NI AYS NAKE SO 22 to 23
[17:18, 10/27/2017] ESHAT AYSM:
*NI AYS NAKESO*
Page 22
.
.
.
_WRITEN BY Princess Eshat Aysm_
.
.)
In Dedication to *ABDULLAHI YAHYA SA'AD ZARIYA*
A.Y.S
.
.
.
Matsawa kusa da ita Lidia ta kamo ta tana dariya, "ina farinciki da samun lafiyarki".
murmushi Aisha tayi.
Duk abunda yace ta haɗa mata saida ta haɗa mata, zama tayi tabata labarin ɗan zamansu da sukayi, musamman karatun da takeyi na AlQur'ani me girma yafi komai burgeta, duk abubuwan Aisha takanga tasansu saidai kamar a mafarki, kallon rigar jikin ta tayi ta yamutsa fuska ta ce "wannan rigarfa, nakine"?
Dariya Lidia tayi don ta gano k'yank'yami takeyi, ta ce "sayo miki akayi, ga sauran can awancan jakar".
Ta murmusa ta ce "ɗauko mun nagani".
basufi kala 5 ba, duka dogayen riguna ne, ta ɗan haɗa rai ta ce "Abbah na yana zuwa"?
Shiru Lidia tayi tana kallon ta, "ya kikayi shiru, da yana zuwa nasan da ya kawomun kayana".
sai kuma ta fashe da kuka, ruɗewa Lidia tayi, ciwon nata zai iya dawowa ko wani lokaci, baki ta shiga bata tare da tabbatar mata iyayenta suna zuwa kamar yadda taji Dr Abdul ya faɗa mata.
ya kwanta ne kawai amma yanaso yaje ya sake sanin wani hali take ciki, lumshe ido yayi tuno hawayen dayata sauk'a akan fuskarta, yayi murmushi aranshi ya ce "wannan yarinyar daban take".
Tsam ya mik'e yasaka jallabiyar sa me ruwan madara ya zari key ya fita.
suna cikin wannan darun ya shiga, lokacin k'arfe 12:14
Lidia ta russana ta shaida masa, haɗa rai yayi ya ce "da darennan zakiga iyayen naki".
Harara ta watsa mai tana zunɓuro baki, waro ido yayi ya ce "ohh ashe kin warke ko, ni kike harara"??
daɗa zunɓuro baki tayi ta ce "bakai kayimun tsawa ba".
D'an murmushi ɗauke a fuskarsa ya ce "ki kwanta ki huta, da safe sai nakaiki gida tunda kin warke".
Ya k'arasa maganar yana kashe mata ido ɗaya.
Neman waje yayi ya zauna ya fara danna wayarshi, binshi tayi da kallo tana mamaki, mutumin da take ganinshi a photo inbanda ikon Allah me yakawo ta wajenshi, lokaci guda taji tsanar Faruq ya mamaye ranta, tuno abunda yamata tayi, ta runtse ido da k'arfi, duk hankalinshi yana kanta, da sauri ya taso ya rik'eta ya fara girgiza mata kai, alamar tadaina tunanin da takeyi.
kuka ta farayi k'asa2 tana cewa "Faruq me yasa kamun haka, me nayi maka".
ƘLidia ya kalla da niyyar yace mata tarik'e masa ita yaɗauko allura sai yaga tuni tayi bacci harda wangale baki, yayi tsak'i ya dubi Aisha, jikinshi duk yayi sanyi, tsura mata ido yayi na tsawon lokaci, tsananin tausayin ta yaji ya kamashi, ya ɗaura kanta a faffaɗan kafaɗanshi, "kiyi hak'uri *ESHA*, koda bansan Waye Faruq ɗin a wajenki ba, bansan me yamikiba, inaso kisa a ranki komai a rubuce yake, haka Allah ya k'addara miki, kada kibari damuwar wani ta illata rayuwarki, bakiyi girman da zaki ɗau tension da yawa ba, kinga yanzu kina cikin yanayin da komai zai iya faruwa dake, ko hauka ko taɓin hankali, kinga kinbar iyayenki da wahala, ki nutsu kada kisake tuna abunda wani yamiki na ɓatanci".
sosai maganar ta ratsata, ta sauke ajiyan zuciya me k'arfi, a hankali ta ce mishi "nagode".
murmushin k'arfafa gwiwa yayi mata ya ce "kinyi alk'awari zaki manta komai"?.
ta ɗaga kai, ya harare ta da wasa ya ce "da baki zaki faɗamun".
murmushi tayi da fararen hak'oranta suka fito ta ce "nayi alk'awari".
shima murmushin yayi ya cikata ya mik'e ya na cewa "ki tabbata kinyi bacci, idan bakiyi ba zanji ajikina zamuyi faɗa dake".
zuba mishi ido tayi, itadai yana masifar yi mata kyau da k'warjina, yana burgeta matuk'a, hure idon yayi ya fita yana dariya, bin bayanshi tayi da kallo har ya ɓace, murmushi tayi, alwala taje tayi ta daɗe tana addua kafin ta kwanta, AYS ta faɗa ahankali, da sauri ta mik'e, lallaɓawa tayi ta ɗauko wayar Lidia dayake jikin soket, bata ɓata lokaciba tayi login Fcbk ɗinta, sunannashi yana nan raɗau akan mssg ɗinta, take matsanan cin kewarshi ya kamata, ta lumshe ido tana tunano kalamanshi, lokaci guda wani sanyi ya ratsa cikin zuciyarta, har zata sauk'a sai kuma tayi mishi sallama sannan ta sauk'a, addua ta sakeyi sannan ta kwanta, nanda nan kuwa bacci ya ɗauketa.
Duk yadda yaso yayi bacci gagara yayi, idonshi biyu har gari ya waye, ruwan tea kawai yasha bayan yayi wanka, yaɗau duk abunda zai buk'ata ya nufi mota, akwai aikin dazaiyi ma wani shiyasa yaketa sauri,.
Agogon hanunshi ya duba yaga da sauran lokaci, don haka bai nufi National hospital ɗinba sai ya nufi MANAYS.
A durk'ushe ya sameta tasawa Lidia rigima lallai ita bazata saka dogon rigaba, hannuwanshi ya harɗa yana kallonsu, dariya ta bashi sosai, baisan rigimarta yakai hakaba, a hankali ya k'arasa ciki, da sauri Lidia ta durk'usa ta gaisheshi, rana ta farko kenan da ya fara amsa gaisuwan ta, mamaki ya cikata
[07:49, 10/30/2017] ESHAT AYSM:
*NI AYS NAKESO*
Page 23
.
.
.
_WRITEN BY Princess Eshat Aysm_
.
.
In Dedication to *ABDULLAHI YAHYA SA'AD ZARIYA*
A.Y.S
.
.
.
Hijabin dake ninke akan drowar ya jawo ya mik'a mata, tanata zunɓura baki ta karɓa.
a hankali yace "taso muje".
Da sauri ta mik'e, zuciyarta fal farinciki tana tunanin zataje gida yau.
Da murmushi Lidia tabisu har suka bar ɗakin.
Motarshi ya nufa ya buɗe mata gefen da zata shiga sannan ya shiga shima ya tada motar, yaso yakaita ta zaɓi kayanda takeso ne, ya tuna aiki zaiyi ma wani yasa ya nufi asibiti, bin ko ina takeyi da kallo tana nazari kamar ba garinsu ba, a hankali yake tuk'i yana satar kallonta, can hak'urinta ya k'are ta ce "Dr wai ko na mutune"?
Waro ido yayi ya ce "mutuwa? Haka ake mutuwa"?
Fuskantarshi tayi sosai ta tsareshi da ido ta ce "naga bantaɓa ganin irin nanba, shiyasa na ɗauka ko ba'a duniya muke ba".
Dariyane ya suɓuce masa ya ce "a duniya muke".
"gidanmu zaka kaini ko".
Ta jefa masa tambayar, ya murmusa ya ce "a'a, rakani zakiyi".
Tsuke baki tayi, tayi shiru bata sake magana ba har suka isa.
Office ɗinshi dake cikin Asibitin ya kaita, nuna mata wajen zama yayi ya ce "ki jirani anan".
Kafin yagama faɗi ta ɓarke masa da kuka, da mamaki yabita da kallo ya ce "kina cikin hankalinki kuwa".
Kukan taci gaba dayi, ya matsa daf da ita yace "meyasa kika cika futuna ne"?
Zunɓuro baki tayi tana kunkuni, binta yayi da kallo da lumsassun idanuwansa, yayi tsaki yaja hanunta suka fice.
Tafiya kawai sukeyi yana rik'e da ita har suka k'arasa cikin asibitin, tunda suka shiga ake binsu da kallo, mamaki yakama mutanen, sun sanshi da miskilanci ko kallon su bayayi balle ya amsa musu gaisuwa ko sake fuska, ware ido Aisha tayi tanata kallon mutane, yana rik'e da hanunta yayi ta duba wanda zai duba, damuwarsa kada ya saketa tayi wani waje, don bai yarda ta gama warkewa ba, ɗakin dazaiyi aikin suka shiga, waje ya nema ya zaunar da ita yace "kada ki tashi anan, kijirani".
Kai kawai ta ɗaga masa sannan ya shige ciki, tananan zaune can tafara jin wani irin gurnani haɗe da kuka, da gudu ta mik'e taje tafara lek'ensu, jikinta yayi sanyi ganin inda mutumin yakeyi, ga wani na'ura duk an zagaye kanshi da ita, hawayene yafara sauk'a mata, tana mak'ale a wajen har tsawon minti 40 taga ancire masa, allura taga ya haɗa yayi masa, duk idonta nakai.
A wajen yazo ya sameta, har lokacin tana hawaye, jan hancinta yayi ya ce "wayace kitaso".
Manyan idanuwannan nata ta zuba mishi, wani irin kasalane ya sauk'ar mishi, ya janye idonshi akanta da sauri yana murmushi.
Kaya yakaita tazaɓi wanda takeso tanata murna, sannan ya sai mata abunda zataci, abunka da wanda bai saba yawo ba, ji take kamar suyita zagayawa tana ware ido da hanci tana kallon gari, daidai zasu shiga wayarshi tafara ruri, ta gefen ido ya kalleta haɗi da jan tsak'i yace "ɗauka kice bana kusa".
da hanzari takai hanu ta ɗauki wayar ta kara a kunne.
"Assalamu Alaikum".
shiru tayi ta kasa magana, kallon sunan dake kai tayi ansa UMMANA, ta kalleshi ta ce "Ummace fa".
Bai kalleta ba ya ce "kiyi magana".
sake mayarda wayar kunnenta tayi haɗi da amsa sallamar, "ina Abdul ɗin"?
shafa fuskarta tayi ta ce "yaɗanyi nisa ne".
"wacece ke".
umma ta tambaya, ta juya da sauri tana kallonshi, kamar yasan abunda akace ya ce "kidaina kallo na, kice matar da zan aura ne".
ta zaro ido ta girgiza masa kai, ta ce "idan yadawo zai k'iraki".
Katse kiran tayi ta na kallonshi, ya haɗa rai ya ce "nace kidaina kallo na ko, idan ina tuk'i bana amsa k'ira, nasan maganar aure zatamun shiyasa nace ki faɗi haka".
Dariya ta tuntsire dashi ta ce "babba dakai bakada mata".
murmushi yayi ya ce "to wazan aura, bana iya magana da matane".
"meyasa".
"bansanni ba, haka naga inayi".
dai2 lokacin suka iso, yana faka motar tafito da sauri ta nufi ɗakin, duk dogon rigar yagama isarta, tana alla2 taje ta cire, Lidia tana ganinta ta washe baki ta ce "kun dawo"?
murmushi tayi mata ta ce "eh".
Dariya yayi ya kaɗa kai ya ɗiɓi kayanda suka siyo yanufi ɗakin dashi, lokacin har ta shige wanka, ijiyewa yayi ya fita abunshi.
.
.
.
Momi ce zaune a gaban Ammi suna lissafin yaushe Aisha zata cika Watanni uku suje, ganin ko wata batayi bane yasa duk suka k'agu tayi.
Ammi ta nisa ta ce "ranar munyi maganar Faruq bakice komai ba, kinsan duniya kana naka wani yana binka da sharri, ni a yanda na fahimta ba banza zai aikata haka ba".
Momi tayi ajiyan zuciya ta ce "wlh nima ina wannan tunanin, narasa abunyi ne kawai".
Ammi ta ce "idan Abbahn nasu yadawo zan mishi magana, sai a ɗauko malami a masa karatu, ko akwai aljanu a ciki ko sihiri, yanda naganshi a hargitsennan gaskiya akwai wani abu".
Haka kuwa akayi, malam Hassan dake bayan layinsu suka ɗauko, shima Abbahn baiyi musuba, karatu yayi masa sannan ya bashi adduo'i, hatta ruwan shansa ya zama addua ne, yayi masa faɗa sosai akan ya kula da ibadansa, zasuyi ta karatu har natsawon kwana 7.
Tunda aka fara suka fara ganin canji, gaba ɗaya nutsuwarsa ta fara dawowa, wani iri yakeji, yana jin zafin rabuwarsa da Aisha, har kuka yake zama yayi wa Momi akan a taimaka adawo masa da ita, Momi mamaki ya cika ta, watau dagaske sihiri ne, to waye da wannan aikin, tadai bar mutum da Allah kawai, ta duk'ufa wajen rarrashin ɗanta.
"Faruq, ka nutsu kaji me zan faɗa maka, saki uku kayiwa Aisha, me zata dawo tayi maka".
"Mom ai nasani, lokacin nakasa kai zuciyata nesane, amma yanzu zan iya jure komai Momi, kome tamun zan zauna da ita a haka".
momi ta kama baki ta ce "kanka ɗaya kuwa Faruq, ana gyara saki uku ne ko me"?
ganin bashida niyyar daina sumbatun tace "kaje gidansu saika faɗa musu".
A k'ofar gida yasamu Abbah da jarida a hanunshi, ya tsuguna har k'asa ya gaishe shi, da fara'a Abbah ya amsa ya ce "yaya Momin taka".
Sunkuyar dakai yayi yana susa kai ya ce "dama ita ta turoni, wai.. Wai dama Aisha...".
nanda nan Abbah ya ɗagoshi, ya ce "kada kafara wannan maganar, saki uku kayi mata, a yanzu batada maraba da mahaukaciya, me kake ayi maka".
Kuka ya fara k'asa2 kamar yaro, yana tsananin tausayin Aisha, har cikin ranshi yaji maganar, gashi babu aure a tsakaninsu, Allah ya isa yayi ta ja a zuciyarshi, Abbah sarkin tausayi, ji yayi ya bashi tausayi, musamman daya tuna cewa ba laifinshi ba ne, ya dubeshi da kyau ya ce "
Babu aure a tsakaninku, kafin ta warke nasan lokacin ta gama iddarta, kai kuma zanyi maka fatan samun wata kamarta".
Yana faɗin haka ya shige gida abunshi, AMMI dake tsaye a bakin k'ofa tana baiwa Sadiya aika Abba ya shigo, bayani yashiga yi mata, tayi salati ta ce "ni dama nasan ba laifin yaronnan bane".
Faruq ɗinne ya shigo duk suka zuba mishi ido, Abbah ya ce "wani abune".
Tsugunawa yayi a wajen yana hawaye ya ce "bazan iya tafiya ban baku hak'uri ba, tabbas kun mun karamci sosai, wlh ni kaina sai yanzu nake dana sanin abunda na aikata, amma nayi alk'awari zan ɗau nauyin jinyar tata har ta warke, kuma ko a haka tasamu miji zata iya aurenta, saboda babu iddah akanta"....
Wangale baki Ammi tayi, "tsawon shekaru uku Faruq kace babu iddah? Me kukayi to"?
Susa kai yayi kunya takamashi kamar ya nitse, Abbah yayi murmushi ya ce "kajiki da wani magana, wannan bata taso ba, bincike ya nuna anshiga tsak'aninku ne, banga laifinka ko ɗaya ba, zan sake maka alfarma a karo na biyu, ka nemi auren k'anwarta SADIYA idan ta amince ni kuma zanbaka".
Da sauri Sadiya ta sake baki tana kallon Abbah, shima Faruq ɗin shi yake kallo, wannan mutumin ya shammaceshi da yawo, bai isa yace masa a'a ba, shidai yasan Aisha kawai yakeso ba wata ba, murmushi ya k'irkira da iya kacinsa fatan baki ya ce "Nagode Abbah".
Comments
Post a Comment