NI AYS NAKE SO Part 6
💅💅💅
💋 *NI AYS NAKESO*💋
💅💅💅
.
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
_We dont just entertain and educate we also touch the herts ƙf readers_
.
.
_WRITEN BY Princess Eshat Aysm_
.
.
In Dedication to *ABDULLAHI YAHYA SA'AD ZARIYA*
A.Y.S
Page 6
.
.
Kwance yake a ɗakin Umman sa sai juyi yake yi, shi kanshi baisan meke damunshi ba, amma yana tunanin baya wuce nasaba da tunanin yarinyar da baisan yaya take ba, hasalima baisan tsohuwace ko yarinyaba, bak'a ko fara bai sani ba amma har cikin ranshi yakejin kewar hirar da sukeyi da bai wuce sati da haɗuwarsu ba, k'anwarsa ce Raliya ta shigo ɗauke da flask na abinci, ta dungura a gabanshi sannan ta nemi waje ta zauna, "Yaya me yake damunka ko abinci baka fiye ciba".
Zuba mata ido yayi kafin yace "lafiyata k'alau, ko jiya danaje skul kasa kome nayi, ina tunanin watace ta tsayamun arai".
Ajiyan zuciya Raliya tayi "kasan idan Umma tasan baka cire Aisha arankaba har yanzu bazataji daɗi ba, tunda tayi aure kamanta da ita".
Murmushi yayi, dagani banajin daɗi bane "ke waye yafaɗa miki ban manta da itaba".
"kaji Yaya, jiyafa inaji kana bacci kana cewa Aisha kizo mutafi".
Tashi yayi ya zauna ya ce "watace wannan, sunan ta Aisha itama".
Da murmushi a fuskarta tace "a wani anguwa take"?
Shiru yayi naɗan lokaci kafin yace "Bansani ba, sunanta kawai nasani sai kalamanta duk da bana soyayya bane ta tsayamun a rai, a fcbk muka haɗu da ita".
Dariya ta fara mishi harda rik'e ciki, "kace da aljana kuka haɗu, aikuwa dole a fara maka addua, su dama haka suke, su jefa tunani a zuciyar mutum kawai don kada yaci gaba a rayuwa....
Hanu yakai zai daketa tayi waje da gudu, dai2 lokacin Umman su tazo shigowa, "menene haka, kin taɓoshi ko".
"Umma aljana ya haɗu da ita, don nafaɗi gaskiya zai bugeni".
"kedai bakijin magana, kinsan shi idan ranshi na ɓaci baya wasa amma saida kika k'ureshi, tafi ni kibani waje".
Barin wajen tayi tana kunkuni.
yana jinsu ya jawo wayarshi ya hau fcbk, waro ido yayi ganin msg ɗin ta, da sauri ya buɗe, amsa sallamar kawai tayi, cikin farinciki ya aika mata da sak'o.
_Ashe tafiya bashi yake nufin mutum ya mutuba, nayi gangan cin sawa a raina bazaki dawo gareni ba, kullum tunani nakeyi yaushe zan sake ganin rubutunki, kin tafi da tunanina, kin jefa zuciyata cikin k'unci, bana iya banbance dare da rana Aisha, Allah yasa ba laifi namiki ba, idanma laifine kada ki sake tafiya kibarni_ ".
Tana kwance tana jinsu Hajara sunata murna zata auri Faruq, tunani takeyi Faruq ya haɗu babu laifi, zata aureshi ko don k'annen ta, k'arar shigowar sak'o tayi, a tunanin ta Faruq ne har tafara mitan daga bata waya zai fara damunta, ganin daga fcbk ne yasa tayi hanzarin buɗewa, abunda taganine yayi mungun kiɗimata, "kenan shima yanajin abunda nakeji, anyama gaskiyane".
"uhmmm".
Shine abunda ta tura mishi, a take ya maido mata amsa, "Baki yadda ba ko, ki faɗamun garin da kike sai nazo".
Murmushi tayi tace "Sadiya matsu kiji, kinga wai yana so yazo".
Hajara ta ce "Aunty don Allah kishare Ays ɗinnan, yazo ina, kema kinsan ba barinki za'ayi ki futaba ki ɗauko mutum tun daga Zariya, Abbah yaji wallahi sai yayi kusan kashe ki".
Sadiya ta ce "kice mishi kawai basai yazo ba".
Zuba musu ido tayi na tsawon lokaci sannan ta rubuta mishi
_me zakayi a garinmu, daga yanzu muna tare anan basai kazo ba_
💋 _shikenan, amma don Allah kada kisake nisa dani, ki turo mun numbanki, da photon ki_.
Wani malalacin dariya ta saki, ni kuwa me zai kaini tura photo na..
💋 _zamuyi rayuwa a haka, batare daka ganni ba, nima bazan ganka ba, bazan ɓoye makaba, na kamu da sonka tun kafin mufara magana, idan har kayi kewata da gaske to na tabbata ka kamu da sona, wannan wani haɗine na Allah, daga yau munzama abu guda ko bamuga juna ba_
Gani yake kaman zata sake barin shi shiyasa ya amince da wuri.
.
.
Momyn Faruq bata bar gidan ba saida sukayi magana da Abbah, ta nuna masa tana son ayi bikin da wuri zata k'arasa karatun ta acan, sun tsaida magana akan nanda wata 2 za'ayi biki.
Lokacin da Aisha taji maganar sam bata damu ba, dama damuwarta karatu tu ance zatayi acan, su Hajara murna kamar me.
A daren ranar kuwa Ays ya canza mata gaba ɗaya, wani soyayya yake bayyanar mata yana mata, yaron ya tafi da imanin ta, ko kaɗan takai minti ɗaya bata bashi amsa ba zaiji kamar ya kurma ihu, yayi ta mata mita kenan, k'arshe numban ta ya karɓa ya k'irata, lokacin da yaji muryanta zaucewa ne kawai beyi ba, muryace me daɗin ɗanɗano kamar ana busa sarewa, dai wajen asuba ya barta ta kwanta, nanma bata iya baccin ba tunanin aurenshi kawai takeyi, hankalin ta gaba ɗaya ya koma kanshi, tana zaune aka k'ira Sallah, taje tayi Sallah ta ɗan taɓa karatu, ta haura fcbk, kalaman shi tafara cin karo dashi wanda ya turo mata da asuba.
" _ESHAA fatan kinyi mafarkina_"
Murmushi tayi aranta tace "inama nasamu nayi bacci".
Shirin sauk'a takeyi bata bashi amsaba ya turo,
" _Naga kin karanta sak'ona baki bani amsa ba, da ace nasamu bacci nasan dole zanyi mafarkin ki, muryanki kaɗai idan natuna daɗin sa nakanji bazan iya tashi ba, ina sonki da yawa Eshaa_"
Lumshe ido tayi daɗi yana ratsata,
ta tura mai " _nima banyi bacci ba_"
Soyayyar su suka sha sosai, ba wanda ya damu da rashin fitowar ta don yanzu aure zatayi a faɗar su, sai wajen 11 ta ajiye wayar, nanma dak'yar ya barta, wani irin so yake mata dashi kanshi baisan lokacin da yashiga ba.
A falo ta tarar dasu Ammi, Hajara 'yar lukuta anata zuba kamar aku, kuma wai duk taɗin faruq takeyi, zama Aisha tayi a gefen Ammi tagaishe ta, da fara'a ta farka taje "'yar gata an tashi"?
Langaɓe kai tayi ta ce "Ammi yunwa".
Hajara ta kama baki tace "Aunty tun jiya kike sha mana k'amshi tun ba'ayi auren ba".
Gaban Aisha ne yayi mummunar faɗuwa don ita daga jiya zuwa yau babu abunda ta tsani ji kamar Aurennan, har wani zufa ta farayi, Ammi tana lura da ita ta ce "Aisha kina lafiya kuwa".
Narai tayi da ido zata fara kuka, Sadiya ta ce "Ammi lokacin da kika zo haihuwar Aunty amma kinyi ta kuka ne".
duka Ammi takai mata ta ce "kinci gidanku".
Aisha kam k'ara muryan kukan tayi.
Ammi tayi salati "yanzu a haka za'ayi auren abu kaɗan ki ɓare baki, me aka miki".
"Ammi don Allah kada amun aure wallahi *NI AYS NAKESO*
Ammi ta kaɗa baki ta kalle ta shek'ek'e "waye kuma haka, a ina yake, kanki ɗaya kuwa".
Hajara tayi tsaki "Ammi kada ma ki saurare ta, wani aljani ta haɗu dashi".
Ammi ta waro ido kamar zasu faɗo, "Aljani kuma?"
Sadiya duk haushin Hajara ya cikata, ita duk abunda Auntyn ta takeso shi take so, bata so taga ana mata faɗa.
Ammi kam ganin Aisha batada niyyar yin shiru ta nufi ɗaki taɗauko wayar ta ta k'ira Abban su, babu ɓata lokaci yadawo yasan k'irannan bana lafiya ba.
Kukan Aisha ne ya amsa masa sallama, da sauri ya k'arasa ciki ya kamota "mamana me aka miki".
muryan Ammi yaji tana cewa "saifa kayi da gaske, kukan banza takeyi wai aurennan bata so".
Dubanta Abbah yayi a hankali ya ce "Mamana bakison Faruq ɗin shine kike kuka, bazan miki auren dole ba, share hawayen ki".
Tsagaitawa tayi da kukan tanajan numfashi,
"Aurenne baki so ko kuma Faruq ɗinne baki so"?
baki ta ɗan turo ta ce "Inason Auren amma *NI AYS NAKESO*
Wani kallo ya jefeta dashi ya ce "wanene shi, a sanina bana barinku da kowa, kuma bakiyi girman da zaki iya bijiremun ba, a ina kika samoshi"?
Su Hajara anata tsilli tsilli da ido, Ammi ta ce "Nidai naji rashin kunya, wai auren tana so..
Abbah ne ya ɗaga mata hanu, ya ce "Mamana inajinki, waye AYS A ina kika samo shi"?
Nanma shiru tayi, ganin ranshi yafara ɓaci ta ce "a waya muka haɗu".
Wani ɓacin raine yaji ya bugi zuciyar shi, cikin kausassan murya ya ce "kinada hankali kike faɗamun wannan bak'in maganar, to wallahi sai namiki abunda bakiyi tsammani ba, matuk'ar kika sake ambatan wannan sunan saina saɓa miki, inbanda shashanci bakisan waye shi ba kice shi kike so".
Yana faɗin haka yafice yana cewa "kada asake k'iran shi akan wannan shashancin".
Aikuwa yana fita tafara birgima tana cewa NI AYS NAKESO, bayanda Ammi batayi ba amma tak'i bari, k'arshe k'annan nata zama sukayi suka fara tayata kukan, ran Ammi idan yayi dubu ya ɓaci, wayan wuta ta nemo tafara zuba mata kamar Allah ne ya aiko ta, saida taga ta fara kuka da k'yar ta kyaleta, da sauri su Sadiya suka ja ta zuwa ɗaki, idonnan ya kunbura suntum, Hajara ta ce "Aunty bakici abinciba".
Kaɗa mata kai tayi alamar ta k'oshi, Sadiya kuma ta haɗa mata ruwa me zafi taje tayi wanka, baki suka shiga bata da kalan rarrashi amma tace itafa sam Ays take so.
bayan Abbah yadawo Ammi take faɗa mishi Aisha fa ko abinci bataci ba, saida na mata duka muka dai2 ta, polk ɗin hannun shi ya ajiye yace "ni kaina na kasa samun nutsuwa, hauka nakeyi zan aura mata wani wanda bansanshi ba, ga ɗan gida yaron kirki".
Ammi tace "nifa inaga jinnu ne suka shafe ta, kamata yayi mu ɗau mataki tun yanzu, kanajin sunanma kaji sunan Aljanu".
tsawon lokaci kafin ya ce "ki ɗebo ruwa yanzu a cup ki tofa mata _IFTALISSIHIR_
tasha ta shafe jikin ta, inaga wani tahaɗu dashi yayi mata asiri.
.
Eshataysm@gmail.com
Comments
Post a Comment