NI AYS NAKE SO 24

������
      �� *NI AYS NAKESO*��
                 ������
Page 24

.


.

.



_WRITEN BY Princess Eshat Aysm_

.

.

In Dedication to *ABDULLAHI YAHYA SA'AD ZARIYA*
A.Y.S







.




.

.







Jiki a sanyaye yabar gidan, ita kuwa Sadiya tsananin tausayin Aisha ne yasake kamata, share hawaye ta farayi Abbah yace "kukan menene kuma, idan bakiso bazan miki dole ba, yabani tausayi ne, mutane basuda imani ko kaɗan, amma nafi tunanin aljanin yaronnan ne zaiyi haka".
Ammi ta ce "wani yaro kuma".
ya kaɗa kai na takaici ya ce "yaronda ta haɗu dashi wai AYS ne ko waye, ranarda yazo daga ganin k'wayar idonshi zai aikata haka".
Ajiyar zuciya ta sauk'e ta ce "Allah yasa hakan yazamo mana alkairi".
Duk sukace "Ameen".
Abbah yace "kina sonshi ko kuwa"?
Zunɓura baki tayi ta ce "ni bana sonshi".
Ammi tayi dariya ta ce "tafi abunki ki barshi, haka ake tambayar".
murmushi Abbah yayi kawai.

.
.
.
.

Tunda daga ranar ta fara mak'alewa Dr.Abdul idan  zai tafi tare suke tafiya, idan baizo ya ɗauketa ba tayi ta kuka kenan, su kuma abunda basu so kenan kada ciwon yadawo, da safe idan yabata magani tasha tare zasuyi ta zagaya wajen, babu wanda zai ganta yace jinya aka kawo ta, ahaka har tafara gane kan aikin nasu, ta fara gane matsalar kazane ake bada magani kaza, ko National zai tafi tare suke tafiya, tayi ta raba ido, wani lokacin tasa masa rigima ita dole akaita wajen Abbanta da Ammin ta, dak'yar suke shawo kanta.
Watanta biyu sukayi wani irin shak'uwa da ita, Dr Mansur tunda yatafi Sudan bai dawo ba, saidai suna waya kullum da Dr Abdul.

Lidia kuwa tajata a jiki sosai, A hankali musulunci yafara shiga jikinta, saboda Aisha bata wasa da ibadanta ko kaɗan, duk abunda takeyi bata manta Allah, dare kuwa rabashi takeyi ta kwana tana Ibadarta.


Abu ɗaya yake damun Abdul yanda tunanin ta yake nema yafi k'arfinshi, dazaran sun rabu zai fara tunanin ta, duk wani nutsuwar shi ya koma kanta, a baya babu abunda yake hanashi tunanin Ayshar sa datayi aure, sai haɗuwarsa da wannan Aishar a faɗansa.
Ganin bacci yak'i zuwa masa ya ɗau wayarshi ya hau Fcbk, yakan juma bai hauba, saboda aikinsa yayi yawa yanzu, ɗan murmushi ya sake tuno abubuwa da yawa da yayi, mssg ɗin dayak'i buɗewa kusan wata guda yace bari ya duba yagani, ganin sunan Aisha ne saida gabanshi ya faɗi, sallamace kawai amma saida yaji hawaye yafara sauk'o masa, a fili ya ce "nayi rashin abunda nafiso fiyeda komai nawa, Allah ya baki zaman lafiya ESHA ta".
Kamar zai sauk'a sai kuma ya tura " _ESHA kinada aure, don Allah kada kisake mun magana_".
Runtse ido yayi yana tunanin tsawon shekaru uku yakasa cireta arai, ɗan tsuka yayi ya ce "Allah yagani nayi k'ok'arin cireta nakasa".
Dak'yar bacci ya ɗaukeshi donma ɓarawone.






Ta idar da Sallar asuba kenan tana shirin shiga wanka taji an bauɗe k'ofar, da sauri ta juya don ganin waye, Dr Abdul ne, shi kanshi baisan yaya akayi ya taho ba, suna idar da Sallah ya figi motarsa ya taho, bak'ar jallabiyace ajikinsa me haɗe da hula, binshi tayi da kallo har yanemi waje ya zauna bata daina kallonshi ba, haɗe rai yayi irin borin kunyarnan, tayi murmushi ta ce "yau da wuri zamu tafi kenan, amma naga baka shirya ba".
Daɗa ɓata rai yayi ya ce "kiyi abunda zakiyi, nazo duba wanine".
shiru tayi tasan duk saurin dayakeyi sai yasaka Unifoam yake fitowa, ganin tana tsaye yasa ya mik'e, a hankali ya taka har inda take, bakinta ya kama yaɗan murɗe, ai kuwa taji zafi sosai ta k'wala k'ara saida Lidia ta farka tana zare ido, ya ce "idan kika sake ganina baki gaisheni ba saina cire bakin".
kuka ta fashe dashi sosai, wani tsawan yadaka mata "kewai kullum sai kinyi kuka ne"?
kukan taci gaba dayi abunta, ya runtse ido ya toshe kunnuwansa yana mata dariya, Lidia har tasaba da faɗansu, dariya tayi tashiga bayi ta barsu a wajen.
dai dai kunnenta ya raɗa mata "idan bakiyi shiru ba bazanje ko ina dake ba".
harara ta watsa masa ta zunɓura baki ta ce "don Allah ka kaini gida tunda na warke, ko Abbah na ka 'kiramun naji muryarsu".
shiru yayi yana nazari, can ya ce "banida numban".
da sauri ta ce "inadashi".
mik'a mata wayar yayi ya ce "ki k'ira kafin nadawo kin shirya, yana faɗin haka ya fice.
tsalle tayi tana murna, abun haushi tayita k'ira a kashe, kuma numban kawai ta haddace, jiki a sanyaye ta ajiye wayar, lokacin Lidia har tayi wanka ta fito, itama wankar tashiga, tana fitowa ta samu har tajera mata abun karyawa, cikin k'ank'anin lokaci ta shirya, cikin riga da siket, siket ɗin har k'asa, rigar ta ɗan kamata kaɗan, Lidia ta bita da kallo ta ce "kinada kyau".
murmushi tayi mata ta ce "nagode".
jakar kwalliyarta ta jefa mata ta ce "kiyi kwalliya zakiyi kyau".
bataso ba don dai batason musu da mutane shiyasa tayi yak'e tafarayi, hijab tasaka meɗan girma, wayar taɗauka tasake k'ira amma akashe, me makon ta ajiye sai tafara masa bincike, duk pix ɗinsa ne a wayar, yana masifar yimata kyau, ita kaɗai taketa murmushi, anan taga Umman tasa, suna kama sosai, gajiya tayi da kallon photonan tasauk'a ta kunna data, kamar mayya ta haura fcbk nasa, zatayi log out ta haura nata taga sunanda ya girgiza ta.

Comments

Popular posts from this blog

Australian Visa Application information: Visa Types & Requirements

[Sunnah] What Muslim Should Observe On The Day Of Eid

Canada Immigration: How To Apply For Canada Permanent Resident Visa