a ranar aka kawo lefen Hafsat, Sultan ya taka rawar gani sosai domin komai me tsada yasaka.
Sultan ne zaune a gaban Baa yana masa bayanin yanda bikin zata kasance domin ya gayyaci manyan mutane.
"Ina Junaid ne Momyn ku tace tare za'ayi bikin naku amma naga bai yi taken action akan abun ba, je ka k'ira mun shi naji me yake jira".
Mik'ewa yayi ya nufi d'akin Junaid.
Jin motsin ruwa yasa yagane wanka yakeyi don haka ya zauna domin jiran shi yafito.
Idon shi ne yakai kan screen d'in wayarsa, photon Hafsat ne akai ta zunb'ura baki kamar zatayi kuka da uniform ajikin ta.
A take yaji wani mummunan fad'uwar gaba bai san lokacin da ya shiga gallery ba, duk pix d'in Hafsat ce yawanci ranta a b'ace ne guda d'aya ne yaga tana dariya.
wani kishi da bak'in cikine ya turnuk'e shi ya ajiye wayar sai huci
yake yi, a haka Junaid ya fito ya same shi kallo d'aya ya mishi yagane a kawai matsala, wayar sa ya kalla yaga ba'a nan ya a jiye ta ba, yasa hanu ya d'auka ya dubi Sultan da ya had'a rai yana binshi da kallo.
"Me
kake nema mun a d'aki, kasan baka da lafiya me yasaka mun bincike? ina ta k'ok'arin kauce wa duk wani abun da nasan zai b'ata maka rai amma sai da ka kalli abun da kasan zai b'ata maka rai, Hafsat taka ce har abada nasan matsalar ka kenan kake ta huci haka, na haramta wa kaina ita tun ranar da kazo da albishir d'in zata aure ka, kada kadamu da maganar daka ji inayi wa momy abunda ya wuce muke tattauna wa akai, bana son rasaka zan iya sadauk'ar da komai nawa na sama maka farinciki Sultan".
Sultan yayi murmushin nan nashi ya mik'e yace "kada kadamu, Baa yana nemanka".
yana fad'in haka yasa kai yabar d'akin.
Junaid ya zauna dishan a wajen ya kama kanshi da yake ta sarawa ya fara sumbatu "Ban san ina zan tsoma rayuwa ta ba, kullum soyayyar ki k'aruwa takeyi a cikin raina, ban san yaya zanyi in cireki a raina ba, why Hafsat zaki shigo mun rayuwa ta yanda bai dace ba, why".. sai kuma ya rushe da kuka "Mutuwa ta tafi mun sauk'i a kan narasa ki, ta yaya zan yi rayuwa babu ke, dawa zan rayu to...?
Babu amsa dole
ya daina sumbatu yayi kuka me isan kafin ya rarrashi kanshi, ya fad'a toilet ya wanke face d'in ya nufi k'iran Baa.
"Dama maganar auren naka ne naji kayi shiru abu saura kwanaki".


"Baa ai an janye wannan maganar, mom ta hanani nema da tun tuni nabar k'asar nan ta ce sai anyi bikin Sultan zan tafi". "To Allah yasa jinkirin ya zama alkairi".
"Ameen Baa".
Sultan kam gidan su Hafsat ya nufa ko hankalin sa zai kwanta.
Haneefa badai surutu ba kamar ana saka mata batir.








"Aunty wlh naso a kano akayi bikinnan na gayya to k'awaye na da yanzu gidannan ya cika da mutane".
"To sarkin surutu ko za'a tattara a koma chan ne saboda k'awayen ki". Momyn su Haneefa ce tayi maganar.
"Mom kema kinsan bani da suru....
Inna datake ta yab'a lalle a hanu ta ce "
Fad'i abun ki yarinya bata da k'awaye kamar me aljanu".
Zunb'ura baki tayi ta kwanta jikin Mom tana mata shagwab'an da basu jima me take cewa ba.
Haneefa ta tuntsire da dariya "Aunty wlh baki sanin kin girma shagwab'a ta miki yawa, koda yake tsohuwa ce ta sakalta ki, idan ba haka ba menene abun wani kuka anan, idan kinyi auren zamuga mawanda zaki rik'a narkewa ai...
Mom ce ta tabita zata buge bakin ta tashi ta fita da gudu tana dariya, karo sukayi da Sultan da yake k'ok'arin shigowa ai kuwa ta shige bayansa ta na cewa "Mom kiyi hak'uri".
Dariya yayi daya gane laifi tayi yaja hanunta suka shiga cike ya ce kidaina tsokana nasan tsokana kikayi".
Ya russuna ya gaida Mom yajuya ya gaida Inna.
ya juya kallon sa ga Hafsat da tayi kicin2 zata yi kuka, shi dariya ma take bashi abu ba abuba tayita kuka wa mutane.
Mom mik'ewa tayi dama wanka zata shiga.
Da sauri ya koma kusa da ita yana tambayar ta waye ya tab'ata.
Haneefa me zatayi inba dariya ba ta ce "wlh ashe ku kuke sakalta ta, babu fa abunda aka mata".
yace
"Hafsy na wai haka"?
"Inna muje na wanke miki lallen yayi yanzu".
Ba musu ta mik'e suka fita.
"Hafsat tambayar ki zanyi, yaya kuke da yaya Junaid Don Allah"?
Banbarak'wai taji tambayar "Ban gane me kake nufi ba yaya Sultan".
Ya dafe kai "i mean a makaranta kukanyi magana ne"?
Ta zuba masa ido na tsawon lokaci shima d'in ita yake kallo ta ce "yakan koya mun karatu idan bangane lesson ba, bayan wannan babu wani abunda yake had'amu... yauwa sai kuma yakan yimun bulala idan yabani assgnment banyi ba, mutumin da bashi magana yaushe har zanyi magana dashi".
Zaro Ido yayi "Bulala yake miki"?
"kuma fa ni kad'ai yake duka bai tab'a zane kowa ba sai ni, duk gidanku suna sona shi kad'ai ne bashi....
Dakatar da ita yayi a d'an tsawace ya ce "Auren mu saura kwana 2 amma.. sai kuma yayi shiru.
"Amma me"?
"Amma duka yak'are".
yafad'a yana dariya, itama dariya tayi ta ce "Gabana fad'uwa yakeyi tun jiya amma Innah tace nafara jin tsoron auren ne".
yaja hancinta ya ce "kuma kin yarda tsoron ne"?
Ta rufe fuskanta tana dariya.
"Na zone ki fad'amun ko akwai abunda kike buk'ata na hidimar dazakiyi, nasan waccan kud'in sun kasa miki".
"yaya sun isa, walimah kawai zamuyi Abbah bazai bari ayi wani bidi'a ba, anjuma za'a zo amana lalle da wanke kai gobe muyi walimah shikenan kawai".
yayi murmushi ya ce "Jibi kuma ayi me"?
"kai yaya".
yayi dariya ya ce "zan wuce ki kularmun da kanki".
"to yaya kaima haka".









Tunda ya koma yake tunane2 a hankali kanshi yafara ciwo, lokaci kad'an jikinsa yayi zafi sosai kuma still tunanin da yake bai daina ba, ciwon da yake ji ma baya gaban shi ko kad'an.
wajen dinner ne aka ga bai fito ba Momy ta ce "Haulat k'ira shi kwana biyunnan da yunwa yake zama na rasa me yake damun sultan".
Junaid ya ce "Nima na matsu ayi aurenan ko zai koma normal".


Baa ya girgiza kai kawai bai ce komai ba.
A hautsine ta dawo tana kuka "yaya sultan bashi da lafiya sai rawar sanyi yakeyi".
su duka suka mik'e suka nufi wajensa, ba b'ata lokaci aka kaishi asibiti.
.
.
.
.
Wacce Mom ta mata wayane tazo tun daga me duguri, gyara ta mata normal wanda ake k'ira da gyara d'aya tamkar ga dubu, lallen ma simple a ka mata manyan zane irin na 'yan me duguri, kitsone dai aka yaryad'a shi k'ananu tayi kyaw sosai sai shek'e takeyi kamar zinare.
Nan fa daru ya tashi Haneefa ta fara bori dole itama a gyarata haka.
Akayi rarrashin akayi dukan amma fafur tak'i tayi shiru ita fa sai taga tafara shek'i irin na Aunty Hafsat, Innah kuwa ta ce a mata dole itama haka aka mata dilke aka yarfa mata kitso da lalle, tayi kyaw sosai kamar ta had'iye kanta idan ta kalli madubi.
Su Ya Haidar sukayi ta tsok'anan ta wai itama a d'aura mata aure da limamin anguwan tunda tafito kamar amarya.
Basu suka gama abunda zasuyi ba har kusa asuba don haka ba wanda halin da sultan yake cike a gidan.
suna brkfst Abban su ya shigo jiki a sanyaye ya ce "Ashe yaronnan bashi da lafiya baku fad'amun ba"?
Abincin da takai baki ta tofar ta ce "Yaya sultan ko, naji ajikina Abbah na kasa gane me nakeji ne, don Abbah kace mishi
gobe ne fa auren idan na rasashi mutuwa zanyi wlh Abbah".
Sosai take kuka, bata san me suke cewa ba tayi waje da gudu yayi dai2 da fitowar Yaya Junaid zai koma asibitin ya hangota, jan glass d'in yayi ya ce "ina zakije"?
"plx uncle ina yaya sultan"?
Tausayi ta bashi ya bud'e mata front ya ce ta shiga, bata musa ba tashiga.
Jikinshi ta kwanta tana kuka tana ta k'iran sunan shi baima san tanayi ba saboda jikin nashi yayi tsanani zuciyar tashi da ba'a so ta buga sai da ta buga, allura suka mishi ya samu yayi bacci.
Ahaka su Innah suka iso suka sameta ba wanda bai tausaya mata ba awajen musamman Haneefa da itama taketa rusa kuka, da k'yar aka jasu aka fitar dasu.
*WASHE GARI*
Rana bata k'arya sai dai uwar d'iya taji kunya.
Dubban Mutane sun hallara kamar yadda aka gayyace su.
Abokan Baa da Abbansu Sultan Duk Sun Hallara Hardaga K'asashe Daban2.
Sun yanke shawarar ayi auren tunda mutane sun taru.
Junaid aka bari a jikinsa sai yaya khalifa.
.
.
saura baifi 2mnt a d'aura ba sak'o ya shigo wayar Baa, a kid'ime
ya nufi asibitin baiyi wa kowa magana ba.
kukan dayaga Junaid yanayine ya tabbatar masa da gaske SULTAN ya MUTU.
.
shima kuka yashiga yi wiwiwi kamar k'aramin yaro, d'aya b'angaren kuma anata k'iransa a waya ko b'a fad'a ba yasan masu d'aura aure ne shi ake jira, cikin kuka ya shafa fuskan Sultan ya ce Allah yajik'an ka d'an albarka.
fita yayi ya koma gefe ya k'ira amininsa Muhammad Jut mahaifin Hafsat.
"saifa hak'uri Allah yayi wa sultan rasuwa".
"what! Kasan me kake fad'a kuwa"?
"Nasani Abokina, ashe taron mutanennan mutanen sa ne... kuka ne ya kubce masa yakasa magana.
*INNALILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJIUN*
Abunda muhammad jut yaketa nanata wa kenan.
"calm down aboki na, tunda hakane angama shirya komai me zai hana a d'aura da JUNAIDU".
"Nima nayi wannan tunanin, a d'aura kafin a sanar dasu zancen mutuwar".
.
.
.
Haka kuwa akayi, aka d'aura auren JUNAID da HAFSAT akan sadaki naira dubu d'ari.
.
.
.
Baa yana gama wayar ya koma d'akin da sultan yake, Gaban gadon yanufa ganin JUNAID ya k'ura masa ido baya ko k'iftawa
"Baa zo kagani naga kamar yana motsi".
.
.
.
INA MASOYAN JUNAID SAI KU KWASHI SHOCKY!
*MASOYAN SULTAN NIDAI NAWA NATAYA KU KUKA*
HAHAHAHAHA
[7:00PM, 8/12/2017] Aysha Bichiki: 🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈
*SONE AJALINA*
🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
By 💅AISHATU SALIHU BICHIKI💅
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Page 8
.
.


















Da sauri Baa ya matsa yana zare ido kamar wanda yayi laifi.
ya matsa da kunnuwan sa wajen k'irjin Sultan, a hankali sautin numfashin sa ke fitowa alamar yana raye.
yajuya dubansa ga Junaid ya ce "yanzu ya za'ayi"?
cikin rashin fahimta Junaid ya ce "zanje nak'ira Doctor...
"No! ina nufin maganar aurennan... sai kuma yayi shiru ya ciro wayar sa, shi dai Junaid binsa kawai yayi da kallo. "Ina fata ba'a d'aura aurennan ba domin ya farfad'o".
Banji me aka fad'a ta d'aya b'angaren ba naga Baa ya zabura ya mik'e "ok ina zuwa yanzu". Nan ya kashe wayar har yanzu Junaid shi yake kallo.
"JUNAIDU! an d'aura auren dakai"...
A Rud'e yabi Baa da kallo ya kasa magana, Baa bai bi ta kanshi ba yadubi Sultan ya ce "Nasan bakaji na sultan balle ka gane magana ta ina fatan Allah ubangiji ya d'agamun kafad'un ka, na gode wa Allah da ya barmun kai a raye".
Junaid k'iran likita yafita yi yafara tunanin Baa d'in ma yana buk'atar a dubashi, tun lokacin da ya ce an dakai aka d'aura auren yagane ciwon sultan ya juya shi.
Atare suka shigo da likita yayi dube duben shi ya tabbar sultan na raye dogon suma yayi, sai dai zuciyar shi tana buk'atan hutu kafin yadawo hayyacin sa, za'a masa allura yanzu yasamu bacci na tsawon awa 24, dazaran ya farka insha Allahu zai dawo normal.
Abu kamar wasa mutuwar sultan yafara bazuwa yakai har kunnen Hafsat,
.
"Doctor kad'an yi chkn wannan d'inma.. ya nuna Baa yafad'a yana susa k'eya.
wani wawan kallo Baa ya mishi ya ce "kaci ubanka nace, haukace wa nayi ko? Tunda ya farfad'o yanzu zaka saketa a d'aura dashi".
Maganar tashi ta sake baiwa Junaid dariya ya farayi k'asa2, shi kan shi Doctern dariya yakeyi.
Baa ya bud'e baki zaiyi magana wayarshi tafara ringn, ganinan zuwa kawai yace ya watsa wa Junaid wani kallo kafin ya ce "ka kula dashi ina zuwa".
Tunda ga nesa mutane suka fara tururuwan gaishe shi, wasu suna cewa yaya me jiki wasu suna cewa yaya hak'uri, duk amsa d'aya yake basu
*ALHAMDULILLAH*
Kutsawa yayita yi har ya iso wajen Amininsa."
"Kaji wani abun al'ajabi yanzu yaya za'ayi"?
Baa ya ce "zamu sa ya saketa yanzu in yaso sai a d'aura da sultan d'in".
Muhammad Jut ya girgiza kai "Ba haka za'ayi ba, shi lamarin aure rikitar wane dashi kuma matar mutum ai kabarin sa, tunda abun yazo da haka nabaiwa Sultan d'in auren 'yata HANEEFA sai a d'aura yanzu".
cikin tsananin farinciki Suka rungume juna, atake aka d'aura
Auren Sultan da Haneefa.







.
.
.
BAYAN AWANNI
.



"Ohhh ni wannan lamarin da d'aure kai, wannan ai kuskure kuka tafka, memakon kumayar masa da matarsa sai ku aura masa wacce bai santaba, yaya zakuyi da soyayyar da suke fama dashi ga yarinya sai suma takeyi wa mutane".
Abbah Ya kad'a kai kawai ya ce "haka Allah ya k'addara hak'uri zatayi a hankali zata so wannan d'inma, ita Haneefan tasan da zancen aurene? amma tayi tawakkali, akwai wanda take so acan kano haka ta hak'ura saboda ta yadda da k'addara, kinga Inna don Allah kibar surutu duk mun rufawa juna asiri ne kuma insha Allah zai zame mana alkairi tunda bada niyyar yimusu dole mukayi ba Allah ne ya juya al'amarin sa".




Hafsa dai kukan ta taketa sha arasa wanda za'a had'a ta dashi sai wanda yatsane ta, adduar ta Allah yad'au ransu itada sultan suhuta yafi.

Haneefa ma kukan takeyi gani take kamar itace zataci amanar 'yar uwanta, tasa aranta sai tasan yanda za'ayi wannan auren ya juye.












......................................





Bayan awa 24 Sultan ya farka, a hankali yafara buÉ—e idonshi yana gani dishi2, salati yayi yafara k'iran sunan Hafsat, Junaid ya mik'e da sauri ya isa gabanshi ya rik'o hannun shi ya ce
"Sannu broz".
Ya gyaÉ—a masa kai kawai.
Likita yak'ira yazo ya duba shi yace "Alhamdlh yanzu inane yake maka ciwo".
Kanshi ya nuna dayake É—an sarawa.
Ya ce "anjuma zaka daina ji insha Allah.
daganan yagama rubuce2 ya fita.
Junaid ya matsa kusa dashi yana masa sannu.

"Ina Hafsa, an É—aura mana auren ko"?
Ya tambaya yana k'ok'arin tashi.
Sai a lokacin maganar Baa yadawo wa Sultan na cewa an É—aura auren dakai.
YaÉ—anyi murmushi ya ce
[3:05PM, 8/16/2017] Aysha Bichiki: 🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈
*SONE AJALINA*
🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
(we dont just entertain and educate, we also touch the ❤ hearts of the readers).
.
By 💅AISHATU SALIHU BICHIKI💅
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Page 10
*MUHIBBAT DURLIN ALLAH UBANGIJI YA BAKI LAFIYA 'YAR ALBARKA*
.
.
.
.

Dak'yar aka samu Hafsat tayi shiru, sai da momyn Haneefa tayita rarrashi tare da cemata idan har ta yadda aka kaita ta kwantar da hankalin ta to dakanta zata sashi ya saketa sai tadawo sultan ya aure ta, haneefa kuma bama za'a kaita ba za'a datse auren, da wannan magana yasa tayi shiru har ana d'an hira da ita.
Zagewa Momyn tayi ta gyara yaranta, duk wani tanadin gyaran da tayiwa Hafsat su biyu yanzu take musu, tasha alwashin babu wanda zai d'and'ana mata yara ya wulak'an tasu, darajar mace a gidan miji shine ta samu 'yanci, soyayya da ban 'yanci daban, duk sonda namiji zai miki matuk'ar baki nemi 'yancinki ba to fa bazaki ji dad'in soyayyar ba, domin a zuciyarsa ne kad'ai zai rik'a mutuntaki.
Bayan Sun dawo daga asibiti dak'yar aka hanashi zuwa gidansu Hafsat aka fake mishi da cewa a kwai mutane da yawa a gidan ba lallai ne ya gantaba.
Bawani Biki akayi sosai ba, Hafsat ta saki ranta sosai momy tana dad'a rarrashin ta tana kwantar mata da hankali akan dazaran tayi biyayya ta kwantar da hankalinta to sultan zai dawo gare ta.
Innah Kuka tayi sosai dak'yar aka b'anb'are Hafsat ajikin ta duk sun cika gidan da kuka lokacin da aka zo d'aukar amarya.
Sultan dai ce masa akayi sai ya warware ayi bikinsu da Hafsat, Tunanin sa duk yatafi akan Junaid ya amince an d'aura masa aure da sadiya ne ganin ba'a daina shagali ba.
Wajen Abbahn ta aka kaita yayi mata nasiha me ratsa zuciya daya sata zubarda hawaye sannan aka kaita gidansu Junaid, Sashin Baa.
Nanfa kukan ta yazamo sabo gani take kamar ta yaye rufin kanta ko zataga sultan.
zaune suke a parlour daga momy sai Baa aka shigar da Hafsat, da sauri mom ta mik'e ta rik'ota ta rungume ta tace "kidaina kukan nan hafsat, da Junaid da sultan duk abu gudane, yanda sultan zai kula dake nayi imanin Junaid zai baki kulawa shima, k'addara ta riga da ta zama fata, tun ran gini tun ran zane Allah ya k'addara
Junaid ne mijinki, kiyi k'ok'ari ki cinye wannan jarrabawar...
Baa ma nasiha yamata daganan aka wuce da ita gidanta.
Bawani k'awaye take dasu ba daga tsofin da suka kaita sai k'annen momy su biyu da Haulat, Sai Kuwa 'yan gayyan sod'i su Hajara Da Sadiya 'yan Leken Asiri Kenan.


Basu Wani juma ba suka tafi bayan sun gama santin gida aka bar amarya daga ita sai halinta.
kifuwa tayi taci gaba da kukan ta kamar ranta zai futa.
Junaid kam yana d'aki jin yanda aketa gud'a a gidan, yarasa farinciki yakeyi ko bak'inciki, shidai yasan yana cikin jin dad'i yana jinshi kamar bashi ba idan ya tuna cewa Hafsat itace matar sa.
Mom ce ta tura k'ofar tashiga tayi mamaki ganin kamar ma bacci yakeyi, duka ta d'aka masa daya sashi mik'ewa cikin sauri, "baccin me kakeyi? wazaije yayi maka gadin matar taka, kasan k'arfe nawa kuwa yanzu"?
k'arfe 11 yagani yad'an ja numfashi "haka akeyi ranar da aka kai amarya sai miji yaje, da kinbarni gobe sai naji da wuri..."
"Idan kagama surutun kashi ga ka shirya yanzu ka wuce kabar gidannan".
.
Shiri yayi yasaka farar shadda datasha aiki da bak'in zare yafito ango sak k'amshine kawai ke tashi. Mom tana ganinshi tayi dariya tace ko kaifa, kayi sauri kaga dare yayi Allah ya tabbatar da alkairi.
.
.
Gajiya tayi da kukan tayi shiru tana ajiyan zuciya, ta k'udun dune awajen har bacci yayi awon gaba da ita. A hankali ya bud'e k'ofar d'akin ya shiga, ya k'arewa d'akin kallo sannan yajuyo ga dubansa gareta yaga bacci takeyi da gaske, ya yaye mayafin kanta ganin yarufe mata fuska ya gyara mata kwanciyar yabar d'akin kamar kyaftawar ido.
kusan 2rh ya kwashe a zaune bai sani ba.
kuka ya fara ji k'asa2 mara sauti yana shiga kunnen sa adaidai lokacin da bacci ya fara fizgan shi, da sauri ya mik'e ya nufi d'akin daya tabbatar cikin sa take, ganin yanda ta runtse ido take ta kuka ne abun yaso bashi dariya kamar ba yanzu ta gama shan baccin ta ba.
Tsawa ya daka mata ya ce "menene kike kuka wa mutane a darennan, kin gama baccin ki zo kina wani b'are baki".
Dad'a b'arke wa tayi da kuka harda birgima, ya kama kanshi ya ce nidai nashiga uku, me kukan nata yake nufi, bata sona kenan lallai zan canza taku, zuba mata idanuwan nan nasa yayi, k'aramin bakin ta kawai yake kallo da yasha jambaki, ya sauk'e ajiyan zuciya kafin ya futa bai sake bi takan ta ba, kukan nata yana matuk'ar shiga ransa idan ya ci gaba da kallon ta shima zai iya yin kukan.
Kwanciya yaje yayi amma yakasa baccin kuma gani yake idan ya rarrashe ta zata iya raina shi, ji yake zuciyar shi duk a jagule.
Zuwa yayi ya rage kayan jikinsa, har ya zauna ya tuna da abincin da momy ta bashi ya kawota.
Lokacin ta daina kukan sai ajiyan zuciya take yi, sultan kawai take tunawa tana tunanin yanzu wani hali yake ciki, jin an buÉ—e k'ofa ne yasata mik'ewa da sauri don ita mungun tsoron shi takeji idan ta tuna dukan da yake mata a makaranta.
[12:31AM, 8/19/2017] Aysha Bichiki: 🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈
*SONE AJALINA*
🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
By 💅AISHATU SALIHU BICHIKI💅
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Page 11

.
.
.
.



D'aure face yayi kamar wani zaki ganin yanda take ta zaro ido, cikin takun nan nasa ya k'arasa cikin d'akin ya ajiye foodflask d'in dake hanunsa tare da flet da cokali, ya koma ya d'auko mata Bottle water da fresh milk, da kanshi ya zuba mata soyayyen indomie ne da k'wai, saboda yunwar da take ji sai had'iyar yawo takeyi duk da indomie bai dameta ba amma takasa motsi har yagama zubawa ya mik'e ya koma kan stool d'in dake jikin mirrow ya zauna ya zuba mata ido, mungun tsoron shi take ji takasa koda motsawa ne ganin baice ta ci ba.
"ko sai an baki abaki ne? kin cika wa mutane gida da kuka kin hanasu bacci har asuba ta kusa, kinsan kinajin yunwa ai saiki fad'i gaskiya".
zunb'ura baki tayi kafin tajawo abincin ta fara ci, rabonta da abinci tun ranar da aka ce mata sultan yana asibiti, don haka ta cinye tas tasha fresh milk d'in kad'an ta ajiye ta koma gefe ta zauna, ba k'aramin mamaki yayi ba ganin ta cinye, bai ce mata komai ba ya kwashe kayan ya fita dasu ya barta tana lek'ensa tana mamakin yanda yasauk'o har
ya zuba mata kuma ya kwashe.
Ranar dai babu wanda yayi bacci a cikin su, gari yana wayewa kuwa yabar gidan, wanka tayi ta saka atamfa d'inkin riga da siket ta nad'a d'an kwalin kamar goggoro, ta saka yari gold tayi simple makeup amma fa tayi kyaw sosai, gidan ta shiga zagaya wa d'akin dake kallon natane ta gane shine na Junaid an tsara d'akin sosai, gadon dake d'akin har yafi nata girma, kitchen ta duba taganshi k'aton gaske komai akwai ciki ta bubbud'e fridge d'in tayi murmushi ganin komai yaji aranta tace inama yaya sultan na aura da yanzu muna tare, nan hawaye yafara wanke mata fuska, knokn k'ofa akayi ta share hawayen da sauri taje ta bud'e, Haulat tagani suka rungume juna suka k'arasa ciki.
tad'an had'a rai ta ce "shine jiya kuka tafi kuka barni baku tayani kwana ba".
Haulat ta zaro ido ta ce "mukwana a ina? wlh yanzu ma banyi niyyar zuwaba momy ce tace na kawo miki abinci, kinsan fa boss d'innan kika aura bazaki rik'a ganina sosai ba don nasan zai iya korata".
Narai2 tayi kamar zatayi kuka ta ce "Ina
yaya sultan d'ina ya warke ko"?
Haulat ta kama baki "kinada hankali kuwa Hafsat? kinada auren kike tambayar lafiyar wani? to nidai babu ruwana kuma kiyi istigfari".
mamaki ne yakama Hafsat ta ce "yanzu kina nufin bazan auri yaya sultan ba"?
Dariya Haulat ta tintsire dashi ta ce "wannan k'azamin tunanin naki ya bani dariya, wani irin aure kuma bayan ya auri k'anwar ki, to wlh kicire shi a ranki ki rungumi mijin ki don natabbata yaya Junaid yafi sonki akan kowa, kina ganin bai damu da kowa yayi karatu ba saike, kuma in fad'a miki yaya sultan d'inma ya manta dake yanzu soyayyar su suke sha da Haneefa, saboda ke sakarai ce bazaki yi tunanin tayaya zanyi biyayya wa mijina ba kina tunanin wani wanda ya manta dake".
sosai maganganun suka sosa ran Hafsat Sai yawo yake mata a zuciya duk da ita dai Haulat tayi hakane saboda ta manta da yaya sultan, ganin ta kasa maganane Haulat taci gaba da cewa "kinga yaya Junaid sauk'in kai gareshi, kiyi k'ok'ari ki koya mishi sonki zakiyi alfahari dashi ko ba yanzu ba zaki gasgata
magana ta".
wani k'aramin littafi ta ciro a handbag d'inta ta ce "ki karanta wannan ni zan wuce, idan kikayi wasa da damanki mijin ki ya tafko miki kishiya ba yanda kika iya".
ta fad'a tana dariya.
"Don Allah kada ki tafi yanzu kibari muci abincin sai ki tayani gyara gidan".
Dak'yar ta zauna kafin wani lokaci gidan yayi fes ko ina ya d'au k'amshi.
kayan turaren wuta dasu humra kuwa mom ta mata kamar bazasu k'areba
Kafin ta tafi sai da tayi ta bata shawara duk akan ta manta da Yaya Sultan ne.
Tunda ya futa da sassafe gida yayi yaje yayi kwanciyar sa a d'akin momy har wajen k'arfe 12, shima shigowar Haulat ne ta dameshi da b'uruntu ta tab'a can ta tab'a can, ai kuwa yana tashi yafara balbale ta da masifa, dama so take ya tashi yasa tayi haka.
"uncle kayi hak'uri, pics d'in Aunty Hafsat ce data manta zan tattara na kaiwa yaya sultan tunda bai samu ya aure...
tafad'a tana k'unshe dariya da gayya tayi maganar, wani wawan damk'a ya mata ya d'aga hanu zai mareta sai kuma ya fasa, yana huci yabar d'akin da sauri ya nufi sashinsa yayi wanka yayi sallah yasaka k'ananun kaya sun masa kyaw, ko sallama baiyi wa mom ba saboda tana wajen sultan tana bashi magungunan shi.
Tun daga harabar gidan yafara jin sanyi aranshi har ya k'arasa shiga, lumshe ido yana shak'an k'amshin daya sanyashi jin bacci.
Ba kowa a perlourn don haka ya nufi d'akinta, littafin da Haulat ta bata take karanta wa, lokacin ta sake wanka tasaka englishwrs ta d'aure kanta da hairbon pink me kalan kayan.
Tsayawa yayi yana kallon ta ba k'aramin
kyaw tayi masa ba, k'aramin pink d'in bakinta ya zubawa ido, takawa yayi ya isa gabanta ya tsuguna, har lokacin karatun ta takeyi tayi nisa a ciki wani waje taji kunya ta lumshe ido wani waje tayi dariya, tsintar kanshi yayi da kamo hannun ta da yasha lalle, ta mik'e da sauri zata kurma ihu ya toshe mata baki ya ce "sai ayita sallama baki amsawa ko, bani naga me kike karanta wa".
da sauri ta b'oye littafin tana dariyar daya sashi sandarewa, wutar sonta ne ya dad'a ruruwa a cikin zuciyar shi, shima murmushin yayi yana binta da wani irin kallo idanuwan sa a lumshe ya mik'e ya ce "kinci
abinci"?
kad'a ido tayi wai ita ala dole zatayi fari da ido yanda ta karanta acikin littafin, hakan datayi kuwa ba k'aramin tsumashi yayi ba.
"Baki bani amsaba".
Ta d'an shagwab'e fuska ta ce "na ci".
murmushi yayi ya bar d'akin, da gudu ta tashi tana lek'ensa don bataso ya futa ba yamata kyaw fiye da yanda take kallon shi a baya, ko don bai d'aure fuskan bane oho.
Kwanciya yayi yana tuno siffar ta, fara ce tanada manyan idanuwa,
k'irar ta kuwa ta kalangu ce, zara zaran yatsunta ya tuno yayi ajiyan zuciya ya mik'e zaije ya nemawa cikinsa abinci, duk
kasala ta sauk'a masa.


.
::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
:::::::::::::::




Kiyi hak'uri Haneefa kinga ba lafiya yake dashi ba ki tausaya mishi ki kula dashi ki mantar dashi komai, idan kikayi kin gama mana komai, zamu zauna dake anan dazaran ya gama warkewa zaku koma gidan ku don Allah kiyi hak'uri ki kula dashi a hankali zai soki".
Haneefa Sarkin Tausayi ta share hawaye ta ce "Insha Allah zanyi iya k'ok'ari na kuma basai kun had'ani da Allah ba tunda mijina ne zan kula dashi".
Baa yayi ta saka mata albarka.
Sashin Sultan aka kaita, mom ta nuna mata wajen ta ce "Bazan ce masa komai akanki ba tukunna, kibishi aduk yanda ya d'auke ki kinji d'iya ta".
sunkuyar dakai kawai tayi tana murmushi.
Haneefa Wayayya ce nak'in k'arawa, irin matannan ne masu iyayi ga saurin sabo don haka take da tarin k'awaye da ita kanta batasan yawansu ba, Allah ya zuba mata surutu ba'a tab'ata ta k'yale sai dai tanada tausayi sosai.
D'akin nashi ta murd'a ta shiga, yana kwance da alamun bacci yakeyi, tasha mamaki dataga d'akin tsaf2 duk da ba lafiya yake dashi ba, hakan ya tabbatar mata cewa yana tsafta, k'arewa d'akin kallo tayi na tsawon lokaci kafin ta mik'e ta futa ta koma perlour, batasan me zatayi ba don haka ta kwanta awajen har aka k'ira sallar azahar, tana yunk'urin tashi taji motsin shi yana fitowa, turus yayi awajen da mamaki don shi ko Hafsat bata tab'a lek'owa sashin sa ba, d'an murmushin nan nashi yayi ya ce "Haneefa me yafaru, Hafsa ce ta aiko ki ko? yanzu nake cewa zanje tunda nasan mutane
sun ragu ko"?
wani murmushi ta sakar mishi ta ce "Eh Aunty ce tace nazo na duba ka, kuma... umm kumaaa wai..... nataya ka zama kafin agama bikin.. nanda sati d'aya dai infact....
zaro ido yayi yace "ki tayani zama a ina wai, kinsan me kike fad'a kuwa"?
k'ugu ta kama ta ce "na sani mana, kasan kana buk'atan a kula dakai saboda ciwon ka, ganin ba yanzu za'a gama bikin ba sai nanda sati yasa aka yanke hukuncin nazo na zauna dakai".
kallon mahaukaciya ya mata ya saki dariya ya ce "ok naji, wani irin kulawa zaki bani"?
"zan rik'a yi maka abinci nazauna nayita maka tad'i, na gyara maka waje, nayi maka wanka, nasaka kayi bacci.....
Dariyar dayake tayi ne yasa ta tsuke bakin ta tayi shiru tana watsa mai harara wanda ya gama tafiya da imaninsa, karo na farko da yaji wata mace ta burge shi bayan hafsat.
yarfa hanu yayi ya ce "ki fara aikin ki yanzu, zanje wajen mom naji wannan banzan
al'amarin
waye ya k'irk'iro shi"...
.
still dariya yakeyi har yabar d'akin.
Tana ganin yafita tasaka key, tasha d'amara ta hau aiki, komai ta canza masa wajen zama ta canza tsarin wajen gaba d'aya, ta jawo kayan da mom ta biyota dashi, akwatina ne guda 8 cike da kaya sai manyan gana massgo guda 2 tayi murmushi ta ce "Ashe dai mutanennan sun gane".
kayan make up ta cika akan mirrow, takai duk wani abunda zata buk'ata na toilet takai, ta d'ibi kayan shi dataga na daud'a ne ta zubasu a ingine wanki ta jefa sabulu ta rife, kafin wani lokaci ta gama wanke su tass ta shanya, batayi tunanin akwai kitchn a wajen ba sai taga akwai tayi murna kuwa sosai, ganin har dasu nama a fridge d'in ya bata mamaki batasan mom
ce ta zuba musu komai ba.
farfesun kifi tayi daya cika gidan da k'amshi, tayi alalan doya sannan ta markad'a kwakwa da dabinon ta ta tace tasa mai k'ank'ara da flavour taje ta jera masa su.
Sau Uku kenan tanaji ana buga k'ofan
tayi banza aranta tace zama ka gaji da bugawa sai nagama wani ya shigo.
Wanka tashiga ta dad'e tana gasa jikin ta saboda duk ta gaji, ta d'auro alwala tayi sallah sannan ta duk'ufa kwalliya, humra ta shasshafa ajikin ta sannan ta fesa turarruka, dogon riga ta saka bak'i me adon duwatsu agaban wajen k'ugun yad'an kamata, ta yane kanta da k'aramin hijabi. (nidai nace wallah
tasha kyaw).
Jin muryan momy a bak'in k'ofar tana k'wala mata k'ira ne yasa tayi hanzarin zuwa ta bud'e k'ofar.
*masha Allah*
Abun da mom tafad'a kenan data ganta kafin ta k'arasa shiga, murmushi tayi ganin wajen gashi k'amshi duk ya cika wajen aranta ta ce "lallai mace rahama ce wannan itace matar da tadace da d'anta me larurar ciwon zuciya, tasan zaman nasu zaifi dad'i saboda be fara sonta ba tun farko balle *SONTA YAYI AJALINSA*
"Duk ke kika sha aikinnan haka".
ta sunkuyar dakai tana murmushi.





"Naji dad'i sosai Haneefa Allah yayi miki albarka, gashi can yanata masifa ki rufe k'ofa kink'i bud'ewa ashe aiki kikasha, Allah ya miki albarka"
Ahankali Ta Ce "Ameen".
Mom tana mik'ewa itama ta tashi ta d'auko flask d'in data zuba musu abincin tabi bayan ta dashi.
Yana kwance a d'aya daga cikin kujerun falon yana latsa wayar sa suka shiga, bai san tare suke ba, ya ce "Kin korata ta tafi ko mom, narasa gane inda maganar ku ta dosa ace wai zata kula dani haba Mom baku tsoron wani abu yafaru ne"?
"mun dai gama magana dakai kada nasake jin wata magana a bakin ka".
"nadaina mom".
Dai2 lokacin ya d'ago ita ya fara gani ta kafe shi da ido kuwa, saida hanjin cikinsa suka murd'a, ya had'iye yawu yayi murmushi ya ce "m sorry".
Murmushi Kawai tayi ta d'an saci kallon Mom taga hankalin ta yana kan Tv, ta kashe masa ido d'aya tare da karkad'a masa eyelashes d'in ta.
k'irjin sa ne yayi fat, da sauri ya mik'e yana fad'in innalillahi aran shi, wani irin feelings yakeji har tsak'ar kanshi.
[12:48PM, 8/21/2017] Aysha Bichiki: 🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈
*SONE AJALINA*
🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
(we dont just entertain and educate, we also touch the ❤ hearts of the readers).
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
By Aishatu salihu Bichiki.
page12
Ina ganin sak'onnin ku insha Allah yanzu zaku rik'a ganina kullum.
kuma labarin ba wani me yawa bane🤣
.
.
.
.


Haneefa ma mik'ewa tayi tsam tabi bayanshi, harda É—an saurin ta, ta iske shi, yaÉ—an dube ta ya girgiza kai yana murmushi, koda suka k'arasa sake baki yayi ganin inda wajen yayi matuk'ar haÉ—uwa, har cikin zuciyar shi yaji wani irin sanyi ya nemi waje yazauna yace mata "sannu da aiki, amma inaso kimun alfarma É—aya".
Saida ta É—aga masa gira ta ce "inajin ka".
"yauwa, wlh Hafsat nakeson gani don Allah ki san yanda za'ayi ki k'iramun ita, sauran kwanakin Yayi yawa bazan iya jurewa ba".
Dariya tayi kafin ta ce "Aikina na kula dakai, na hanaka tunanin kowa, don Allah ka manta da Hafsa har sai ranarda ta dawo gare ka,
Idan har kasake wasa da rayuwar ka kasa tunani aranka zuciyarka bugawa zatayi ka mutu, na manta ban baka labari ba, ranarda za'a É—aura auren ku ka mutu fa".
Kallon ta ya tsaya yi yana mamakin yanda ta k'ware a surutu marasa amfani.
"ke kinsan mutuwa kuwa, ba gani a raye ba".
"yaya Allah kuwa ka mutu, sai aka fasa É—aura auren saboda babu yanda za'ayi a É—aura aure da gawa, daga nan bansan me yafaru ba kawai sai naji Abbah na yace naje na kula da yaya sultan har sai ya cire komai aransa kafin nadawo".
Tana k'arasa maganar ta koma kusa dashi ta zauna, a hankali tace "me ka fahimta"?
murmushin nan nashi yayi ya ce "ban fahimci komai ba".
Ta zumɓuro baki ta mik'e tana kunkuni, abincin da tayi ta zuba masa still tana ta zunɓura baki, shi dai dariya take bashi, k'asan zuciyar shi kuma yana sak'a masa abubuwa akan Hafsat, wata zuciyar ta ce kodai da akace ya mutu itama Hafsan mutuwa tayi? Sai kuma yace Auzubillah!
.
Sai da ya cinye abincin ta mik'e ta nufi haÉ—a masa ruwan wanka.
.
.
.
.
Dare mahutar bawa.
Anan tsiyar take, tunanin shi ya tsaya cak lokacin da yaga ta haye gadonshi ta kwanta.
"ke ki taso ki wuce ki tafi gida".
daÉ—a mik'ewa tayi harda jan numfashi.
wani tsawa ya daka mata
"Bakiji bane?
me kike nufi?
tare zamu kwana wai?
ni ba k'aramin yaro ba an wani turoki kula dani, wannan ma salon iskanci ne".
ya faÉ—a haÉ—e dajan tsaki.
É—an buÉ—e idon ta tayi ta sakar masa murmushi, "kazo mu kwanta Yaya Sultan, tsoron me kakeyi".
a hankali ta sauk'o daga gadon, wani irin rigane a jikin ta tsayin shi iya cinya, sharara ne kana ganin komai na jikin musamman wajen da yake motsi.
sandare wa yayi a wajen, ya haÉ—iye yawo ya runtse idonshi.
Tsoro da fargaba sun cikata amma bayanda ta iya dole wannan hanyar zatabi yagane ita matarsa ce batare da yayi tunanin wacce ta masa nisa ba.
Dab dashi ta tsaya ta ce "salon iskanci fa kace, iyayen namu ne 'yan iska ko kuma ni da nake taimaka maka? Tare zamu kwana Yaya sultan".
Ta faɗa tana rik'o hanunshi, wani shock taji har tsak'iyar kanta, shikam imanin sa tafiya yayi don bai taɓa kasance wa da mace hakaba, yarinyar ta gama rikita shi sosai, jawota yayi ta faɗo jikin sa, k'ara ta saka yasa 'yan yatsun sa ya murɗe bakin ya ce "idan ba salon iskanci ba menene? Ki faɗamun bayan na farfaɗo sai me yafaru da har aka turo ki nan, ban yadda haka kawai iyayena zasu turoki zama nan ba, ina Hafsat! Ta mutune?
Bakinta na rawa tace "ni ce matarka ba Hafsat ba, Hafsat tana raye lokacin dakayi dogon suma aka É—aura auren Hafsat da Junaid...
cika ta yayi ya mata alamar tayi shiru.
pilow ya ɗauka ya nufi perlour yayi kwanciyar sa, kuka yake sosai da bai taɓa irin wannan kukan ba, meyasa Hafsat ta kasance ba matata ba? Rayuwa tace ita!
kuka yakeyi sosai zuwa wani lokaci ya mik'e da sauri ya koma É—akin, itama kukan takeyi, ya matsa kusa da ita ya É—ago fuskan ta tana kallon shi "kiyi shiru, nagane yanzu, k'ok'arin ki kiganni cikin farinciki, kema baki sona ko?".
shiru tayi ya jawota jikin sa ya rungume ta haka kawai yaji tausayin ta ya kamashi.
"kidaina kuka Haneefa, zan soki zan mance bayana, nima zan kula dake kamar yadda kike k'ok'ari akaina, da naÉ—auka Hafsa itace bugun zuciyata amma yanzu nagane kece Farinciki na, babu wanda ya isa ya goge abunda Allah ya rubuta, dukkanin mu k'addara muka runguma inafatan hakam yazama alkairi a garemu".
DaÉ—a rungumo shi tayi tana kuka, ya É—ago fuskan ta yasa harce a lips É—inta yana zagaye su, jikin ta ne yayi wani irin sanyi bata ankara ba taji bakin shi cikin nata yana wani irin tsotsa, ganin tana neman zamewa ne ya É—auketa a dire a gado, bakinshi yakai kunnen ta yaraÉ—a mata a hankali "yau nakeso insa miki ajiyata mu basu mamaki, inaso na nuna musu na manta da AJALINA kamar yadda suke fata".
kunyane ya kamata ta ɓoye fuskan ta a k'irjin sa.
yalolon rigar ta ya zame yafara wasa da ita.
Nidai ganin SADIYA 'yar leken asiri ta zuba ido yasa na zunguro ta na jata muka bar É—akin, ihun Haneefa kawai muke jiyowa sai Sultan daketa sa mata albarka.








🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈
*SONE AJALINA*
🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈
🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
(we dont just entertain and educate, we also touch the hearts of the readers).
By Aishatu Salihu Bichiki.
.
*JINJINA GA JAMIL Y KURFI ALLAH YABAR ZUMUNCI*
.
*BANA BANBANCEKU*
*MY SWEET NAFISA AND SADIYA SADNAF*
.
_INA ALFAHARI DAKU_
_MATAN PURE MOMENT_
*PRINCESS ESHAT AYSM*
*MOMYN SULTAN*
*AISHA A YABO*
*SADNAS*
*FASHUNA*
*FARIDA SWRRY*
*FATEE AXLAND*
*MARYAM MUKTAR*
*UMMU IFTIHAL*
*NANA FA'AD*
*'YAR GATAN SADNAF*
*UMMUN YUSRA*
*MASHKURA UTHMAN*
*UMMY ABDUL*
*MRS FAWWAZ*
*MOMYN IHSAN*
*SEEMALOVE*
*UMMU KHADY*
*MARYAM S BELLO*
*FANNAH K AHMAD*
*AUNTY KHAUSAR*
*MAMAN KHADIJA*
*MERYAM*
*ROOKIEY KAXS*
*RUFAIDA YUSUF*
*BIEBIE DEE*
*FATIMA NASHUKA*
*UMMU SAFWAN*
*FIRST LADY*
*MEERNAH PARROT*
*AYSHA*
FEEDY LOV
SAMRA
MAMAN KHAIRAT
SALMA
SUMMY
INDON K'AUYE😂
UMMA YAHYA
SHUKRAh
JANNAT LAMEED'O
💋
BICHIKI FANS
*ILYSM*❤
.
.
.
.
.




Tarairayar Haneefa yakeyi tamkar k'wai, kwana É—aya ya manta da *AJALINSA*.
(nidai nace anya zai manta Ajalinsa)
Da kanshi yaje yayi ta godiya wa iyayen sa da iyayen Hafsat da suka bashi Haneefa.
.
.
.
JUNAID na hango mak'ale a cikin labule yana lek'en ta, yasan dazaran ta ganshi komawa É—aki zatayi, shikuma yafi so yayi ta ganin ta yana jin sanyi aranshi.
da wata É—amammen skin tired yabi cinyoyin ta zuwa k'afar ta ya É—ame sai kayi zaton babu wando ajikin ta, bata É—aura É—ankwali ba sakamakon kitson da tasha k'ananu sun kwanta a gadon bayan ta, tasan dai bayanan amma jinta take duk a takure bata saba saka irin wannan kayan ba, tsaki tayi tana ja wa Haulat Allah ya isa.
Toilet ta fara wankewa da hypo ta feshe da freshner É—akunan nasu ma duk ta gyara su, tana gama girki ta gyara kitchn É—in fes, ganin magriba ta gabato yasa taje ta saka key a k'ofar falon da niyyar zataje tayi wanka, labulen ta zuge aikuwa taga k'afa ta k'asan labulen, ihu ta kurma tana karanra ayatul kursiyyu a tunanin ta aljani tagane, rufe idon tayi ta kasa guduwa sai kurma ihu take tana karanta duk abunda yazo bakinta, da sauri yafito ya rik'ota aikuwa ta daÉ—a callara ihu tana neman sandarewa, gaba É—ayama batajin me yake faÉ—a, ganin ta gama razana ne ya daka mata tsawa da iya k'arfin shi.
A hankali ta buÉ—e idon tana kallon shi still kukan takeyi, ya rungume ta tsam a k'irjin sa yana É—an bubbuga bayan ta alamar rarrashi.
DaÉ—a kwantar da kanta tayi ajikin sa tana ajiyan zuciya, ya lumshe ido yanajin daÉ—i gani yake kamar a mafarki wai Hafsat ce matar sa, yarinyar dayafi so fiye da komai a rayuwar sa, pick ya mata a goshin cikin matsanancin so, yaÉ—an É—agota ta daÉ—a rarumo shi ta k'ank'ame shi, yadan saki murmushi yace "Tsoron me kike ji ne wai"?
Cikin labulen ta nuna masa ta ce "Uncle akwai aljani a ciki".
Dariya yayi ya É—aga ta yakaita har É—aki ya ajiye ta, juyawan dazaiyi ta rushe da kuka kamar wacce ake zaneta.
Zuba mata ido yayi naÉ—an lokaci kafin ta ce "me kike so yanzu kuma?"
"wanka zanyi".
"wankan kikewa kuka?"
Shagwaɓe fuska tayi ta ce bazata iya shiga ba, wasa2 ta tubure dole sai ya rakata wankan, ba yanda ya iya dole ya nufi bayan gidan tabishi a baya, har lokacin a razane take.
Tunda suka shiga ta tsaya a bakin Bath É—in tana nok'e2, ya haÉ—a girara sama da ta k'asa yana harar ta.
"me kike nufi HAFSA"?
Bata taɓa jin ya k'ira sunan ta ba sai ranar kusan ma sai tace shi kaɗai ya iya k'iran sunan.
Zunɓuro baki ta yi tace "na fasa wankan".
matsawa yayi kusa da ita yana faÉ—in "ki sani na rako ki sannan ki mayar dani shashasha, idan na irga uku baki fara ba wlh dakaina zan miki".
ya rufe idon shi ya fara countn.
"uncle don Allah kada ka buÉ—e idon"
murmushi yayi a ranshi yace k'aryama kenan.
"kema idan kin shiga kada ki buÉ—e idon ki, idan kika buÉ—e nima zan buÉ—e".
sai da ta haɗa ruwan ta saci kallon shi taga ya juya mata baya ya rufe ido sannan ta cire kayan jikin ta tafaɗa bath ta fara wanka, idon ta yana rufe sai hanzari takeyi ya ɗan juya a hankali zai saci kallonta, abun da ya ganine ya sashi waro ido numfashin sa har yana sark'ewa, shi duk tarin shekarun sa bai taɓa ganin k'irjin mace bama balle ya ganta tsirara, k'arasawa yayi wajen bai ma saniba don shi yagama futa a burki, ji kawai tayi ana shafa k'irjin ta, ta buɗe ido zata callara ihu yayi saurin saka bakin shi anata ya rufe, gaba ɗaya cikin ruwan shima ya shiga yafara sarrafa ta son ranshi, saida yaga yana neman gutsire mata baki don tsotsa ya cire a hankali, ya rungume ta yana mayar da numfashi, itakam kuka ta saka tana rarraba ido batasan da irin wannan kwamacalar ba a rayuwar ta.
Wuyan ta yabi da kallo ya lumshe ido ya buÉ—e baki dak'yar kamar me raÉ—a ya ce "kukan me kike yi, bana son jin wannan kukan Preety
kinsan ke kika sani biyo ki ko".
Kunyan shi ya gama kama ta takasa buÉ—e ido, tanaji tana gani ya mata wankan ya tsotsi nan ya tsotsi can har ya gama ya naÉ—e ta a towel ya kaita É—aki.
Gaba É—aya ta manta da wani Aljani bata da burin da yawuce ya futa ya bar É—akin amma shi k'ok'arin shafa mata mai ma yake yi, har kwalliya ya mata, yana so ya zame towel É—in yanajin kunya don bai gaji da kallon ta ba.
Daure wa yayi ya É—auko mata doguwar riga yasaka mata kafin ya zare towel É—in ya mayar toilet É—in.
jin k'arar ruwane yasa ta gane shima wankan yakeyi, tayi ajiyan zuciya tana tuno abubuwan da yamata, lumshe ido tayi dataji tana son irin abun, ta É—anyi murmushi da ta tuno kyakkyawan fuskar shi.
Ruwan da taji an yarfa mata ne yasa ta buÉ—e idon ta da suka lumshe, yabi k'aramin bakin ta da kallo ya ce "Har kin fara kewa ta"?
kunya ya bata ta ɓoye fuskar ta tana murmushi, bai je masalla ci ba kuma bai tafi ɗakin shi ba, anan sukayi sallah tare har aka k'ira isha suka gabatar sannan sukayi nafila raka'a biyu ya juma yana adduar Allah yabasu zaman lafiya da zuria ɗayyiba, yakuma gode wa Allah da yabashi abun da yafi k'auna a duniya.
suna shafawa ya janyo ta jikin sa ya dafa goshin ta ya karanta wannan adduar
_BISMILLAHI... ALLAHUMMA JANNIBANA SHAID'AN WA JANNIBISHHAID'ANA MA RAZAK'ATANA_.
yana gama karantawa ya mik'ar da ita ya ce "ina zuwa"
Binshi kawai tayi da ido har yabar É—akin, ta sauk'e numfashi a hankali taji sonshi yafara fizganta, cikin kasala ta mike ta haye gadon ta kwanta don wani irin bacci ne ke kwasan ta gashi tanajin yumwa amma batajin zata iya ci.
koda yadawo har tafara bacci taji shigowar sa, bai mata magana ba ya ajiye ledan hanun sa yaje ya ɗauko abu ya dawo, kaji ne da yougort da kanshi yayi ta figa yana saka mata a baki, ita dai tarasa dalilin da yasa takasa taɓuka komai tanaji tana gani ya cire mata hijabin ya dauke ta kaita toilet ya mata brosh sannan yayi shima.
yellown riga ya ciro mata tsayin ta iya cinta me É—an k'aramin hanu, sai da ya rage wutan É—akin ya haye kan gadon har ta fara bacci ya É—ago ta, nan fa tsoro yafara kamata ta ce "uncle bacci".
Yatsa yasa a bakin shi yamata shhhhhhhhh alamar tayi shiru, runtse idon ta tayi tanaji yana kiciniyar cire mata ta fara hawaye, nan fa ya sake arba da abunda yake zauta shi, bai saka mata rigar ba ya mannata a jikin sa yanajin yanda kukan ta ke fita a hankali.
"Hafsa, meyasa bazaki daina kuka a kusa dani ba, inaji kamar zuciya ta zata fashe idan kina kuka, da kinsan tsawon lokacin dana É—auka ina dakon sonki da kin daina kuka a kusa dani, nagode wa Allah daya bani farinciki a rayuwata yamallaka mun macen da mafarkin ta yazamto abunyi na kullum, da ace na rasaki na tabbata da *SONE AJALINA*
Duk wanda zai soki a bayana yake Hafsat, ki cire É—an uwana aranki na rok'eki nasan abunda yake sakaki kuka kenan".
ya kamo hannun ta yasaka a k'irjin ta ya ce "kiji yanda zuciya ta take bugawa, duk akan sonki".
wani sabon kukan ta buɗe tausayin Junaid ya kamata don bata taɓa sanin sonta yakeyi ba.
ganin bazatay shiru bane yasa yafara nuna mata salonshi, salone me cike da É—unbin soyayya, salon da ba kowani namije ne ke iyashi ba.
Wannan dare shine daren da bazasu taɓa mantawa ba a ayuwar su, darenda Junaid yake mafarki kullum, shi kukan daɗi ita kukan daɗi da azaba don hankali ya tafiya da ita har ya cimma buk'atan sa.
kyaututtuka kam tashata har saida ta toshe masa baki.
.
..
Dukkanin su sun manta da bayan su soyayya kawai suke tsalawa, Mom kafin ta koma Kano saida taje gidan Æ´yaranta ta dubasu.
Tun da suka ga Sultan ya warke suka tattara shi da matar sa suka tare a gidan su.
Yaya Haidar  dama tunda yaga Haulat yace yaga mata akasabikinsu lokaci k'ank'ani.
..
..
.
*BAYAN SHEKARA D'AYA*
.
.
HANEEFA ta haifi santaleliyar yarinyar ta aka saka mata sunan Momyn su SULTAN.
HAFSAT kuwa lokacin cikin ta yayi k'ato sai uwar shagwaɓa datake zubawa, INNAH aka ɗauko mata ta zauna da ita, idan kaga JUNAID saika rantse shine me cikin.
.
Itama ba'a jumaba ta fara nak'uda, gaba É—aya Junaid ya kiÉ—ime kuka yaketayi ganin wahalan da take sha gashi Innah ta hana zuwa asibiti, dak'yar tasamu ta masa wayo yabar É—akin tasaka key.
.
kukan jariri yaji ya koma É—akin da gudu
Yana bugawa, bata kulashi ba can yasake jin wani kukan hakan ya tabbatar masa da cewa 'yan biyu ta haifa masa, a wajen yayi sujjada yana godewa Allah.
Maza biyu ta haifa gwanin sha'awa dukkanin su da JUNAID suke kama, murna wajen dangi ba'a magana, anyi shagali kamar babu gobe, washegarin suna mom taÉ—au 'yarta suka wuce Kano zatayi wankan gida.
Junaid kamar ya mutu haka yaji bayanda ya iya.
...
.
*BAYAN WASU SHEKARU*
.
.
HANEEFA da HAULAT 
nagani a gidan HAFSAT
Yaransu sunyi wayo sosai gwanin sha'awa suna tattauna wa akan kasuwancin da zasu fara.
Ganin mazajen nasu dokiya ta zauna suma suka yanke hukuncin bazasu zauna haka ba.
.
.
.
.
TAMMAT BIHAMDULILLAH.
Anan nakawo k'arshen wannan littafi me suna *SONE AJALINA*
.
Fatan alkairi ga dukkanin masoya na ako ina suke.
.
.
Yanzu za'a iya watsa wannan novel É—in a duniyar fcbk kamar yadda nace dama sai nagama.
.
.
_INA FATA KUN NISHAD'ANTU_
.
LOV U ALL💋💋💋

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

Australian Visa Application information: Visa Types & Requirements

[Sunnah] What Muslim Should Observe On The Day Of Eid

Canada Immigration: How To Apply For Canada Permanent Resident Visa