NI AYS NAKE SO 19

💅💅💅
      💋 *NI AYS NAKESO*💋
                 💅💅💅
Page 19
.
.
.

_WRITEN BY Princess Eshat Aysm_
.
.
In Dedication to *ABDULLAHI YAHYA SA'AD ZARIYA*
A.Y.S





.


.
.





_kuna hak'uri da É—an wannan É—in, kuna mun uzuri, yanda kuke rububin wannan book É—in haka nake rububinku, har kullum ina godiya da adduoin ku gareni_
Love you all my wtsp group💋
.
.






Ƴyana futa Lidia ta kamo hanunta ta ce "kiyi hak'uri".
Kallon ta kawai Aisha tayi batace komai ba, batasan dalilin bada hak'urin ba, abincin lidia ta zuba mata ta ce, girgiza mata kai tayi alamar ta k'oshi, Tea ta haÉ—a mata me kauri ta mik'a mata, zata girgiza kai Lidia ta ce "kada mu fara haka dake, kisha zakiji daÉ—in jikin ki".
Kau dakai tayi ta ce "na k'oshi".
Duk k'ok'arin da Lidia tayi haka tak'icin komai, ta haɗa ƙmata abu yayi kala goma amma duk tak'i ci, haka ta k'yaleta taje ta kwanta.
Dr Abdul yana fita a É—akin ya k'ira Mansur
"nifa na tafi kaje ka kula da ita, taci abinci sosai kafin ta kwanta, akwai alluran da zan mata k'arfe 5 na asuba".
"to kawai Dr Mansur yace mishi ya kashe wayar, harar wayar yayi kamar yana ganinshi, yaÉ—an ja tsuka.
Har bacci ya É—auketa lokacinda ya shiga, Lidia taÉ—an zamo ta shaida masa bataci komai ba.
Shiru yayi can yace tashe ta taci wani abu".
D'an buga k'afarta Lidia tayi tana tashinta, ko motsawa batayi ba, allura ya É—auko ya É—an soka mata a hannun ta, firgit ta tashi, kamar zatayi kuka take kallonsu, wani tea É—in ya haÉ—a ya mik'o mata, zata kauda kai yayi murmushi ya ce "daure kisha, ko bakison komawa gidane"?
Da sauri ta amsa ta fara sha, tana shanyewa ya zubo mata abinci, shima cinyewa tayi, dariya kawai yayi yabar É—akin, komawa tayi ta kwanta bacci ya sake É—aukan ta.
k'arfe 4 ta farka tanajin fitsari, Lidia ma firgit ta tashi tana kallonta, ganin ta nufi toilet tayi ajiyan zuciya, itakam alwala ta É—auro tazo ta tada Sallah, da mamaki Lidia ta kalli agogo, ta zuba mata ido hartayi raka'a biyu bata daina kallonta ba, addua tayi sannan tafara karatu, duk da a hankali takeyi Lidia tana iya jiyo muryar tata me daÉ—in sauraro, baki da hanci Lidia tasake, lokaci guda taji tanason karatun.
Tananan sake da hanci aka fara Sallar asuba, mik'ewa tayi tafara gabatar dashi.
cikin nutsuwa ya buÉ—e É—akin ya shigo, farin kayansu na likitocine a jikinsa, sai wani kafcecen rigar sanyi a saman, tsayuwa yayi a bakin k'ofar ya harÉ—e hannayen sa yana kallonta, a nutse take Sallar harta idan bai motsa ba, Lidia tana gaisheshi ko amsawa baiyiba, É—ankwalin datayi sallar akai ta É—auka ta naÉ—e ta koma zata kwanta, har gabanta ya isa yace "daren jiya kinci abinci"?
Lidia ta kalla don bata gane me yake faɗa ba, dawo da kallon ta tayi kanshi, kallon shi tashiga yi babu ko k'yafta ido, wani irin sarawa kanta yayi, burinta tagano a ina ta taɓa ganinshi amma ta kasa tunawa, a ranta har ji takeyi kamar ta taɓa rayuwa dashi, hanu yasa yana hure idon nata amma ko gezau batayi ba, sosai takeso tagano wani abu, zuciyarta har wani harbawa takeyi, tsaki yayi ya ce "wannan kallonfa"?
da iya k'arfinta ta fashe da kuka, da sauri ya k'araso gabanta yana girgiza kai, "kada kiyi kuka, ciwon naki da sauk'i kada kidawo dashi babbah, ko namiki laifi ne"?
shi kullum idanuwanshi a lumshe suke kamar mejin bacci, gasu manya amma a lumshe suke, kukan ta fara tsagaitawa har lokacin kallonshi takeyi.
Maganin dayazo dashi ya mik'a mata tare da ruwa ta shanye
É—an murmushi yayi ya kalli Lidia ya ce "ki kula sosai".
russunawa tayi ta amsa da to.
Yana fita ya nufi office É—inshi, don lokacin gari bai gama wayewa ba, kwanciya yayi akan dogon kujerar dake cikin É—akin.
Tabbas kallo yafi komai tasiri a rayuwar mutane wajen isarda sak'o, kamar yadda lokaci guda Abdul yafarajin wani iri a cikin zuciyarshi, tsareshi da idon da Aisha tayine ya tsaya masa arai, ko yaya ya motsa sai yaji tsikan jikinshi yana tashi, ya runtse ido yana tunano sanda yaganta tana addua, murmushi yayi yana shafa sumar kanshi, tashi yayi da sauri kamar wanda aka tsikara, wani jaka yaje ya buÉ—e yaciro wata waya, wayar tanada É—an girma, shikaÉ—ai yaketa murmushi, lokaci guda ya haÉ—a rai alamar ya tuna wani abu, wayar ya buga akan table É—in gabanshi, kamar k'aramin yaro yafara kuka yana wani sumbatu.
"Tunda na rasa Aisha narasa komai a rayuta, yau gashi inacikin daular da basu da wani amfani agareni, bansan kamanninta ba, sonta bai taɓa girgiza araina ba, zan rayu na mutu ni kaɗai bazanyi aure ba...
Dr.Mansur daya daÉ—e da shigowa, yazo tambayarshi yau a wani a asibiti zai zauna yatarar dashi yana wannan haukar, kusan kullum abunda yake haÉ—asu faÉ—a kenan, kusa dashi ya isa yaja kunnenshi da k'arfi, ko gezau Abdul beyiba sai wani hararar daya sakar mishi, tsaki Mansur yayi ya ce "kana jinyan mahaukata, alhalin kai kadace da zamowa mahaukaci, wai wannan wata yarinya ce haka, inbanda hauka ko ganinta fa bakayi ba, ni bana tantama wallahi aljanace".
wani kallo ya mishi ya ce "Aisha ba aljana ba ce, ko banganta ba naga mahaifinta, naga unguwarsu".
Tuntsirewa da dariya Mansur yayi ya ce "muje na maka allura ko zaka dawo hayyacinka".
tsaki yayi ya É—au makullin motanshi ya fita yabar Mansur yana masa dariya, har ya isa jikin motar yabishi da gudu yana tambayarshi ina zaije, bai kulashi ba yaja motarsa yabar cikin asibitin.
.
.
.
mahaifin Unaisa abun duniya duk ya isheshi, A k'alla Unaisa zatayi shekaru 23 amma babu wanda yake zuwa wajenta, yayi niyyar
Yi mata aure da wani amma fafur tak'i ita akwai wanda takeso, ya zuba mata idon amma abun ya gama ɓata masa rai a halin yanzu, mamanta ya k'ira ya shaida mata akwai wanda zai aura mata nanda sati biyu, shiru tayi don ita wannan lamarin yana bata mamaki, kullum ganin yarinya takeyiwa Unaisa, shikuma duk ya ɗaga hankalinshi akanta.
K'wala wa Unaisa k'ira tayi, tana ɗaki tanajinsu, baki a zoɓore ta fito ta zauna jikin umman tata.
"kin girma baki san kin girmaba, sa'oinki duk sunyi yara amma kinanan kina zaga gari, na baki nanda sati uku idan baki fito da wani ba wallahi a matsayina na ubanki saina aura miki duk wanda nayi niyyah".
Hankali a tashe take  kallonshi, "Baba don Allah me natare maka"?
.
.

Comments

Popular posts from this blog

Australian Visa Application information: Visa Types & Requirements

[Sunnah] What Muslim Should Observe On The Day Of Eid

Canada Immigration: How To Apply For Canada Permanent Resident Visa