NI AYS NAKE SO Part 12

💅💅💅
      💋 *NI AYS NAKESO*💋
                 💅💅💅
.page 12
.

_WRITEN BY Princess Eshat Aysm_
.
.
In Dedication to *ABDULLAHI YAHYA SA'AD ZARIYA*
A.Y.S

Page 12
.


.
.





*SADDIQA MUNIR*
😭😭😭😭😭😭😭😭😭Allah yatsine miki unaisa algunguma Aisha sai Ays😀 kigama haukanki ta auri masoyin gaskiya🤣 *NIMA AYS NAKESO*
Eshaert inasonki har cikin raina tun a shimfidar mijina Allah Albarkaci zuriarki sista😘
_siddiqa nadaÉ—e ina ganin sak'onki nagod sosai_
*NI AYS NAKESO ai yanzu labarin ya fara, ina k'aunar duk masu turomun sak'onni, ina gani sak'onku nagode da addua*
.
.
MARIAM _naga sak'on ki ta gmail Allah yabarmu tare_.



.
.

Ganin ya nufota yasa tarufe k'ofar tasa key, zama tayi a wajen ta fara kuka kamar Allah ne ya aikota, babu irin buga k'ofar dabaiyi ba amma tak'i buÉ—ewa, cikin k'unan rai yabar wajen yanufi É—akin shi, zama yayi a bakin gado ya kama kanshi, kishine ya turnuk'eshi, sunan Ays kuwa ya nanata yafi sau 20 "waye shi"?
Dabarane ya faÉ—o mishi yayi murmushi tareda mik'ewa.
"Aisha bata sona haryanzu, menene banidashi wanda takeso"?
ShikaÉ—ai yake magana har ya isa k'ofar É—akin Unaisa, a kaushashe ya k'ira sunanta, saida hanjin cikinta ya kaÉ—a, amma ta dake ta ce "Nifa kaina ke ciwo bacci nakeji".
Wani uwar harara ya watsa mata "ke kinada hankali kuwa, ina k'iranki kinamun banzan magana".
Binshi tayi da kallo duk ya futa a hayyacinshi, dariyan cikin zuciya tayi, "dole na iya takuna idan yagane k'aryane kashina ya bushe, wani abuma saina aureka yaro wannan É—aure fuskar taka zanyi maganinshi...
Tsawar daya daka matane yasa ta saita nutsuwarta.
"ki bani numban Ays É—in yanzu...
Wani zaro ido tayi ta ce "Haba yaya, akan É—an abunda nafaÉ—a maka shine harda neman numba, nafaÉ—a makane kaÉ—au mataki badon kayi bincikeba, tunda kaji na ambaci AYS kaima kasan ba k'arya zanyi makaba".
Sake baki yayi yana kallonta, yanaso ya ya cusawa zuciyarsa cewa k'arya take masa amma ina babu zancen k'arya a ciki, komawa tayi ta kwanta tabarshi a wajen.
kanshi ya É—au zafi dayawa, haushin Aisha ne duk yacikashi, yanaso yasamu sanyi a ranshi amma yasan bazai iya faÉ—awa Momi wannan maganar ba, duk wani hukuncin daya yanke sai yaga bazai yiyuba, tun farko ya bari Aisha tasoshi kafin ayi aurensu amma aka É—aura bai saniba, a hankali hawaye ya fara wanke fuskanshi, hukunci É—aya ya yanke, dole zaiyi nesa da ita, bazai bari zargi ya shiga rayuwarsu ba, amma yasan dole wataran zata soshi, da wannan tunanin ya tafi masallaci.
A ranar kwana Aisha tayi bata runtsa ba, duk tunaninta Faruq matsala yasamu, duba datayi yana masifar sonta tasan ba abune me yiyuwa ya daketa ba, da tunani kala kala ta kwanta, ganin babu bacci a idonta yasa ta ɗauro alwala tahau sallah, har asuba sannan tayi karatu sosai, ta juma tana addua kamar yadda ta saba, wanka tacaɓa tasaka wani shadda shuɗi, tayi kyau sosai dukda ba iya ɗauri tayiba dayake shaddane sai tayi kyau, cikin sanɗa tafara lek'e, bataji motsi ba don haka tayi sashin Momy da gudu, a kitchen ta sameta tana fere dankali, ta tsuguna ta gaisheta, fuska a sake ta amsa ta ce "yau dai kin tashi da wuri, ko tare zaku futane, gashi can kwance a falo bacci ya ɗaukeshi".
Murmushi kawai Aisha tayi sannan ta shiga
tayata aikin, har suka gama hankalinta nakan taje ta duba Faruq.
Bayan sun gama ta kwashe taje tajera komai a yanda ya kamata, ganin Momi tayi ɗaki yasa taje kusa da Faruq da sauri, tsugunawa tayi a gabanshi ta zuba mishi ido, kyakkyawane fari k'al dashi, bata taɓa ganin kyawun shi ba sai ranar, lokaci guda taji sonshi ya fara fizganta, ɗan murmushi tayi takai hanunta kan suman kanshi da niyyar taɓawa, Mom ce tafito a lokacin, tana ganinta ta wayince tafara bugashi, wai ya tashi yaci abinci.
Wucesu Momi tayi tana cewa "idan yafara bacci baya gajiya kuma ahakan cemun yayi zai tafi gun aiki da wuri".
Abun mamaki hawaye ne taga yana sauk'owa daga idonshi yana gangarowa kumatunshi, a razane ta mik'e don ita bata É—auka maza suna kuka ba, hanunta ya fizgo yace "ina zakije".
Girgiza kai tayi dukda idonshi a rufe yake.
"kin kasa gane menene so, bawanda zai soki kamar ni, kina cutana kin É—auka asirinki a rufe yake, to kisani nasan komai Aisha, nasan wataran zakiyi nadaman saka wani aranki ba niba".
A kiɗime take kallonshi, bakinta na ɓari ta ce "me nayi maka, me yakawo wannan maganar".
Unaisa ne ta fito tare da Momi, dama k'iranta tajeyi, ganin hanunshi cikin na Aisha saida ranta ya sosu, watau duk wannan sharrin datayi mata bai damuba, lallai wannan É—an bala'i ne, amma dani suke zancen.
Shikam dabara yayi ya goge hawayen fuskarshi, a É—arare yaci abincin, Mom tana kula dashi duk hankalin ta ya tashi, "Son bangane yanayin ka ba, ko akwai matsala ne"?
Murmushin dole yayi ya ce "Transfer za'a mun awajen aiki shiyasa duk naji kewarku ta fara kamani".
cikin kulawa ta ce "wani irin trnsfa kuma Faruq".
Shafa kanshi yayi ya ce "yanzu dai ina sauri idan nadawo sai muyi maganar".
jiki a sanyaye ta ce "
Allah yabada sa'a".
Unaisa har wani zufa tafarayi, shikenan zai ɗau matarshi subar garin, kowa da tunanin da yake ranshi, yana mik'ewa Aisha tabi bayanshi, magana take mishi yayi banza da ita, cikin k'ank'anin lokaci yagama shiri ya tafi, zama tayi tayita rizgan kuka, maganganun shi da shareta da yayi sunfi komai taɓa mata rai, har aka k'ira azahar bata motsa ba, koda yadawo ma bata saniba.
Shikam transfer ya nema aka turashi Lagos, dak'yar yasamu yayi nasara aka turashi wajen, Momi tayi bak'in ciki sosai, tasaba zama da É—an nata zatayi kewarshi, koda ta masa maganar Aisha cewa yayi bazai tafi da itaba saboda karatun ta, ajiyan zuciya tayi sannan tayi masa fatan alkairi.
Ranar Monday ya tafi abunshi, yariga yasawa ranshi sai Aisha tagane matsayinshi azuciyar ta zai dawo, idan yaci gaba da zama to tabbas zargi zai shiga tsakani, daganan saki yabiyo baya, shikuma abunda bazai taɓa iya aikatawa ba kenan, yanajin son Aisha a ranshi tamkar mashi, yariga daya tokareshi babu abunda zai iya cireshi.
ba Aisha ba hatta Unaisa saida tayi kukan tafiyar, ba kunya tacewa Momi zata koma Niger, Mom bata kawo komaiba tafara yimata shirin tafiya, itama kwana biyu tsakani ta koma Niger.
Malam Umar zaune a tabarma larai tana yanka mishi kankana sukaji ihun yara ana oyoyo, duk suka zuba kunne suji waye sai ganin Unaisa sukayi da kaya nik'i2, da fara'a mahaifin ta ya ce "yau zaki dawo ko waya bakiyi kin faÉ—a ba".
Zama tayi a jikin Maman ta ta ce "nafiso ku ganni nasan kunyi kewata".
Larai ta ce "ni kuma me zai kaini kewarki, mahaifinki dai da baya gajiya da sa maganarki".
B'ata rai tayi ta ce "mama ni wai me nake mikine".
"rabu da ita yanzu tagama surutun yaushe zaki dawo, tafini kewarki ma".
Duk sukayi dariya sannan suka shiga gaisawa, suka tabayeta ya tabaro su Momi tace lafiyansu lau.
Lafiyayyen gadon ta tabi ta kwanta tana sauk'e gajiya, wayarta ta ciro a jaka ta cire sim É—in ta mayar da asalin nata.
Sak'onnin k'awayen ta sukayi ta shigowa, don ita dama bawani saurayi takeda shi ba balle tadamu, sak'on k'awarta É—aya ta buÉ—e KARIMA.
Murmushi tayi kafin ta k'irata ta shaida mata ta dawo, cikin farinciki Karima ta ce "shegiya sai yau, gobe ina zuwa kunce jaka".
"wani jaka zaki kunce, ai jakar gaba ɗaya taki ce, kedaivsai kinzo akwai ƙlabari fa".
karima uwar son gulma ta ce "k'awata fara faÉ—amun mana kinsan bana iya bacci idan akwai labari ba'a bani nasha ba".
Dariya Unaisa tayi tace "ki kwana a zaune shegiya kawai".
Daganan ta kashe wayar tana dariya.

Comments

Popular posts from this blog

Australian Visa Application information: Visa Types & Requirements

[Sunnah] What Muslim Should Observe On The Day Of Eid

Canada Immigration: How To Apply For Canada Permanent Resident Visa