NI AYS NAKE SO Part 9
💅💅💅
💋 *NI AYS NAKESO*💋
💅💅💅
.
*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
_We dont just entertain and educate we also touch the herts ƙf readers_
.
.
_WRITEN BY Princess Eshat Aysm_
.
.
In Dedication to *ABDULLAHI YAHYA SA'AD ZARIYA*
A.Y.S
Page 9
.
.
.
www.Eshataysm.tk
.
.
.
Isowar su bak'aramin mamaki yasha ba, ganin gidan acike tun daga Gate aka fara masa wak'ar ango2, be sauraresu ba yayi wajen Momy da sauri, tana ganinshi ta mik'e ta taroshi, zatayi magana ya rigata, "Mom me yake faruwa ne".
ta ce "je kayi wanka kaci abinci ka huta".
Ya girgiza kai yace "ki faɗamun Momy".
Yanda ya shagwaɓe fuskane abun yabata dariya
"kaga ga bak'i katafi, ina zuwa".
Wajenshi ya nufa da zummar yayi wanka, tun daga nesa yafara ware ido har ya isa ciki, gaba ɗaya tunaninshi tsayawa yayi, yasan wata biyu aka saka biki amma da gaske biki akeyi, kodai wata aka auramun ba Aisha ba, da sauri ya janye wannan tunanin don zai iya aikata kome matuk'ar bai aure ta ba, wanka yashiga yayi sallah sannan yaɗan cakula abincin da yagani, keys ɗinshi kawai ya ɗauka yafigi mota yayi gidansu Aisha, tana kwance jikin Ammi zuciyar ta a cunkushe tana tunanin wani hali Abdul ɗinta yake ciki, taji Abbah yana k'wala mata k'ira, saida gabanta ya faɗi, Ta mik'e da sauri ta nufi wajenshi, sunkuyar dakai tayi tace "Abbah gani".
ɗaukar ta cak taji anyi ana dariya k'asa2, ta buɗe baki zata runtuma ihu yayi saurin saka ɗayan hannun ya rufe bakin, waje yayi da ita a maimakon falon da Abbah yace yashiga, be direta a ko inaba sai cikin motarsa, sai lokacin ta buɗe idon ta, ganin shine yasa tayi ajiyan zuciya gamida ɗaure fuska, be damuba ya ce "labarin da Abbah yabani yayi masifar yimun daɗi, fatana, burina duka sun cika, na auri macen da nafi k'auna a rayuwa ta".
Tsagaitawa yayi da maganar ganin ta fara kuka, a ruɗe yace "Har yanzu baki sona Aisha, kifaɗamun, namiki alk'awarin bazan miki dole ba tafiya ta kamani, bansan hukuncin da kika yanke ba aka ɗaura mana Aure, haryanzu baki sona, kimun magana kidaina kuka".
idonta shaɓe2 da hawaye ta ce "NI
AYS NAKESO".
Wani haske yagani kafin duhu, ya kama kanshi dayaji yana sarawa, ya ce "wanene Ays, a ina yake".
"nima bansan shiba".
Tafaɗa kai tsaye.
"ki daure ki soni, menene baki so tare dani".
Shiru tayi don bayida wani makusa, zuciyar ta ce kawai ta karkata kan wani, a hankali yace "bakida hurumin ambaton sunan wani a yanzu, aurena yana kanki, ki iya bakin ki daga yanzu".
Share hawayen fuskarta tayi tace "bazan sakeba".
Murmushi yayi me ciwo don har lokacin yanajin zafin sunan Ays data ambata mishi, "zan tafi, daga tafiya nadawo duk nagaji, nasan ko cikiyata bakiyi ba".
Murmushi tayi batace kome ba, ya ɗaga gira ya ce "shikenan zantafi dake yanzu, basai ansha wahalar kawoki ba".
a tunanin ta dagaske yakeyi kawai sai tafashe da kuka, murmushi yayi yanaganin inda hawaye yafara ɗiga, ya matsa kusa da kunnen ta ya ce "abun kuka baya miki kaɗan, wasa nake miki".
Murfin motar ta buɗe, kafin k'iftawa da bismillahi harta ɓace, ya susa kanshi yana dariya, fitowa shima yayi tanufi cikin gidan, da Sadiya sukaci karo ya ce "yauwa, ga wannan kibaiwa Auntyn ki, kuyi hidima dashi".
Har k'asa ta tsuguna tayi masa godiya.
.
.
.
Biki akasha dukda babu lokaci amma sun k'ayatar, Amarya da Ango sunyi k'yau kamar a sacesu a gudu, kayan lefe kuwa Mom batayi k'asa a gwiwa ba dozin tayi mata, 'yan uwanshi yanda suke sonshi haka sukayi ta janta a jiki, tunda UNAISA taganta ta lik'e mata,
Su Hajara suna mak'ale da ita, tana kuka suna kuka, dama dak'yar aka ɓanɓareta ajikin Ammi, shi kanshi Abbah saida yayi kuka, bayan anwatse harta ɗan tsagaita da kukan tacew Sadiya "ki kawomun wayata gobe".
Sadiya tace "Ammi ta karɓa, tace idan kin tambaya ace ta fasa shi".
Shiru tayi ranta taji ya ɓaci, ko bakomai taso msg ɗin Ays ya zamto abokin hiranta, tasan har abada shine zaɓin ta dukda bata taɓa ganinshi ba, wasu hawayene masu zafi suka zubo mata, kusa da ita suka matsa suna rarrashin ta, motsin angwaye sukaji tayi saurin jan mayafin ta rufe fuska, duk maganar tasu tsok'anace sai nasiha, ko za'a yankata batasan me suke faɗi ba, tunanin ta ya tafi akan da yanzu gidan Ays aka kaita, ganin su Sadiya sun mik'ene tadawo hankalin ta, ashe wai gida za'a kaisu, nanfa tace zama bada itaba, mik'ewa tayi tana rik'e dasu tana kuka, Faruq yayi murmushinnan nasa, dama tuni abokansa sunyi gaba, hanun ta yarik'e gam ya ɓanɓareta ajikin Hajara, da ido ya musu alamar su tafi ana jiransu.
suna futa yajanyo ta jikinsa, ajiyan zuciya ya sake me k'arfi, mayafin ya yaye, ya tsura mata ido, tayi kyau sosai, hawaye na sauk'a ɗaya kan ɗaya, goge mata yashiga yi amma sai daɗa ɓullowa sukeyi, saitin kunnenta yaraɗa mata "kiyi shiru, gobe zan kaiki gida kinji".
Daren ranar yasha fama da ita, dak'yar yasamu tayi bacci, addua ya tofa mata ya rufe mata ɗakin yafita, donshi tunda ya lura bata sonshi gaba ɗaya jikin shi yayi sanyi.
Washegari kuwa nanma dabara yamata yace gobe zai kaita, tunda sassafe Momy tasa aka kaimusu abun karyawa, ruwan tea kaɗai yasamu tasha, duk yanda taso haka yake binta.
Duk 'yan biki sun watse saura 'yan Niger, suma sungama shirinsu tsaf akan zasuyi sammako su tafi, nanfa Unaisa tace sam batasan wannan zancen ba, bayanzu zata tafi ba, mahaifinta kamar zai daketa Momy tace "mezai hana subarta, ai zumuncin kenan,
dole suka barta sukayi tafiyansu.
.
.
.
.
AYS tunda ya koma aka kasa gane kanshi, dazaran ya fara tuna cewa dagaske tayi aure sai tari ya tashi, ba wanda yasan abunda yake damunshi sai daga baya da aka isheshi da tambaya, wasa2 yafara aman jini, mahaifinshi yayi mummunan kiɗimewa, da taimakon Allah da taimakon likitoci akasamu yaɗan warware, satinsa biyu da warkewa Admission ɗinsa ya fito, yayi murna sosai, nan yafara shirye2 tafiya karatu, har lokacin Aisha tana manne a ransa.
Comments
Post a Comment