NI AYS NAKE SO Part 5


       *NI AYS NAKESO*
                 
.
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
_We dont just entertain and educate we also touch the herts ƙf readers_
.
.

_WRITEN BY Princess Eshat Aysm_
.
.
In Dedication to *ABDULLAHI YAHYA SA'AD ZARIYA*
A.Y.S

Page 5
.


.


*Gaskiya ina raina cmmnt ɗinku sosai, kuma ni wannan tnx ɗin baya burgeni, sharhinku akan novel ɗin shine k'arfin gwiwata, dama saboda ku nakeyi menene amfanin ka karanta bazakayi magana ba, grups ɗin wtsp idan mutane goma ma sukayi magana bana damuwa, amma fcbk sai kaga grup fiyeda dubu goma amma cmmnt ko 50 bazai kaiba, nidai ku gyara ko kuma nadaina kawowa fcbk*


.
.
_ina son masoyana aduk inda suke, addu'ar da kukemun yana ratsa har zuciya ta, Allah ya barmu tare_
.
.
.
.
.
*AYSHA LOV*
*BILKISU BC*
*AMEENA MEENAH*
_MUCH LOVE_
.
.
.
.
.
.
.




.
.








Kwana 4 amma har lokacin Abbah baya kulata, kota gaishe shi baya amsawa, idan taje karatu ma korata yake yi, kanta kuwa kullum acikin ciwo yake yi, saboda tsaban kukan datakeyi, awajen k'annan ta da Ammi ne take ɗan samun sauki.
.
.
*Dare mahutar bawa*
Ammi ta zuba tagumi baccin ma yak'i zuwa mata, wannan shariyar da Abbah yake nunawa Aisha abun yana taɓa ta, tunda ya k'wace wayar sai ya hak'ura, dubanshi tayi taga baccin shi yake yi, mik'ewa tayi da niyyar barin ɗakin taji ya rik'ota,
"Haba Amina, meyasa kike damun kanki, kinsan duk duniya nafi kowa son Aisha, idan nabarta zata lalace, baki ganin tafi k'annan nata sakarci".
Ammi ta taɓe baki ta ce "tun farko kajata a jiki yanzu ka ɓullo da wannan hukuncin
Kullum da kuka take wuni".
harcikin ranshi yaji kukan nata, ya ce "Daga yau nadaina fushin shikenan nima adaina fushi dani ko".
murmushi tayi ta ce "ko kaifa".
Saida suka kwanta yace "yaron daya ɗauko ta a mota rannan ashe ɗan gidan BUZAWA".
Da mamaki tace "ayyah rashin sani".
"jiya yazo mun da wani magana, wai Aisha yakeso da aure".
Ammi tayi dariya tace "Haba2, Aishar nawa take, ai yabari ta girma tukun".
"nima abunda na faɗa mishi kenan ya nuna mun nataimaka Mishi yanda zan rik'e Aisha haka zai rik'eta, ganin ya takuramun na amince mishi, nima zan huta da ɓacin ran da take saka mini".
Tashi Ammi tayi rik'e da baki ta ce "ɗan wannan laifin har kana k'iranshi laifi, gaskiya kabarmun 'yata tayi karatu kafin".
"Amina har kin manta halin Aisha, duk ranar da zata fita sai ansamu wani ya biyo ta, yanzune da suke hutu samun kwanciyar hankalina, Auren nata shine gatan ta, kinga yaronnan bashida wani aibu donme zaki ɗaga hankalin ki".
"To amma Alhaji masu biyotannan fa ba ita take k'iransu ba, su suke biyota".
Ya nisa yace "yanzu dai nagama magana aure zanmata, gobe zai kawo mahaifiyar sa su gaisa".
Ganin bata sake fuskaba yasa ya shiga rarrashin ta har ta sauko, "Allah yasa hakan yazamo alkairi".
Washegari da sassafe Ammi tace musu zasuyi bak'uwa, gaba ɗaya suka hau murna don akwaisu da son bak'i saboda basu zuwa ko ina, daga gidan kakansu sai  makaranta, Aisha binsu kawai take da kallo inda suka zak'e, ita bataga abun murnaba, dama anguwa zasu tayi farknciki, ita sam batason mutane, idan ba tasan mutum ba bazakaji ta masa magana ba, saninma irin na sosai ɗinnan, danginsu gaba ɗaya bata saba dasuba sai Maman Ammi.
"Aunty mungama girkin".
taji Hajara tana faɗa.
Ta ce "Yaran Ammi 'yan albarka me kuka dafa mata".
gabanta suka kawo suka dire, k'amshi kuwa ya cika wajen,
Jalop ɗin Kuskus sukayi sai Chip na potatoes, sai drink kala biyu, da Sweet Runs.
"karfa kuce banyi aikin ba, wannan rawan kan naku kunji jiki, bakusan bak'uwar ba kun zak'e dayawa".
Sukayi dariya Sadiya ta ce "tunda kika ga Ammi tasan da zuwanta ta musammance".
Hajara ta ce "Ni damuwata musamu muyi mata rakiya idan tazo tafiya, kinga zamuga gari".
Duk suka tuntsire da dariya, Aisha ta ce "nikam bana fatan nasake zuwa ko ina ruwa ya tareni....
Hango Abbah sukayi ya nufo gunsu fuskarnan cike da fara'a, duk suka zuba ido suna tunanin meya kawoshi.
Hanun Aisha yazo ya rik'e, da dariyarshi yace "Mamana har yanzu ba'a huce ba ne? Ko ɗan sake rannan yanzu bakiyi".
Ta sunkuyar dakai tana dariya, "komai ya wuce ai, na yafe miki".
Su Hajara suka hau tsallen murna, "Abbah mungode, dama ɗazu tagama kuka wai yanzu baka kulata".
Tausayin ta ya kamashi ya kalle ta, idonta har sun ciko zata sake ɓare baki yace "kukan me kuma, nadaina fushin kada kisake tsallake dokata kinji".
ɗaga mishi kai tayi, ya ce "muje Amminki tanason ganinki".
yana rik'e da hanunta suka nufi wajen Ammi.
Ammi tana hakimce suka shiga, ya ce "ga uwata ki mata faɗa, amma bance a ɓata mata raiba".
Ammi tayi dariya tace "nima uwatace nafika sonta".
Duk sukayi dariya kafin yace "Zanshiga ciki, bazan koma office ba nafiso yaronnan yasameni akwai maganarda zamuyi".
ta ce "To Abbahn yarana".
Yace "Abun naki harda son kaine, yaranmu zakice".
"to yaranmu".
"ko kefa".
Sukayi dariya ya fita.
Aisha tana kishingeɗe ajikin Ammi, irin wannan wasan nasu yana bata mamaki don ita gani take sun girma amma sai suyi ta wasa.
"Aisha kinajina ko, nasanki da rashin hankali, wannan bak'uwar tanada matuk'ar muhimman ci a rayuwar ki, idan tazo kika share ta kamar yadda kika saba yi wa mutane zakiga yanda zanyi dake, ki sake jikin ki sosai kada tagane bakison mutane kinji ko".
Zunɓura baki tayi ta ce "Ammi wai ni me nakeyi na rashin hankali, kullum sai anmun faɗa".
dariya Ammi tayi ta ce "keɗinne ai, kije kiyi wanka yanzu ki shirya, kada kisa riga da zani kinsan baki iya ɗaurawa ba".
kuka tasakarwa Ammi harda bubbuga k'afa "ga su Sadiya amma ba'a k'irasu ba saini.... Buge bakin Ammi tayi tace "zaki tashine ko saina saɓa miki".
da gudu ta tashi tana kuka.
su Hajara suna jiyota sukasa dariya, Sadiya ta ce "Aunty ya kamata kibarmun girmannan tunda dama nafiki tsayi da k'iba".
Hajara tace "da hankali".
ganin zasu ɓata mata rai yasa ta wuce tabarsu a wajen.
Ruwan wankan ta haɗa me ɗan zafi tasaka turaren wanka aciki ta shiga, daɗin ruwanne ya kashe mata jiki tayi zamanta har tana lumshe ido, AYS ne ya faɗo mata arai tasake lumshe ido tana tunanin yaushe zata sake ganin sunanshi, da zata samu taji muryan shi da taji daɗi, da k'yar tayi wankan tafito ɗaure da towel, hand drya ta ɗauka ta tsane ruwan kanta dashi sannan tashafa mai da hoda ta ɗan murza lips stik abakinta, "bak'uwar tanada muhimmanci agareni kuma, me Ammi take nufine, to hala wata 'yar uwa take mata, ba wani kwalliyar da zanyi gayyan sa ciwon kai".
sumbatun ta tagama ta ciro wani less riga da siket purple, sai zagayen fari ajiki tasha aiki, ɗinkin yayi mata ɗas daidai jikin ta, ganin ba iya ɗaura ɗankwali tayi ba yasa ta ɗauko k'aramin farin gyale ta yafa me goldin ajiki, tana cikin fesa turare taji hayaniyan su Hajara, "wa innan mahaukatan yanzu haka bak'uwar ne ta iso suke wannan ihun".
ɗan tsaki taja tayi waje itama.






Kusan shiga babban falon nasu taji taci karo da mutum, saura kaɗan ta faɗi ta ɗago cike da masifa tayi tsammanin k'annen tane, mutumin data ganine yasata sandarewa awajen, UMAR FARUQ ne, yana sanye da shaddarsa rigar ɗinkin half, tayi bala'in yimasa kyau, murmushi kawai yake zubawa dimples ɗinnan nasa suna lotsawa, hanu yasa ya rufe fuskan shi, "wannan kallon zakisa nazama mummuna".
Lek'ek'e ta farayi ganin babu kowa ta ce "me ya shigo dakai gidanmu, karufamun asiri ka tafi".
Nok'e kafaɗa yayi ya ce "nima gidanmu ne, babu ruwanki dani".
Kaɗa baki tayi
zatabar wajen yajawo mayafin ta, "kinyi kyau sosai, kamar nasace ki na gudu haka nakeji".
Murmusawa tayi ta ce "kaima kayi kyau".
Murmushi yayi yace "nagode".
D'akin Ammi ta nufa anan take jiwo hayaniya, Farar matace kyakkyawa kana ganinta kaga Faruq, tsayuwa tayi turus, ko ba'a faɗaba tasan mahaifiyar Faruk ne, ganin Ammi tanata watsa mata harara ne yasa ta k'arasa kusa da matar ta gaisheta, da fara'ar ta ta amsa, Ammi tace "yarana sun haɗu duka, saiki zaɓi naki aciki muga ko zaki gane ɗiyar taki".
Momy tayi dariya ta ce "tun shigowar ta nagane ta, wannan tayi lukuta".
ta nuna Hajara ta nuna Sadiya ta ce "wannan tayi tsayi da yawa, amma ɗiyata 'yar daidai ce, daban take".
Ta jawo Aysha ta ce "ko ba itace wannan ba".
gaba ɗaya sukayi dariya, Ammi tace "kin canka".
Sadiya ne ta zunɓura baki tana mita wai su bata sonsu, Momy tayi dariya ta ce "kunga wannan ɗauketa zanyi takoma wajena, dole na zaɓe ta".
Sai kuma suka fara mata gwalo.
Abincin da sukayi suka kawo mata, babu wani fulako tanaci tana santi, itadai Aisha duk ta takura kanta, matar nan ta jani da yawa.
"Tareda ɗana nake, ban muku bayani ba, Aysha taimaka kije kada yaga na daɗe".
Ammi ta ce "ah ah kitafi mishi da abinci".







Su Sadiya ma duk mik'ewa sukayi suka bi bayan Aisha, suna daf da shiga falon Aisha ta ce "A'ina Ammi ta samo mutanennan, ɗan natafa wanda yaɗauko ni a motane ranarda ruwa yamun duka".
kama baki sukayi Sadiya tace "dama yasan gidannan kenan".
Hajara ta ce "koma yane idan sun tafi Ammi zata mana bayani".
Da sallama suka shiga, ɗan ɗagowa yayi ya amsa amma k'asa2, duk hankalin shi yana kan Aisha yabita da kallo ko kyafta ido bayayi, yayi missing ɗin fuskarta sosai,  su Hajara kuwa hankalin su yana kan shi ganin yanda yabi Auntyn su da kallo kamar zai haɗiye ta, ita ɗinma duk kunya ta kamata aranta tace "me mutuminnan yake nufi ne".






Gaishe shi sukayi suka bar wajen, lokaci kaɗan Hajara ta dawo mishi da kayan abinci, Aysha ta mik'e zata bita yayi saurin taka k'afarta, 'yar k'ara ta saki yayi yayi saurin ɗagawa, lokacin har Hajara ta fita, ya tsuguna wai yana hura mata k'afar, dariya ya bata don ita ba zafin da taji rakine kawai, amma ta k'unshe dariyar, zama yayi a kujerar da yake fuskan tarta, yak'ira sunanta a hankali, ɗagowa tayi ta zuba masa ido, ya ce "kinga mahaifiya ta ko"?
Ta ɗaga masa kai kawai, ya ce "tana sonki sosai, don ke tazo gidannan".
Zaro ido tayi, yace "eh, tun ranar da ruwa ya miki duka kika tafi da imani na, nasan idan narantse miki ko baccin kirki banayi ba tare da tunanin ki ba bazanyi kaffara ba, ban taɓa so ba, kada ki watsamun k'asa a ido, nayiwa Mahaifin ki magana kuma ya bami ke".
Binshi kawai takeyi da kallo har yagama, jin maganan shi na k'arshe ne ya jefata a damuwa, tunanin ta ɗaya idan tayi aure shikenan bazataga Ays ba, fashewa tayi da kuka da iya k'arfin ta, hankalin shi in yayi dubu ya tashi, "don Allah kiyi shiru baki sona ko?


Bazan miki dole ba kiyi tunani, amma wallahi idan baki amince ba akwai matsala, ki tausayamun Aisha".
har k'asa ya suguna mata, sai a lokacin ta rage kukan, yace "Baki sona ko".
Ta girgiza kanta, "to meyasa kike kuka".
Nanma girgiza kanta tayi, ya kaɗa kai yace "bani wayarki nasa miki numbata, idan kinyi tunani duk hukuncin da kika yanke ki faɗamun".
A hankali ta ce "banida waya".
Shiru yayi can ya ciro ɗayar wayarshi ya mik'a mata "














Ki rik'e wannan zan k'iraki nanda kwana biyu".
har tasa hanu zata karɓa ta tuna Abbahn ta, ta ce "kabarshi kawai, Abbah na yahanani rik'e waya".
Daɗi yaji aranshi wannan ma wani tsaro ne, ya ce "ki karɓa, zanyi wa Abbah bayani, bazai hanaki ba".
Hanu biyu tasa hanu ta karɓa, da zolaya ta ce "bafa aro ba, kyauta".
Yayi dariya ya ce "zan iya baki kyautar kaina balle waya".
Murmushi tayi tace "nagode".
Zuciyarta fal farinciki tayi ɗakinsu Hajara da gudu, tun kafin su san me takeyiwa dariya suka hau tayata ('yan abi yarima asha kiɗa).
wayar ta mik'a musu, me tsadan gaskene sosai, Hajara ne ta ɓata rai ta ce "kinsan Abbah ya hana ko".
"to 'yar bak'inciki sai kitsaya kiji bayani, nasan wannan kallon da biyu, nafi matsuwa naji me yakawo su gidannan".
Sadiya ta faɗa tana gyara zama, dungurin ta Aysha tayi ta ce "ke tsaya nahau Fcbk sai nabaku labari".
Sake baki sukayi suna kallon ta suka kasa magana, tsawon lokaci Hajara ta ce "Aunty anya ba asiri aka miki acikin fcbk ɗinnan ba kuwa, daga baki waya...
Sadiya ta katseta, "tayani wannan tunanin, kuma babu abunda takeyi aciki dazai amfaneta sai kallon sunan wannan ɗan Aljanin".
Itadai batace musu komai ba tahaura abunta, sak'onnin nasa ta duba duk sallama ne yafi goma, ɓata rai tayi aranta ta ce "baimayi kewata ba yaronnan".
amsa mai sallamar tayi kafin ta sauk'a.
tajuya duban ta ga k'annenta da suka zuba mata ido, ta ce "menene haka kamar zaku cinyeni, to ai banma hauba, bari nabaku labari, Faruq wai sona yakeyi".
nan tayi musu bayanin inda sukayi, hhh tsalle suka fara suna murna sunga kyakkyawan saurayi, "Aunty kada kitsaya jan aji don Allah yahaɗu, kuma kinga Mahaifiyar shi tana sonki, me yarage miki, zakiyi ta haifan nyawawan yara".
murmushi tayi ta ce "shikenan tunda kuna so nima inaso na amince, amma sai ya k'ira nanda kwana biyu zan faɗa mishi, rungumeta sukayi su duka suna murna.

Comments

Popular posts from this blog

Australian Visa Application information: Visa Types & Requirements

[Sunnah] What Muslim Should Observe On The Day Of Eid

Canada Immigration: How To Apply For Canada Permanent Resident Visa