BENZEMA

📨📨📨📨📨📨📨📨📨📨
*BENZEMA*
📨📨📨📨📨📨📨📨📨📨
page 1
.
.
writen by *PRINCESS ESHAT AYSM*
(AISHA BICHIKI)
.
.
DEDICATED TO
*SADIQ ABDULLAHI BENZEMA*
.
.



gmail: Eshataysm@gmail.com
📨
07014612958 for cmmnt.
Eshataysm.tk
my blog
.
.



Dogon matashine fari k'al dashi, kallo É—aya zakayi masa ka tabbatar da tsananin kyawunsa, yana sanye cikin blue É—in jins da riga jareen, fuskarshi mak'ale da farin glass wanda ya k'ara fito da kyakkyawan fuskarshi, hanunshi mak'ale da agogo k'irar Sabbson, tsaye yake ajikin wata mota da alama jiran wani yakeyi, saidai fuskarshi a É—aure tamau yana kallon abunda yaÉ—auke masa hankali, 'yan matane guda biyu kansu É—aure da k'aton daro, dagani talle zasuje, wani dake gefensu yace "ke zo kizubamun doya".
da hanzari ta sauk'e,dak'yar saboda tarin yawanshi, a ɗan nesa ɗayar ta zauna tana jiranta, ita da alama zoɓo take sayarwa.
"na nawa zan zuba maka"?
Ta tambaya tana tauna cingam, cikin muryar mashaya yace "cikamun robar".
Cikawa tayi ta mik'a masa, cikin k'ank'anin lokaci ya cinye, ta karɓi robarta tace bani 100 natafi, wani kallo ya watsa mata yace "bani dashi".
A hasale tace "wlh baka isaba, kasan bakadashi zakacimun kaya to wallahi saika bani kuÉ—ina".
ko kallo bata isheshi ba ya É—auke kansa yana kallon wani gefen, masifa ta hauyi kamar zata kamashi, fuskarshi cike da masifa ya juyo ya sharara mata mari, *BENZEMA* dake nesa yana hangosu ya runtse ido yanajin k'una a cikin ranshi, cikin takunsa a hankali ya isa wajen, kamar bazai iya magana ba yace "nawane kuÉ—inki"?
Cikin kuka tace "naira 100".
500 yazaro a jikinsa, dukda kuɗin jikinshi kenan haka ya mik'a mata yasa kai yabar wajen batare da ya saurareta ya karɓi canjinba, fuskarsa cike da ɓacin rai, ji yake kamar yayi kuka, daf zai shiga mota wata matashiyar mata ta tsaya a gabanshi, dukda bai saurare ta ba yasan kuɗi take nema, wuceta yayi yashige motar, daidai lokacin wanda yake jira yashiga motar.
tada motar yayi yaɗau hanya sannan ya taɓe baki yace "yauma mata sun saka kuka ko".
shiru yayi masa ya É—auke kai, Abokin nashi yayi dariya yace "Allah ya kyauta".
bawanda yasake magana har suka isa cmpnd É—in gidan, ko kashe motar baiyi ba Benzema yayi saurin shigewa ciki, Murmushi Saif yayi yana k'ok'arin fita a motar.
A falo ya taradda mahaifiyar shi wacce suke k'ira Ummi, kusa da ita yaje ya zauna yace "Ummi sannu da gida".
K'are mishi kallo tayi naɗan lokaci sannan tace "Sadeeq bakajin magana ko, meyasa sau goma zaka fita sai kadawo ranka a ɓace, kai kenan kullum haka zaka kasance"?
Zunɓura baki yayi kamar zaiyi kuka yace "Ummi har yaushe mata zasu daina gararanba agari, su masu ɗaurawa yaransu talle basu san abunda yadace bane? Ga sana'a kala2 wanda zasuyi acikin gida su sami kuɗi basai sun fitaba amma...
Shiru yayi yana kallon ummi data tsareshi da ido, murmushi tayi don tasan tatsuniyar gizo bata wuce ta kok'i, kanshi ta shafa tace "inbanda abunka, abunda mace zatayi acikin gida ta samu wani abu ai sai idan tanada babban jari, akwai sak'a, akwai É—inki, akwai haÉ—a irin mayuka damuke sayarwannan, su turarruka, gasunan dai dayawa, amma duk sai kanada kayan aikinsu kuma kaga idan babu hali a ina zasu samu, dole yaransu suyi talle don samun abunda zasuci".
shiru yayi can yace "su kuma masu barace barace fa"?
Saif ne yashigo yace "Ummi wannan É—an naki kamata yayi kidaina barinshi yana futa".
Harara ya watsawa Saif yana murmushi, yace "zakasha  mamaki duk ranarda nasamu dama akansu damar zata k'are".
Ummi tayi dariya tace "Allah ya taimakeka akan kyakkyawan nufi".
"Ameen".
suka amsa dukansu sannan ta gabatar musu da abinci.
Har isha suna tare da Saif kafin yayi masa sallama yatafi, tunda ya kwanta yanemi bacci yarasa, tunanin rayuwarshi yafara kafin mahaifinshi ya rasu.

Comments

Popular posts from this blog

Australian Visa Application information: Visa Types & Requirements

[Sunnah] What Muslim Should Observe On The Day Of Eid

Canada Immigration: How To Apply For Canada Permanent Resident Visa