NI AYS NAKE SO 25

������
      �� *NI AYS NAKESO*��
                 ������
Page 25

.


.

.



_WRITEN BY Princess Eshat Aysm_

.

.

In Dedication to *ABDULLAHI YAHYA SA'AD ZARIYA*
A.Y.S







.




.

.







Ware ido tayi sosai taga dagaske ABDULLAHI YAHYA SA'AD tagani, da sauri ta fara bincikawa, babu tamtama shine, hawayene tare da dariya suka gauraye fuskarta, ta manna wayar a k'irjinta tana kuka sosai, lallai yau ta yadda *SO AJINI YAKE.*
Tunda taganshi taji yafi kowa burgeta, ashe Ays ɗinta ne, dariya kuma sai ya suɓuce mata tashigayi babu k'akk'autawa, Lidia ta tsura mata ido tana tausayin ta, tana tunanin ashe har yanzu bata warke ba.



Tana cikin wannan yanayin ya shigo, da sauri ta ɗaga ido tana kallonshi hawaye nabin kumatun ta, jiki a sanyaye ya matsa kusa da ita ya ce "banson kukan nan Esha".
Kallon shi tashiga yi sama da k'asa kamar taga sabon abu, hanu yasa ya zare wayar a hanunta yana cewa "kullum sai kinyi kuka bansan matsalarki ba".
Tsurawa wayar ido yayi, lokaci guda ya haɗe rai ya ce "meyasa kika shiga nan"?
Wani irin sonshi ne taji yana ratsa ta, fuskarta ɗauke da murmushi ta ce "bani nashiga ba, gani kawai nayi".
Yanayin kallon datake mishine ya burgeshi, murmushi yayi ya ce "mutafi".
Juyawa yayi da niyyar fita, sai ji yayi ta ɗale bayanshi tana dariya, a kiɗime ya fara k'ok'arin cireta amma ta k'ank'ameshi, bata daina dariyar ba sai lafewa datayi a bayan.
ya kama kanshi yanajin wani abu yana mishi yawo, Lidia ta ce "nifa inaga wani matsalar ta samu".
A hankali ya ce "sauk'o kiji".



Sauk'owa tayi ta ce "kayi hak'uri, bansan lokacin da nayi hakaba".
Hancin ta yaja ya ce "kincika rigima".
Murmushi kawai tayi yayi gaba tabishi a baya, kamar kullum saida yagama duba kowa suka wuce ɗayan asibitin, tunda suka ɗau hanya ta zuba mishi ido, har yafara tsarguwa ya ce "kidaina kallo na".
A hankali ta ce "bazan iya dainawa ba".
Da sauri ya kalle ta, ganin idonta yaciko da hawaye ya ce "haba mana, menene na kuka kuma, kiyi ta kallona to".
Yana magana tanabin bakinshi da kallo, batasan tanason AYS ba sai yanzu, runtse ido tayi tana tunanin iko na Allah  da ya kawota wajenshi cikin sauk'i, a hankali ta ce "nagode Faruq".
mamaki ya kama shi, lokaci na farko dayaji yanaso yasan wanene Faruq ɗinnan.
har suka isa baice mata komaiba,











Da yake babu aiki sosai ranar lahadi Office ɗinshi suka wuce yafara bincike akan Computer, tana zaune daga can gefe tayi tagumi tana kallonshi, bai ɗago ya kalleta ba yace "Aisha, meyasa kike kallona dayawa".
Ajiyan zuciya tayi ta ce "inaso in maka tambaya ne, ranar naji kace bakada mata".
barin abunda yakeyi yayi yana kallonta, ya ce "eh inajinki".
"gani nayi yadace ace kanada ita, don Allah kabani labarin ka".
Tunda suka fito yana mata kallon me taɓin hankaline, amma yanzu yanda take maganar a nutse ya tabbatar lafiyanta k'alau.
Kallon ta yayi naɗan lokaci ya ce "a wani dalili".
Shiru tayi kafin ta ce "akwai dalili da yawa, nayi maka alk'awarin zaka sani bayan naji abunda na tambaya, abu ɗaya nakeso shine ka yadda dani".
Nutsuwarta yayi matuk'ar bashi mamaki, har wani kunyarta ya fara ji, ya lumshe idanuwansa kafin ya waresu a kanta.
"a tak'aice ni mutumin Zaria ne, acan nayi karatuna, iyayena ba wasu masu k'arfi bane, don haka makarantar danakeyi bawani me tsada bane, amma inada k'wak'walwa sosai...



Kusan zan samu addmsion na haɗu da wata, bansan kamannin ta ba amma syyr ta me tsananin zafine ya kamani, in tak'ai ta miki ranarda naje garinsu a ranar aka ɗaura auren ta, dani aka ɗaura bansani ba, koda nadawo saida nashafe wata bani ci banasha, suma kuwa nayi yafi misali, ina cikin wannan halin na tafi karatu a ABU ZARIA, anan na haɗu da Mansur, yanada mutunci sosai, munshak'u dashi sosai saboda yanda yake kula da damuwata sai ya zamto bana iya ɓoye masa komai, saboda tunanin yarinyar sai ya zamto bana gane komai a makarantar, duk wani k'ok'arin iyayena hakan baisa namaida hankali ba, soyayya ce bana wasa ba ya kamani, Mansur kuwa dama bashida wani basira sosai balle ya ganar dani, mahaifinshi yanada kuɗi sosai, dama babu inda baiyi ba akan ya turashi waje yayi karatu yace yafiso a garinsu, k'arshe dole ya tilastashi ya tafi can yayi karatu, nan mansur yace bazai iya rabuwa dani ba, babu yanda ba'ayi ba dole mahaifinshi ya haɗa dani muka tafi, tafiyata can yarage mun tunanin abubuwa da dama, kuma wanda yaɗau nauyin nawa bazaiji daɗi ba idan na koma ban tsinana komai ba, cikin shekara ɗaya nazama wani a makarantar saboda tsananin k'okarina, Mansur ma ba laifi ina tursasa masa yayi karatu, shekaru huɗu akeyi amma shekaru biyu nazarce 'yan gaba dani, wannan dalilin yasa mahaifin Mansur ya gina mana Asibiti, shine wanda aka kawo ki, *MANAYS*
Sunan mansur da nawa aka haɗa, har yanzu ban manta ta ba, kuma inbanda mahaifinta bansan kamannin ta ba, wannan shine ni a tak'aice".
tana share hawaye da tsananin mamaki ta ce "Kana wajen aka ɗaura aurenta, kuma da gaske kaga mahaifinta"?
ɗaga mata kai yayi alamar jaddada wa, zatayi magana ya ɗaga mata hanu "tambayar ta isa".
murmushi tayi ta ce "menene dalilin ka nak'in neman wata".
hararta yayi ya ce "tashi nakaiki".

Comments

Popular posts from this blog

Australian Visa Application information: Visa Types & Requirements

[Sunnah] What Muslim Should Observe On The Day Of Eid

Canada Immigration: How To Apply For Canada Permanent Resident Visa