NI AYS NAKE SO 26
*NI AYS NAKESO*
Page 26
.
.
.
_WRITEN BY Princess Eshat Aysm_
.
.
In Dedication to *ABDULLAHI YAHYA SA'AD ZARIYA*
A.Y.S
.
.
.
Ba musu ta mik'e fuska a ɗaure, da gani taji haushi, sai kuma yaji ba daɗi, haka yaɗau keys yayi gaba.
da suka isa ko kallonshi batayi ba tawuce, kifa kanshi yayi yanajin wani iri, wunin ranar cikin kasala yayi ta, gashi yakasa zuwa ya bata amsar tambayar datasa ta fushin, tayi masa kyau sosai fiye da kullum, fuskarta yayi ta hangowa a zuciyarshi, ana idar da Sallar magriba ya koma gida yayi wanka, coffe kawai ya haɗa yasha ya koma Asibitin.
Tana cikin rera karatu Lidia tana gabanta tana sauraro ya shigo, gefen Sallayar ya zauna yana kallon Qur'anin, yana ɗaya daga cikin abunda yasa take burgeshi, ko kallonshi batayi ba harta gama karanta shafin, hanu ta ɗaga tana addua duk da baya ji haka yayi ta cewa Ameen.
Lidia ma Ameen ta ce sannan tajuya tana gaida dashi, ba yabo ba fallasa ya amsa, takaddan hanunshi ya mik'a mata yace "kimun typng".
karɓa tayi ta fita da hanzarinta, kai idonshi yayi kan Aisha ya ce "Ashe kema kin iya fushi ne"?
Harara ta watsa masa ta kauda kai, ya kiɗeme ya ce "me kikeso yanzu"
Zunɓura baki tayi ta ce "Gida zaka kaini".
wani malalacin murmushi yayi ya ce "nifa bani na kawoki ba, idan wata uku tayi nasan Abbahn ki zaizo dubaki, tunda kin warke kinga sai kibishi basai kinyi wata shida ba".
"yanzu watana nawane"?
ya ce "watanki biyu".
yamutsa fuska tayi ta ce "Allah ya kaimu".
Zata mik'e ya rik'o hanunta ya ce "ina neman alfarma, kidaina fushinnan kinsa kaina ya fara ciwo".
dara daran idanuwanta ta sauk'e akanshi ta ce "nadaina, amma nima kadaina mun haka".
murmushi yayi ya ce "nadaina".
duk da baisan me take nufi ba.
Hancinshi taja tana dariya, dariya shima yayi yace "kin ramane"?
Kaɗa mishi ido tayi ta ce "kanaso na ramane"?
girgiza kai yayi yana dariya, ba k'aramin kwanciyar hankali ya samu ba, yarasa me yake damunshi game da ita, itakam jin daɗinta yafi a misalta, tunda ta gane Ays ɗinta ne, takejin kamar sonshi zai huda k'irjinta.
.
.
.
.
NIGER
"Unaisa badake nake magana ba, wani irin amai kikeyi kwana biyunnan, gaba ɗaya kin canza, da anyi maganar asibiti kifara zunɓura baki".
Zunɓura bakin tayi ta ce "Mama nifa nakejin ciwonnan, idan naga ban warkeba ai dole na tafi asibitin".
"to ai shikenan jiki magayi".
Sallamar Kareema ce ta katsesu, da dariya tagaida Maman suka shige ɗaki.
Ko zama batayi ba ta ce "ke nazo da wani zance kuma naga kin wani rame kin k'ara fari".
Unaisa ta ce "faɗan zancen naji".
"ba zama nazoyi ba rakani zakiyi wajen Malamin nan".
Kareema ta ɓata fuska tace "nifa ba inda zani, bana faɗa miki abunda yamunba, kuma haryanzu babu wani bayani".
Kareema ta sauk'e ajiyar zuciya ta ce "kinga sai mu faɗa masa, nifa yanzu gaba ɗaya Yazeed ya canzamun, jiya har dukana yayi".
Unaisa ta ce "duka? Yazeed ɗin? Bamuci ta zama ba".
Da sauri tashirya suka tafi, ko nisa basuyi ba ta fara kwarara amai, ba k'aramin ruɗewa kareema tayi ba, ta ce "k'awata haka kike amai dama, mu wuce asibiti kawai".
Jiki ba k'wari Unaisa ta mik'e, ba musu suka nufi asibitin, gwajin farko aka faɗa mata tana ɗauke da ciki, tun a wajen ta fara rusa kuka, tanayi Kareema tana taya ta, a haka suka nufi gidan Malamin nasu.
basu samu kowa a gunba don haka suka shiga kai tsaye, yana ganinsu ya fara dariya, ganin suna kuka yasa ya tsagaita yashiga tambayarsu, sanar mishi sukayi Unaisa tanada juna 2, me makon ya ɓata rai sai ya wani washe baki, yasan cikinsa ne tunda shi ya ɓare ta, kallonsu yayi ya ce "me sauk'ine ai, basai a cire ba".
Da sauri Kareema tace "yauwa a taimaka mana a cire".
Wani dariyar yayi ya ce "aljanin dare zai cire, sannan ina miki albishir nanda sati biyu za'a ɗaura aurenki da Faruq".
Wani bak'in cikine ya kamata ta ce "nidai damuwata yanzu a cire cikin, wazai aureni da cikine ma".
Jaddada mata dole sai ta kwana yayi sannan a cire, dole ta amince babu yanda ta iya.
Koda Kareema ta faɗi matsalarta wani maganin yabata, ta tafi tabar k'awarta tana godiya, daren ranar Malam yasha aiki akan Unaisa ko ran farko batasha wahala haka, tunda yagane tanada daɗi yakasa barinta, kwana yayi yana abu ɗaya, washegari tanaji tana gani ya hanata tafiya, daren ranarma ta ciyu, tun tanajin abun da zafi harta yafara mata daɗi, dazai kaita yayi mata wanka da ruwan magani, na toshen bakin iyayenta kada su tambayeta ina taje, kuɗi ya tula mata ya ce duk abunda takeson ci taci, bayan sati cikin zai zube.
Comments
Post a Comment