NI AYS NAKE SO Part 7

💅💅💅
      💋 *NI AYS NAKESO*💋
                 💅💅💅

.

*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
_We dont just entertain and educate we also touch the herts ƙf readers_

.

.



_WRITEN BY Princess Eshat Aysm_

.

.

In Dedication to *ABDULLAHI YAHYA SA'AD ZARIYA*
A.Y.S



Page 7

.




.

.



www.Eshataysm.tk




.


.

.




*SHIFA RAYUWA SAI A HANKALI, DA ACE ZAKAYI ABUNDA ZAKAYI A RAYUWAR KA BAZAKA SAKA IDO KAGA ME WANI YAKEYIBA ZAKAJI DAD'I WALLAHI, SANNAN IDAN KAYIWA MUTUM GYARA SAU BIYU KAGA BE GYARA BA SAIKA ZUBA MASA IDO, AKAN WAMI BANZAN ABU KAZAUNA KANA D'EBAWA KANKA ZUNUBI, IDANFA MUTUM YAYI NAGARI YA SANI KUMA BA'A SHIGA TSAKANIN BAWA DA UBANGIJIN SA BALLE KACE KASAN WANNAN YA AIKATA KAZA WATA ZAI SHIGA, INDAI YARINYA TANA HAWA SOCIAL MEDIA TOFA TABBAS DA HATSARI BAWAI SAITA KARANTA NOVELS ZATA LALACE BA, AKWAI MASU LABARAN BATSA MASU ZAMAN KANSU KUMA INDAI ZAKI HAU MEDIA ZAKICI KARO DASU, DUK WANNAN BAISA YARINYA TA LALACE BA SAI BOOK D'IN SURBAJO? BAWAI ABUNDA TAKEYI A BOOK D'INTA YANAMUN DAD'I BANE AMMA HANYAR DA AKEBI YANA B'ATAN RAI, TUNDA KUNSAN TASAN ABUNDA TAKE MEZAISA A ZAUNA ANA CECE KUCE MARA AMFANI, SHIYASA RAYUWATA TAKE BURGENI BAN TAB'A SHIGA RAYUWAR WANI A MEDIA BA, KOWA YAYI NAGARI DAN KANSHI, ALLAH YAKAREMU DAGA RUBUTA DUKKAN ABUNDA ZAI ZAMO GYARANE BA B'ATAWA BA*


.

.


_AKWAI MASU RADDI AKAN SADNAF, BANTAB'A FASHIN KARANTA BOOK D'INTA BA KUMA BANGA WANI ABUNDA TAKE SAKAWA BA, TUNDA TAYI LALATA BATA SAKEBA, DUK WANDA YASAKE ZAGINTA KONI BAZAN YAFE MASABA_.





.
.
.







Haka kuwa Ammi tayi, tofa mata takai mata dakanta, sai dataga ta shanye ta shafa sauran a jiki tabar ɗakin, 20 mscall tagani a wayar ta, ko bata dubaba tasan Ays ne, har lokacin zuciyar ta na mata zafi ta k'irashi, muryanshi na ratsa dodon kunnen ta taji sam bazata iya rabuwa dashiba, bata lura dame yake faɗi ba ta fashe mishi da kuka, har cikin zuciyar shi yakejin kukan, ba k'aramin ruɗewa yayi ba, ya runtse ido yanajin yanda sautin kukan ke fitowa, a hankali ya iya furta "Aisha zakisa numfashina ya ɗauke idan kina kuka, kiyi shiru ki faɗamun me yake faruwa, tun ɗazu nakejin gabana yana faɗuwa".
Rage sautin kukan tayi ta ce "Aure zanyi...
Wani k'ara yasaki ya toshe kunnuwan shi, yanajin yanda kalmar ke masa yawo a kanshi, yana jin yanda zufa ya wanke duk ilahirin jikin shi, lokaci guda hankalin shi yafara barin jikin shi, dak'yar ya furta kalmar "kada kimun haka Aisha, kada ki auri wani ba niba, zanbaki dukkan rayuwa ta da farinciki na, auren wani dai dai yake da rabani da rayuwa ta, na rok'eki kibani dama nazo gareki, nafi sonki fiye da kowa Aisha.... Kuka ne ya kufce masa yakasa k'arasa maganar, itama wani sabon kukan tafara "Ya zanyi, Abbah bazai auramun kai ba, nima mutuwa zanyi".
Ciro wayar yayi a kunnen shi ya runtse idon shi da k'arfi, so, k'auna da tsananin sha'awar ta yafara fizganshi, ji yake kamar ya buɗe ido yaji ta cikin jikin shi, rana ta farko kenan daya taɓa jin sha'awar kwanciya cikin jikin ta, yanajin kukan ta yana shiga tsak'iyar kanshi, nanda nan yafara birkicewa, har zai kashe wayar yaji tana cewa "kafaɗamun inda kake, zanzo gareka, bazan iya rayuwa da wani bayan kai ba".
numfashi ya sauk'e me k'arfi ya ce "dagaske kikeyi Aisha".
Daɗa jaddada mishi tayi akan lallai zata zo zariya , a ɗaura musu aure a can, lokaci guda farinciki ya mamayeshi, imaninsa ya tafi, abunda zai dawo dashi shine yaga Aisha a gabanshi, "AY zaka aure ni aduk inda ka ganni? Zaka zauna dani a duk yanda nake, idan kaganni bazaka gujeni ba".
Murmushi yayi ya ce "ko yaya kike ina sonki, kidaina kokonto akaina, Allah ne ya haɗamu, zan rayu dake duk rintsi".
jinjina kai tayi tareda murmushi har fararen hak'waran ta suka fito, "ki zauna cikin shiri, dazaran kinfito ki Shiga motar Kaduna, dakaina zan k'arasa dake Zariya, inayi mana fatan sa'a".
wani walk'iya tagani, kafin ta ankara taji anshak'o ta, muryan Abba har ɓari takeyi, "gara na kasheki na huta, ada nafisonki akan kowa amma yau ɗaya na tsani kaina dana haifeki, baki isa kisamun ciwon zuciya ba, tsawon shekarun 16 zuwa 17 a duniya ina ɗawainiya dake, rana ɗaya kifara tunanin bijiremun zaki gudu kibi wani k'ato, kashe ki zanyi kowa ya huta".
wani wawan shak'a ya mata da har tafara tunanin lahira take hangowa, duk abunda ake a kunnen Ays, hankalinshi yayi masifar tashi, ko wajen Umman sa bai nufa ba yaɗau abunda yake buk'ata ya tafi tasha ya shiga motar Bauchi.
dak'yar Ammi ta ɓanɓare Abbah taja Aisha suka bar ɗakin, cikin zafin rai yayi waje, bai zame ko inaba sai gidansu Faruq, Momy tayi matuk'ar mamaki da ganinshi, a hanzarce suka gaisa yace "maganar auren yarannan, inaso a ɗaura Aure yau, yanzu, idan akwai shirin dazakuyi kuyi bayan an ɗaura, amma tabbas inaso a ɗaura yanzu, ina shi Faruq ɗin"?
momy tayi murmushi me cike da mamaki tace "mukam a shirye muke, tunda kai kanema dakanka babu matsala, dama burinmu kenan, Faruq ya tafi garin Mahaifinshi ɗazu, Kuma sai bayan kwana biyu zai dawo".
bata jira amsaba ta ɗau waya ta k'ira wani wan Babanshi tareda wani ɗan uwanshi tace "suzo da hanzari aure ya tashi".
kafin minti biyar sun iso, bayani ta musu sannan suka nufi babban masallacin anguwar, anan za'a ɗaura aure Amma liman yabada shawarar a bari idan anyi sallar la'asar sai a ɗaura, gaba ɗaya suka amince.

mota tanata sharara gudu amma gani yake kamar ba gudu takeyi ba, kuka yakeyi sosai a motar kamar k'aramin yaro, meyasa yake cewa zai kasheta, idan ya rasa Aisha mutuwa zaiyi babu shakka, yanajin inda zuciyar shi tayi masa nauyi, ana k'iran Sallar la'asar suka isa garin Bauchi, anguwan nasu da ta taɓa masa kwatance ya nufa, ganin za'a shiga sallah a masallacin da yake kusa dashi yayi hanzarin yin alwala ya shiga yabisu Sallah, ana idarwa liman yace a ɗan dakata za'a ɗaura aure.

kowa ya koma yazauna, anan aka ɗaura auren Aisha Muhammad da Umar Faruq Muhammad Buzawa, akan sadaki dubu ɗari....
tunda aka ɗaura Ays yafara jin hankalin shi yana tashi, musamman dayaji sunan yayi matuk'ar girgiza shi, kanshi yayi masa nauyi dak'yar yake ganin mutane bibbiyu, da k'arfi yafara furta "kada kucemun Auren Aisha akayi, mutuwa zanyi, abunda yayita nanatawa kenan, bawanda ya kulashi har aka gama watsewa, liman ne yaje kusa dashi ya ce "yaro me kake faɗa".
kamo hanun limamin yayi ya ce "kamun rai kafaɗamun cewa ba auren Aisha na akayi ba".
sake baki liman yayi, can ya hango mahaifin Aisha, ya yafito shi da hanu, yana zuwa ya maimaita masa abunda Ays yake faɗa, mahaifin Aisha ya kalleshi dakyau yace "masu suna Aisha ai dayawa, dagajin suna saika birkice, 'yata sam batada saurayi ma".

Liman yayi murmushi yace "yaro kaji".
Abbah ya ce "ba yanzu naga ka sauk'a a mashin ba lokacin da zamu tada Sallah"?
Kaɗa masa kai yayi ya ce "daga zaria nake, yanzu isowa ta".
Dam! K'irjin Abbah ya buga ya zaro ido, wata Aishar kake nema? "
Bakin Ays har rawa yakeyi yace "wata yarinyar danake so ne, itama sunan mahaifinta Muhd, ta faɗamun Aure za'a mata shiyasa na kawo kaina gareta...."
Wani wawan kallo Abbah ya watsa mishi ya ce "kana nufin kaine AYS"?
da sauri yace "eh, nine".
Shak'oshi Abbah yayi yace "dama nemanka nakeyi, kayi hanzarin karya asirinda kayi wa 'yata.

Comments

Popular posts from this blog

Australian Visa Application information: Visa Types & Requirements

[Sunnah] What Muslim Should Observe On The Day Of Eid

Canada Immigration: How To Apply For Canada Permanent Resident Visa