NI AYS NAKESO 16 and 17

[6:32PM, 10/21/2017] ESHAT AYSM💅: 💅💅💅
      💋 *NI AYS NAKESO*💋
                 💅💅💅
Page 16
.
.
.

_WRITEN BY Princess Eshat Aysm_
.
.
In Dedication to *ABDULLAHI YAHYA SA'AD ZARIYA*
A.Y.S





.


.
.
*BICHIKI FANS GROUP*
_🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀ kuna sakamun ciwon kai, aljanu dubu 70 ai nasaka kaÉ—anma ycn, hhhhh duk wacce tasawa kanta ciwo ko ajikina🤷‍♀_
Amma inajin daɗin cmmnt ɗinkufa, tare daku zamu tafi Abuja😂😂😂

.
.
.









DaÉ—ine yakama Unaisa tace "Malam nawane kuÉ—inka".
Yayi dariya yace "ba kuɗi zaki biyani ba, duk lokacin dana shirya karɓar wani abu zan k'iraku".
Ya juya dubansa ga Kareema ya ce "ke kam yanzu bakida wata matsala ko, tunda akayi aurenku bakicemun komaiba".
"ba wata matsala malam, kaidai Allah yabarmana kai, a halin yanzu sai abunda nace akeyi".
Wani shu'umin dariya yayi sannan yace suje zai nemesu, kuma zaiyi aiki akan Faruq nanda sati É—aya.
Da farinciki suka bar wajen, duk inda iyayen Unaisa suka so su mata aure tak'i, tun suna damunta har suka zuba mata ido, kareema kuwa ta auri Yazeed yanzu juyashi takeyi son ranta.
.
.
.
Bayan Dr. Rilwan sun fita da Abbah matsalar Aisha yaci gaba da faÉ—a mishi, sannan ya É—aura dacewa "a yanzune matsalar yake k'arami, amma ba k'aramin buguwa tayiba, idan ba'a tareba zata daina gane komai, k'arshe sai ansha wahala kafin ta warke, kuma matsalan gaskiya ba'a samun kayan aikin a garinnan".
Abbah duk jikinsa yayi sanyi ya ce "haka Allah ya k'addara wa Aisha kuma, indai akwai inda ake aikin acikin duniyar nan ko inane zan kaita, a ina ake samu"?
Dr. Yayi ajiyan zuciya ya ce "akwai abokina su aikinsu kenan akan matsalar data shafi k'wak'walwa, a halin yanzu yana aiki a National Hospital dake Abuja, sunada asibitinsu me zaman kansu, zan haÉ—aka dashi, insha Allahu za'a dace, sunanshi Dr. Mansur, sananne ne amma dukda haka zanbaka  numbanshi da address É—inshi sai akaita can".
Godiya sosai Abbah yayi mishi lokacinda yahaÉ—ashi da Dr. Mansur sukayi magana a waya, sun tsaida magana akan washegari zasubi jirgin k'arfe 7 na safe su tafi.
Tunda su Hajara suka fahimci halinda take ciki suke kuka, duk wannan tsiwan Aishan yanzu babu shi, takan zuba ido ne kawai idan anyi magana tagane ta bada amsa idan bata ganeba ta fara hawaye ko kuma tayi dariya.
Washegari kuwa suka nufi garin Abuja.
basu sha wahalan samun Dr. Mansur ba, 'yan gwaje2 yayi mata, ya tausaya mata yarinya k'arama da wannan cuta, donma tanada gata da ankwana biyu hauka zata fara tuburan.
"Alhaji zamu kaita asibitinmu me zaman kanshi, duk masu irin matsalarta ne".
Ammi tace "aikin zai É—au lokacine"?
Murmushi Dr yayi ya ce "sauki nufine na Allah, amma da yardar Allah bazata wuce wata   shida ba, amma munada sharaÉ—i, idan kuka kaita bazaku zauna acanba bazaku dubata ba sai bayan wata uku, kamar makaranta wajen yake, idan iyaye sun zauna muna samun matsala sosai, sannan abunda zataci ku zaku biya kuÉ—inshi kuma basu cin abu me sauk'i, duk kwana É—aya za'a mata amfani da maganin naira dubu 50, dakuma abunda zataci, idan ya muku kuna iya barinta, idan kuma baku shiryaba gaskiya bamu É—aukun wata alfarma".
Kallon kallo Suka shigayi, Ammi ta ce "kana nufin mubar 'yar tamu mu koma garinmu, wannan bazai yiyu ba, da suwa zata zauna"?
murmushi Mansur yayi ya ce "duk inda kuka gani, mudai tsarinmu kenan, akwai ma'aikata sama da dubu, su suke kula dasu".
Abbah ya sauk'e ajiyan zuciya ya ce "wannan ba matsala bace, fatanmu ta samu lafiya, yanzu sai muje muga wajen sai mubar komai a wajenka".
yarfa hanu Mansur yayi ya ce "kuyi hak'uri kuÉ—an jirani, akwai wajen zama yanzu zangama zai mu tafi".
Wani kamfacecen asibitine girmanshi yayi gari guda, iya tsaruwa ya tsaruwa, kaf garin Abuja babu asibiti kamarshi, musamman aka buÉ—eshi don masu ciwon daya shafi k'wak'walwa.
*MANAYS INT. HOSPITAL AND ISLAMIC MEDICATION ABUJA*
Sunan da aka rubuta a jikin katafaren asibitin kenan, sai ware ido su Ammi sukeyi suna mamakin gorma irin na wannan asibiti, wani office suka shiga shima k'atone sosai, da alama office É—inshi kenan, wani file ya É—auko ya fara rubuce2, zuwa can ya fara musu 'yan tambayoyi.
Komai aciki yake rubutawa,
Wasu nurses yak'ira su biyu, nuna musu Aisha yayi sannan ya ce "zuwa gobe za'a É—aurata akan magani, na tsawon sati biyu kafin a mata aiki".
Binsu Ammi Aisha tayi da kallo, sai kuma ta fashe da kuka, "Ammi me yake damuna ne".
Abba ya rungumota ya ce "kiyi hak'uri mamana, zaki warke insha Allah, ko kina tuna abunda yafaru dake a baya"?
GyaÉ—a mishi kai tayi alamar eh, don ita tasan Abbah kuma tasan Ammi duk iyayentane, duk wani rayuwarta datayi kafin aure tana tunawa, har sunan Ays da tunaninshi da kalamanshi sunanan daram akanta, tasan kuma akwai wanda Abbah yace zai aura mata watau Faruq, sannan idan anmata tambaya me nauyi takan kasa gane me ake nufi, amma tamanta komai bayan wannan, tamanta dacewa ta auri wani balle rayuwar datayi dashi.
Murmushi Abbah yayi ya ce "ashe babu abunda yake damun mamana, kinajina, allura za'a koya miki yanda zaki tsulawa mutane, dazaran kin iya kinga kin zama Dr.Aisha".
Murmushi tayi tana kallon Ammi, itama murmushin ne É—auke a fuskarta, wacce Dr Mansur yak'ira da LIDIA ita takamo hanun Aisha tana dariya ta ce "ki taso muje kiga aikinki".
Ta dubi Dr. Cikin yaren indian ci ta ce "ciwon nata ba wani me girma bane, akwai hankali a tare da ita".
murmushi kawai Dr yayi ya ce su tafi da ita.
Abbah harda share k'walla, Ammi kam dama tuni ta fara hawaye, suna gani aka tafi da ita.
Basu bar garinba saida suka gama biyan komai suka tafi akan sai bayan watanni uku zasu zo dubata.
É—aya daga cikin É—akin majinyata aka kaita, É—akine me tsafta harda kayan kallo sai irin gadonnan na marasa lafiya, gefenshi akwai durowa na ajiya magunguna guda biyu, sai k'aramin frige ata bakin k'ofa, akwai kujeru na zama guda biyu.
Lidia ta nuna mata bakin gadon alamar ta zauna, tana zama suka sa kai suka fita.
Bin wajen tagama yi da kallo tana nazarin wani abu, ganin takasa tunanin komai yasa tayi kwanciyarta.
[6:32PM, 10/21/2017] ESHAT AYSM💅: 💅💅💅
      💋 *NI AYS NAKESO*💋
                 💅💅💅
Page 17
.
.
.

_WRITEN BY Princess Eshat Aysm_
.
.
In Dedication to *ABDULLAHI YAHYA SA'AD ZARIYA*
A.Y.S





.


.
.





BuÉ—e k'ofar akayi a hankali aka shigo, Dr Mansur ne, jawo kujera É—aya yayi ya zauna a gabanta, binshi tayi da kallo da manyan idanunta, wani file yaciro daga cikin wanda su Lidia suka ajiye, kallon ta yayi sannan yace "menene sunanki".
Shiru tayi tana tunani, "sunan nakima sai kin tuna"?
Yayi tambayar yana murmushi, itama murmushin tayi ta ce " *ESHA*....
Maimaita sunan yayi har sau biyu, "sunan mahaifin naki kenan"?
Girgiza kai tayi ta ce "Muhd".
KaÉ—a kai kawai yayi ya rubuta, "shekarunki nawa"?
Shiru tayi babu amsa, ɗan tsaki yaja ya ce "zata ɓatamun lokaci".
Duk abunda yadace rubutawa yayi da basirarsa, yana gama ya haÉ—a mata drip ya saka mata sannan ya fita.
Lokaci kaÉ—an tayi bacci.
Lidia ya k'ira ya mata bayanin irin magungunan da zata fara bata kafin a mata aiki, amsa tayi cikin ladabi, yace mata ta kula da ita sosai, idan akwai wani matsala ta k'irashi, nanma amsawa tayi da to, yana gama bata ya tattara yabar cikin asibitin.
D'akin ta koma rik'e da tarkacen abinci, ganin tana bacci yasa ta nemi waje ta zauna ta tsura mata ido, haka kawai taji Aishar ta kwanta mata arai, bin fuskanta tayi da kallo, tanada wani irin k'warjini wanda duk wanda ya tsura mata ido dole yaji ta burgeshi, tananan zaune har ruwan ya k'are, wani ta sake É—aura mata, har lokacin Aisha baccin ta takesha, sai kusan magriba ta farka, Lidia batada aiki sai kula da duk wani motsinta
Tana ganin ta farka ta isa kusa da ita, binta tayi da kallo tanaso ta tuna wacece wannan amma takasa, tashi tayi daga zaunen tana shirin sauk'a Lidia tayi saurin rik'eta, murmushi tayi mata tace "zancire miki ruwan kafin ki sauk'a".
Bai ruwan Aisha tayi da kallo har tacire mata,
Toilet É—in É—akin ta nufa, da sauri Lidia tace "inzo in taimaka miki"?
Murmushi tayi ta kaÉ—a kai.
Ganin komai da komai a ciki yasa tayi wanka ta É—auro alwala, a wajen taga mai ta shafa sannan ta fito.
Abinci Lidia ta fara jera mata, tana murmurshi ta ce "kizo kici abinci".
É—an zuba mata ido tayi, a hankali ta ce "Sallah zanyi".
Shiru Lidia tayi tana kallon ta, ganin babu sallaya yasa ta shimfiɗa ɗankwalinta ta fara Sallah, sake baki Lidia tayi harda buɗe hanci, ita duk zamanta a duniya bata taɓa sanin haka musulmai suke Sallah ba, tana rayuwa da musulmai amma yawanci basu damu dayin sallah ba, bata ganin sunayi.
bakinta a sake har ta idar da Sallahr, É—aga hanu tayi tana addua, ta juma kafin ta shafa, tana jiyowa tayi wa Lidia murmushi, itama murmushin tayi ta matsa da abincin kusa da ita ta ce "kici yanzu, maganinki baya son zama da yunwa".
Zagewa tayi ta ci abincin sosai, bawai abincin yamara daɗi ba, ita sam batason abunda zai taɓa lafiyarta, tunda taji ance maganinki baya son yunwa yasa ta ɗura sosai, tana gamawa ta mij'e zata kwanta, Lidia ta rik'o hannunta ta ce "tsaya kisha magani".
Komawa tayi ta zauna.
Koda ta É—auko maganin rasa wanne zata bata tayi, gaba É—aya ta rikice, ta rasa wanne akace tafara bata, dake zuciyarta tayi ta É—auko wanda ranta yafi karkata akan shine wanda zata fara bata.
ɓallowa tayi ta mik'a mata sannan ta mik'a mata ruwa, tana tsaye sai da taga ta haɗiye kafin ta mata murmushi ta ce "kada ki kwanta yanzu, idan maganin yaɗan sauk'a ciki sai ki kwanta, kinga abincin da kika cima bai gama sauk'a ba, zanje na dubo wata yanzu zandawo".
murmushi kawai Aisha tayi domin ba duka maganar ta fahimta ba.
Ta fita baifi da minti 5 ba, kanta ya fara juyawa, wani iri ta fara ji, hatta yatsunta rawa sukeyi, lokaci k'ank'ani É—akin yafara juya mata sosai, ji take kamar mutuwa zatayi, wani k'ara ta saki ta kwanta a wajen.
Lidia dake bakin k'ofar tana shirin shiga taji k'aran da gudu ta shiga cikin É—akin, ganin halinda take cikine yasa tayi bala'in kiÉ—imewa, zama tayi a gabanta tana tambayar ta "me yake damunta, me takeji".
Ganin idonta ya fara kakkafewa yasa ta k'ira Dr. Mansur, tana kuka take faÉ—a mishi halinda ake ciki.
Kashe wayar kawai yayi.
Mintina baifi 10 ba ya iso, ganin halinda take ciki shima ba k'aramin ruÉ—ewa yayi ba, duk wani taimakon gaggawa ya mata amma yakasa gane matsalar, wayarshi ya ciro da sauri yafara dialin numba.
"Abdul kayi hanzari kashigo ina nemanka".
Ta ɗaya ɓangaren akayi magana,
"babu maganar wasa kayi hanzari abokina don Allah kada ka ɓatamun lokaci yarinta zata mutumun".
ajiye wayar yayi ba tare da yasan yakashe ko be kashe ba.

Comments

Popular posts from this blog

Australian Visa Application information: Visa Types & Requirements

[Sunnah] What Muslim Should Observe On The Day Of Eid

Canada Immigration: How To Apply For Canada Permanent Resident Visa