NI AYS NAKE SO Part 13


      *NI AYS NAKESO*
                
Page 13
.
.
.
_WRITEN BY Princess Eshat Aysm_
.
.
In Dedication to *ABDULLAHI YAHYA SA'AD ZARIYA*
A.Y.S



.
.
.



Karima tazuba tagumi lokacin da Unaisa tagama kwararo mata bayani, "k'awata kin bada ni wallahi, tun kina k'arama kikeson abu amma kin kasa taɓuka komai, kin badani Unaisa".
Unaisa ta sauk'e ajiyan zuciya ta ce "kin kasa ganewa, Faruq ba kamar maza bane, duk kyawuna shi baya gani, saima kinga yarinyar dayake aure".
Karima ta ce "
yanzu babu wani mafita sai abu ɗaya, kinga wajen da kika rakani ranar akan haɗuwata da Yazeed, wajen zamuje, Faruq zai soki fiyeda komai, babu ruwanmu da matarsa tunda ba sonshi takeyi ba".
Unaisa ta k'walalo ido waje "kibar wannan maganar Kareema, wannan mutumin fa boka ne, idan Mama taji sai tayi kusan kasheni, ni nafison muyi 'yar dabara kawai".
Wani kallo kareema tayi mata sannan ta ɗauki jakarta ta ce "kinga tafiyata, mutumin da kika zauna dashi bai sokiba sai yanzu da baki kusa dashi, kina ganin yanda Yazeed yake ɓare2 akaina yanzu".
Rik'e hanunta Unaisa tayi ta ce "kefa banzace memakon ki k'arfafa mun gwiwa saiki wani tashi zaki tafi".
Wani murmushi Kareema tayi ta ce "kinfini sanin ciwon kanki, idan kin hak'ura da Faruq ɗin basai natafi ba, ke ba'a baki shawara kullum sai munyi faɗa, kinma ɓatamun rai dabaki san waye AYS ba har kika taho".
D'an tsaki Unaisa tayi tace "tsaya mutafi yanzu, sai nace rakiya zanmiki".
"yauwa k'awata ko kefa".
(Allah ya bamu k'awaye nagari).
Tafiyar 30mnt sukayi ko gajiya basuyi ba, kuma basu damu su hau abun hawaba saboda taɗin da sukeyi baya buk'atar katsewa, wani kamfacecen gida suka shiga, kana ganinshi kasan gidan wani shahararren me kuɗine, saida sukayi ta shiga kafin suka isa wani k'aramin ɗaki me ɗauke da buzu da tarkace, kan buzun wani mutumi ne rik'eda carbi, wai duk girman gidannan na wannan ɗan tsomarin mutumin ne.
gaisheshi sukayi ya amsa fuska a sake saboda yaganesu, baki washe ya ce "Karima ko".
Da sauri ta ce "eh malam, na rako k'awatace".
Kallon Unaisa yayi na tsawon lokaci sannan ya ce "muga tafin hannun ki".
Hannun ta mik'a mishi, yarik'e sannan yayi wata magana ko menene oho, kusan 10mnt ya sake hanun ya ce "naga komai,
ɗan uwanki kikeso, maganar gaskiya yanason matarsa sosai, abune me wahala ki samu wani gurbi a zuciyarshi, bazai so wata mace ba bayan wannan yarinyar".
Gaba ɗaya sun rikice, Karima tace "don Allah babu yanda za'ayi"?
Wani littafi ya ɗauko yafara rubuce2, tsawon lokaci ya ɗago yadubesu, ya ce "a halin yanzu babu wani abunda zaiyi tasiri a kansu, zanmiki aiki amma bazaiyi amfaniba har sai tsawon wasu shekaru...".
A ruɗe ta ce "shekaru kuma malam, kamar shekara nawa"?
Murmushi yayi yace "kamar shekaru 2 zuwa uku, naga yanzu basu tare, kuma akwai tsari a jikinta sosai, dazaran yadawo shine aikin zai fara".
Unaisa tashare zufa ta ce "ni na hak'ura...
Kareema ce ta dungure ta "ke ai shekarun babu yawa zaki karaya, malam zamu jira, menene sharaɗin".
Babu wani sharaɗi, zaku biya kuɗin bak'in saniya shikenan kuyi zaman jira".
Harda masa godiya kamar abun arziki.
.
.
.
Kewar Faruq yafi komai taɓa ta, idan antashi a makaranta su Hajara takebi suyi gida, sai yamma lis Momi take sawa a ɗaukota, zaman ta acikin k'annenta yana mantar da ita komai, Ammi kullum cikin mata nasiha takeyi, faɗanta baya wuce akan kada tazauna babu addu'a, Momi tausayin ta takeji shiyasa bata matsata, saida ta jera sati idan antashi tana bin gida sannan Abbah ya hana, faɗa yayi ta yi kada rashin hankalin yayi yawa.
A kwana a tashi babu wuya su Aisha angama sch. ko waya basu taɓayi da Faruq ba, itadai Momi tana kulawa da ita yanda ya kamata, idan ta matsa Faruq yazo ya ɗauki matarsa sai ya kashe wayoyinsa sai an kwana biyu ya kunna, don haka ta zuba musu ido kawai.
Result yana fitowa ta Nema mata addmision a Nursing School dake ATBUTH.
Faruq kullum sai Sunyi waya da Abbah, wataran harda su Sadiya yakance a basu, shiyasa sukeji dashi sosai, idan yak'ira Mom ɗinshi kuwa magana ɗaya yakeyi akan Aisha, kada abari ta rik'e waya, itadai to kawai takecewa tasan Faruq bashida daɗi akan kishi, watau yana tunanin kada tayi waya da wani ko, murmushi kawai takeyi aranta tace "yarinyar tanada kamun kai bazata saka mata ido ba".
Tayi ɗare ɗare akan computer tana bincike akan karatun ta, tunda ta gane kan computern ta samu abunyi, wuni takeyi ba'aji motsinta ba, bincike take akan ciwon da yashafi k'wak'walwa, bayan tagama dubawa har zata sauk'a wani photo ya tsaya mata a rai, Dr.ABDUL aka rubuta a k'asan, takai mintina 20 tana karanta bayanan k'asan wanda sam babu wani bayani a kanshi sai akan abunda yashafi aikinsa, tadai gane k'wararren likitan k'wak'walwane kawai.
Photon ta sake zoomin ɗinshi tana kallo, wankan tarwaɗa ne, ga wani gashi luf2 akanshi, yanada hanci sosai gashida manyan idanuwa, itadai likitoci suna burgeta amma taji wannan yayi bala'in burgeta fiyeda sauran.
"Astagfirulla".
Ta furta a hankali sannan ta kashe komai tashiga wanka, tana gama shiryawa ta nufi wajen Momi don ta farajin bacci, kuma acan take kwana acewarta gidan yamata faɗi da yawa.
"har angama karatun"?
Momi ta tambaya.
Sunkuyar dakai tayi tana murmushi ta ce "yau nagaji bacci nakeji, assgnment ɗinma nakasa yi... Wahala yakedashi".
Da kulawa Momi ta ce "kwanta kiyi baccin ki, ai ba'a karatu da zafin kai, idan kin samu nutsuwa sai tashi anjuma kiyi".
Kai ta gyaɗa sannan ta shige ɗakin Momi tayi kwanciyar ta itakuma taci gaba da kallon ta tana murmushi.
Alwala ta ɗauro sannan tayi addua ta shafa a jikin ta, ɗakinma duk ta tofe da addua sannan ta kwanta, amma me Fuskar Dr. Abdul ne yafara mata gizo, da sauri ta mik'e tana zare ido, wani dogon tsuka taja tare dacewa "Allah ya isah idan nasake ganinka".

Comments

Popular posts from this blog

Australian Visa Application information: Visa Types & Requirements

[Sunnah] What Muslim Should Observe On The Day Of Eid

Canada Immigration: How To Apply For Canada Permanent Resident Visa