NI AYS NAKE SO 18

💅💅💅
      💋 *NI AYS NAKESO*💋
                 💅💅💅
Page 18
.
.
.

_WRITEN BY Princess Eshat Aysm_
.
.
In Dedication to *ABDULLAHI YAHYA SA'AD ZARIYA*
A.Y.S





.


.
.




Lidia sai kuka takeyi aka murÉ—a k'ofa aka shigo, Dr Abdul ne cikin takunsa na k'asaita ya nufi inda suke, tsayawa yayi a kusa da Dr Mansur ya ce "menene kake zufa haka"?
Kallonshi Mansur yayi ya ce "ka ajiye rashin mutuncinnan naka, wannan mara lafiyan zaka dubamun, wallahi basirata ya k'are akanta".
Juyawa Dr Abdul yayi wajen da Aisha take kwance, cire farin glass É—in dake manne a fuskanshi yayi yana kallonta da lumsasshun idanuwansa, lokaci É—aya ya tsuguna a gabanta, ya É—aura hannunsa kan k'irjin ta, yaji dai dai numfashin yake tafiya.
Mik'ewa yayi ya fita ba tare da yace musu komai ba, binshi Mansur yayi da kallo a ranshi yana tunanin ina zashi, bai gama tunanin ba ya shigo ɗauke da wani abu, saida yagama gwaje gwajenshi ya jiyo ranshi a ɓace, Dr Mansur ya kalla ya ce "idan ka kashe ta sai kayi bayani".
Kallon rashin fahimta Mandur yayi mishi, ganin ya É—auke kai kamar bazaiyi magana yasa yace mishi "wani irin magana kakeyi Abdul".
Da masifa ya ce "wani irin Magani ka fara bata"?
Nan jikin Lidia ya fara ɓari, dama da tazo bada maganin ta rasa wanne zata bayar a lokacin.
Wani mungun kallo ya watsa mata, "wanne kika bata"?
Ya tambaya kamar zai daketa, toshe bakin ta tayi tana nuna masa, wani tsawa ya daka mata, zaiyi magana Abdul ya ce "laifinka ne, kamata yayi ka tsaya kabata kafin,
Ni sauri nakeyi yanzu zan tafi".
Kallon mara hankali Mansur yayi mishi
"kafi kowa sanin wannan aikin ka ne, taimakon gaggawa take buk'ata, idan ta farka a haka zamu samu matsala".
Wani yamutsa fuska Abdul yayi ya ce "to naji sarkin bayani, saika kama gabanka kawai zan dubata".
K'wafa Dr Mansur yayi sannan ya watsa wa Lidia harara yayi ficewar sa, kamar jira takeyi tabi bayanshi tana bashi hak'uri.
suna futa Abdul yayi murmushi aranshi ya ce "abu ba abuba duk sun ruÉ—e".
File É—inta
YaÉ—auko ya fara dubawa, yanaso yasan meke damunta tun farko, ware ido yayi sosai ganin sunan, ESHA ya faÉ—a a hankali, lokaci guda idonshi suka ciko, juyawa dubansa yayi kanta.
Zan kula dake ko don darajar sunanki, ni kaÉ—ai nake rubuta sunannan sai yau dana gani a karo na farko".
Duk aranshi yake magana idonshi nakanta, cikin gaggawa ya haÉ—a alluran da zai kashe wancan, runtse ido yayi lokacin da yake tsira mata allurar, shi baison allura wa mace ko kaÉ—an, yana gamawa ya mayar da ita kan gadon sannan ya gyara wajen yayi ficewar sa.
.
.
.
.
Momy ce zaune ta buga tagumi da hannu biyu, lamarin Faruq ya fara bata tsoro, kamar k'aramin yaro haka ya zamo wajen iya shege, duk faÉ—an da zata masa akan yaje yabaiwa iyayen Aisha hak'uri sai yasaka mata kuka.
Ranar da aka kai Aisha Abuja taje gidan, jin labarin halin da Aisha take cikine yayi matuk'ar É—aga mata hankali, don haka bata bar gidanba har saida ta jira suka dawo, har kuka tayi lokacinda suka dawo jin wai Aisha acan zata zauna, sosai takeson Aisha a cikin ranta.
Kallon Faruk tayi ta ce "me yake damunka Son, nafaÉ—a maka abunda kayiwa yarinyar nan amma ko maganar zuwa bakayi, meyasa ka canza halayyarka a lokacinda sam bai dace ba".
Kallonta yayi cikin kulawa ya ce "Mom ni kaina inajina na canza, inason Aisha wallahi inajin wani iri a rainane kawai, inaji ajikina kamar ba dai dai nakeba".
Shiru tayi tana kallonshi, tabbas akwai matsala, tunaninta ya tsaya akan aljanune suka raɓeshi.
ajiyan zuciya ta sauk'e ta ce "kana wasa da addua Faruq, ko k'uncin rayuwa bazaka shiga ba idan har Addua ta kama jikin ka, balle wani abu me cutarwa ya samu gurbi a rayuwar ka, kana wasa da rayuwarka Son".
shiru yayi yana sauraranta, faÉ—a tamai sosai wanda shi kanshi jikinshi yayi sanyi, yana ji ajikinshi shaiÉ—an ya samu galaba akanshi.

.
.
Farkawa tayi duk jikin ta a mace, ji take kamar anmata duka, ta mik'e daky'ar ta faÉ—a toilet tayi wanka, a daddafe tayi Sallah, tana addu'a Dr. Abdul ya shigo É—akin, da tsananin mamaki ya bita da kallo, tsugunawa yayi a gabanta ya ware manyan idanuwanshi akanta, tana shafawa ta dubeshi da sauri, É—an murmushi yayi ya ce "kin samu kanki kenan"?
sauk'e idonta tayi k'asa, bata fahimci me yace ba, abincin daya shigo dashi ya tura mata yana cewa "baki haukace sosai ba ashe, kici abinci yanzu inajiranki zan baki magani".
harara ta watsa mishi, ya kashe ido ya ce "ah ashe haukan yananan, ina fata baki fara duka ba".
Lidia ce tashigo, tana ganinshi taÉ—an sunkuya tana gaishe shi, ko kallon ta baiyi ba balle ya amsa, bata damu ba, sun saba da halinshi nak'in kula mutane, sam bashida mutunci sai shegen ilimi, gaban Aisha taje ta zauna tana murmushi ta ce "yaya jikin".
A hankali ta ce "da sauk'i".
Wani malalacin murmushi yayi ya ce "kinajin magana wai"?
sunkuyar dakai tayi ta fara hawaye, da sauri ya tashi ya na cewa "kinga tafiya ta, nayi hakane don nagane matsalar ki, nasan me kike ganewa".
Yana faÉ—in haka ya fice.

Comments

Popular posts from this blog

Australian Visa Application information: Visa Types & Requirements

[Sunnah] What Muslim Should Observe On The Day Of Eid

Canada Immigration: How To Apply For Canada Permanent Resident Visa