NI AYS NAKE SO Part 8

💅💅💅
      💋 *NI AYS NAKESO*💋
                 💅💅💅

.

*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
_We dont just entertain and educate we also touch the herts ƙf readers_

.

.



_WRITEN BY Princess Eshat Aysm_

.

.

In Dedication to *ABDULLAHI YAHYA SA'AD ZARIYA*
A.Y.S



Page 8

.




.

.



www.Eshataysm.tk







.




.






.





Liman da sauri ya janye shi ya ce "Haba muhd, da girmanka kake haka".
Abba yana huci yafaɗawa liman halin da ake ciki, liman yasha mamaki yace "meyasa kayi mata auren da bataso, yaran yanzu ba'a shan bakinsu, amma tunda k'addara tariga fata".
Ya dubi Ays daya fara zubda hawaye ya ce "kayi hak'uri ni na rok'eka da kaina, haka Allah ya k'addaro muku, zanbaka masauk'i a gidana ka kwana zuwa gobe ka koma".
Abbah yace "idan har bai karya asirinnan ba babu inda zaije".
Abun duniya duk ya ishi Ays, hajijiya ya fara ɗaukanshi, kasa gane fari da bak'i yayi, bayama jin me suke faɗa, basu ankara ba sai faɗuwar mutum sukaji a k'asa, da sauri sukayi kanshi, liman duk yagama ruɗewa, addua yafara tofa mishi Abbah kuma ya nemo ruwa aka yayyafa mishi, Kukan Aisha dayaji ɗazune yafara yimasa yawo a kunne, shi kanshi Abbah saida ya tausaya mishi, besan abun yayi tsanani haka ba, dak'yar suka samu yaɗan nutsu suka fara bashi hak'uri, nasiha sosai Liman yayi mishi akan komai na duniya arubuce yake, tunda tayi aure ya manta da ita, rok'onsu yayi akan subarshi koda ganin Aisha yayi daga nesa amma Abbah yace sam bazai yiyu ba, bata ganshibama ta ruɗe balle ta ganshi, yayi hak'uri kawai, bai karɓi tayin liman na yakwana a gidansa ba ya musu sallama ya koma zaria cikin k'unan rai tare da bak'in ɓacin rai.

.

.

Ammi tana janta takaita ɗakinta, share mata hawayen tayi ta ce "kiyi shiru, ki sake ranki kada kisa yaɗau mummunan mafarki, idan har ina raye zan rok'a miki Allah ya baki Ays idan alkairi ne agareki, idan kuma kikaci gaba da abunda kike kinsan Abban naku, zan barki dashi".
Cikin murya me gungunin kuka ta ce "nagode Ammi".
tun suna jiran dawowarshi suga hukuncin da zai yanke har suka fidda tsammanin dawowarshi, koda dare tayi k'in komawa ɗakinta tayi, ɗakinsu Hajara taje tayi kwanciyar ta, kallo ɗaya ta musu tasan sunci kuka sosai, kuma bazai wuce akan halinda take ciki bane, Hajarane ta matso kusa da ita ta ce "Aunty anyi ta k'iranki a waya".
murmushi tayi ta ce "na baki wayar".
Waro ido Hajara tayi tace "kima daina wannan wasan, har abada bazanyi abunda iyayena basu so ba".
shiru Aisha tayi tana nazarin wannan maganar, kenan k'anwarta ma kenan,




Bata sake magana ba har bacci ya ɗaukesu, da sanɗa ta zaro wayar a jikin Hajara, Numban shi ta fara nema a kashe, tak'ira yafi sau 30 amma a kashe, kuka ta fara k'asa2, fcbk tahau taga sak'on shi, "kinshiga rayuwa ta kuma kinmun nisa, nagode da soyayyar da kike mun, bazan sake jinki ba, nima bazaki jini ba, ko mutuwa nayi zanyi farinciki ta sanadin k'aunarki na rasa rayuwata, har abada kece kaɗai, ki kula da aurenki sosai Aisha".
Jifa tayi da wayan tafara kuka da iya k'arfin ta, a tare su Sadiya suka tashi a razane, tambayar duniyar nan sukayi amma sai tsananta kukan takeyi, k'arshe ɗakin Ammi suka nufa a ruɗe, gani batanan ne suka nufi wajen Abbah sun san tana can, suna zaune yana faɗa mata anɗaura Auren Aisha sukaji k'iran da Hajara take ta k'wala wa Ammi, suma a ruɗe suka fito, ganin kukanda Aisha takeyi abun yabashi tausayi, tsugunawa yayi a gabanta ya ce "Mamana kukan me kikeyi".
"Abbah NI AYS NAKESO".
Murmushi yayi yace "to menene abun kuka, yi shiru zan baki duk abunda kike so".
Tsananin mamaki ne k'arara akan fuskanta, ya gyaɗa mata kai yace "Badai Ays ba, yazo garinnan ɗazu, har mun haɗu dashi, idan har yasake miki magana to ni mahaifinki zan baki Ays".
zuba mishi ido tayi sam takasa gane inda maganar shi ta dosa, tuna kalmarshi na k'arshe tayi "ki kula da Aurenki Aisha".
aranta tafara nazarin anya Abbah yanada gaskiya kuwa, to tayaya za'ace mata Ays yazo garinnan, shima me yake nufi da wani aure kuma..
"ki tashi kije ki kwanta, kada ki hanasu bacci kuma, inbanda masifa me yakaiki ɗakinsu keda kikace Allah ya kiyaye ki kwana cikin su".
Ammi ne taji tana wannan maganar, jiki a saɓule ta mik'e suka mara mata baya.

Suna tafiya Ammi ta ɓata rai tace "meyasa zaka yanke hukuncinnan, Aisha fa k'aramace bazam daina faɗa maka ba, kasa wata biyu be makaba zaka ɗaura aure bada saninta ba, nima dana haife ta baka faɗamunba, wani irin gajiya kayi da ita..."
ta faɗa kamar zatayi kuka, ya matso kusa da ita ya ce "kiyi hak'uri Ammi, wutar da Aisha take shirin rurawa yafi k'arfin tunanin ki, ina faɗa miki yaronnan sai gashi a masallaci zamu fara sallah, tunda ya fahimci Auren Aisha aka ɗaura ya suma mana a wajen, idan yazo da k'aran kwana kinga munshiga uku, inaji a jikina auren da namata alkairi ne a rayuwar ta, kimun k'ok'ari ɗaya ki shawo kanta ta amince da Faruq, mungama magana da Momin shi zuwa jibi ayi biki akaita gidan ta".
tunda yafara magana take kallon bakinshi, ita kanta saida taji ta samu nutsuwa, auren shi yafi dacewa da Aisha, mamakin ta ɗaya jin wai Ays yazo harda suma, ta tausaya mishi sosai.
ganin tayi shiru ya ce "Baki huce ba"?
murmushi tayi tace "Allah yasanya alkairi".
shima murmushin yayi ya ce "ki rubuta duk abunda zaku buk'ata, kisan yanda zakiyi ki tambaye ta me take so".


Momy kam ana ɗaura Aure ta fara faɗawa 'yan uwa da abokan arziki, kafin kace me gida yacika da jama'a, Faruq ana Niger ba'asan wainar da ake toyawa ba, duk wanda ta faɗa mishi sai tace kada a faɗa mishi a bari tanaso ta bashi mamaki, gani kawai yayi dangin mahaifansa suna shiri suna cewa rakiya zasu mishi, abokan wasa kuma sai tsokanan shi sukeyi, sunacewa tunda yak'e aure zasuje su zauna mishi, baisha mamaki ba saida yaje gidan k'anin Dadyn shi, kayane nik'i2 a tare a wajen wai gobe zasu mishi rakiya, UNAISA ce ta fito daga ɗaki da gudu jin muryan shi ta ɗale jikin shi tana murna gobe zasu Nigeria, dabara yayi ya janyeta a jikin shi ya ce "kefa bakida hankali, kin kasa gane kin girma sam, shekarunki 20 amma babu abunda ya canza a rayuwarki.
ɗan tsaki taja ta ce "kaifa yayanane, menene don nahau jikin ka".






Baban ta ne ya shigo, yana ganin Fatuq ya washe baki, Allah ya ɗaura musu son Faruq ganin shi suke kamar mahaifinshi, sun so ya zauna a wajensu amma Momy tak'i, Muhammad Buzawa shine sunanda yake amfani dashi, asalin bafulatanin Niger ne, yayunsa biyu mace dana miji sai k'aninshi wanda Faruq yaci sunan shi, shiyasa yake masifar sonshi, yaso haɗashi aure da Unaisa amma jin labarin auren yasa yaja bakinsa yayi gum, a gidan yazauna har dare kafin ya koma gidan kakannin shi, asuban fari suka ɗau hanyar Nigeria, yawansu ba'a lissafi, shi kam mamaki ya cika shi sosai.







.
.
.
.

Washe gari kuwa Aisha warai ta tashi, babu kuka babu ɗaure fuska, saboda kwana tayi tana sallah tana rok'on Allah ya sanya mata sanyi a ranta, tun asuba kuwa tayi ta karatun Qur'ani taji sanyi a ranta sosai, kowa yasha mamakin ganin ta harda dariya, tare sukayi aikin gidan kamar da, Ammi taji daɗi sosai, suna gamawa tace suje suyi wanka zasu rakata kasuwa, murna da tsalle suka shigayi, dukkanin su sunyi shigar dogon riga sunyi kyau, kallo ɗaya zakayi wa Aisha kaga ramar datayi, a kasuwar ma babu wani tambayar datayi ganin irin kayan da Ammi take kwasa, kayan kitchn harda abubuwan da batasan amfanin suba, su Hajara kam kome sukaga ya musu kyau ɗauka sukeyi suce Aunty wannan yayi, da murmshi take rakasu, sun shafe lokaci me tsawo kafin suka gama.

Sashin Faruq Momy tasa aka ɗan gyara don dama a gyare yake, ba yanda batayi da Abbah kada yasai kome ba amma ya ce "bazai iya auren Aisha bai mata kayan ɗaki ba, kayan sashin kaf aka fitar aka zuba na Abbah, ya fitar da ita kunya sosai, babu wanda zai lek'a beyi santi ba, ita kanta Momy saida wajen yayi masifar burgeta, kayan da Ammi ta siyo ma ko gitan bata shiga dashi Abbah ya tura aka kwashe akayi gidansu Faruq dashi, waje kam yayi tubarkalla amma saura haɗuwar amarya da wajen.

Aisha dai zubawa sarautar Allah ido tayi, k'asan zuciyar ta kewar Ays ne fal da tunanin wani hali yake ciki, lokaci2 Ammi tana kallon ta taga wani yanayi take ciki.
Ayar da Ammi ta siyo ta gyarashi ta wanke, yana bushewa ta ɗauko turmin k'arfen ta ta dakashi, sannan ta tankaɗe, sannan ta ɗauko dabinon data cire k'wallayen ta haɗa da mazark'waila ta dakasu sosai, haɗawa tayi da garin ayar nan ta cakuɗa su waje ɗaya.
duk abunda takeyi su Aisha suna kallonta kowa yana jira tagama suyi tambaya, gani ta saka a roba ta rufe Sadiya ta ce "Ammi wannan kuma na menene".
Ammi tace "kunga ai ba wani haɗi nayi me yawa ba, ba'aso amarya wacce bata taɓa aure ayita ɗura mata abubuwa ba, ko zallan wannan haɗin tasha zata wadatar".
Hajara ta ce "Ammi na waye wannan ɗin".
Babu ruwanki Ammi ta faɗa lokacin da ta mik'e, katon tukunyar data ɗaura taje dubawa.
haɗin zumar matane a wajen, ganin yayi ta sauk'e ta taceshi sannan ta mayar tasaka zuma da aciki ta rufe, saida ta gama kome ta k'ira Aisha ɗaki, tunda tafara mata nasiha Aisha tagane inda abun ya dosa, wasu siraran hawayene ya sauk'o mata,
Ammi taci gaba da cewa


" Ki kasance Macen da ta yarda ita mace ce, don haka ta tanadi duk abin da ake bukata a wajan mace.
Ki zamto Mace mai hikma da azanci, wacce ta karanci mijinta da kyau, kuma take kaucewa duk abin da
zai haddasa matsala a tsakaninsu.
Ki zamto Mace mai taushin hali da nutsuwa, wacce miji yake jin nutsuwa, idan yana tare da ita.
Ki zamto Mace da kudi bai dame ta ba, ita mijinta kawai take so, ko da akwai ko babu.
Kasance  Mace mai hakuri da juriya, babu gunaguni, babu mita, da kai kara ga iyaye ko kawaye.
Ki dauki kanki likita., mijinki a mara lafiya, domin ya sami kulawa, ta musamman da.
riritawa.
Ki zamto Mace mai saurin daukar ishara, tana gane shiru da magana, da motsi da yanayin shigowa da
fita, samu da rashi da kuma yanayin da ake ciki a duniya ko a gari.
Ki zamto  Mace mai sakakkiyar zuciya, mara kulli da ramuwa.
Ki zamto mai karawa miji kuzari da karfin hali, a kan kyawawan manufofinsa.
Ki kasance mace mai rikon amanar aure, da soyayya ga mijinta kawai.

sannan Allah yana ganinki duk ranarda kikayi gigin tunanin wani a gidan mijinki.


kada kibari Allah yayi fushi dake Aisha, ki rayu da tarbiyan dana baki kada ki bani kunya.

dukkaninmu muna sonki, gata muka miki, Allah yasa auren ya zamto sanadin Aljannar ki".
tuni Aisha ta ɓalle da kuka, dak'yar Ammi ta rarrashe ta, wannan ayar ta ɗauko ta dama mata da nono ta mik'a mata tashanye tas, zumar nan tabata cokali wajen goma, rufesu tayi sannan ta ce idan dare yayi yau anan zaki kwana, gyaɗa mata kai Aisha tayi.

Comments

Popular posts from this blog

Australian Visa Application information: Visa Types & Requirements

[Sunnah] What Muslim Should Observe On The Day Of Eid

Canada Immigration: How To Apply For Canada Permanent Resident Visa