NI AYS NAKE SO 28

💅💅💅
      💋 *NI AYS NAKESO*💋
                 💅💅💅
Page 28

.

.

.

_WRITEN BY Princess Eshat Aysm_

.

.

In Dedication to *ABDULLAHI YAHYA SA'AD ZARIYA*
A.Y.S

.

.

.

Ranar wata talata da daddare, yayi daidai da saura kwana 2 Aisha ta cika wata uku, tana kwance idonta yana lumshe kamar me bacci, wani iri takeji kamar zuciyarta tana bugawa, ba abunda yake damunta sai tunanin wani irin rayuwa zatayi idan ta rabu da AYS, taya zatayi ya gane itace Aishar sa, a hankali hawaye ya fara sauk'o mata, tasan idan har tabar garin bai ganeba ta rasashi kenan har abada, wayar Lidia ne taji yafara ruri, tsaki taja ya katse mata tunani, harya tsinke aka sake k'ira, sauk'a tayi a hankali ta isa inda Lidia take ta fara tashinta, a firgice ta tashi tana zare ido, batace mata komaiba sai nuni da ta mata da wayarta, da bacci cike a idonta ta isa wajen wayar ta ɗauka, ganin sunan ne yasa ta zaro ido tana mamaki, bata daina mamaki ba har k'iran yasake katsewa, a karo na uku a ka sake k'ira, ɗauka tayi tana baza hanci kamar ta wajen zataji maganar, Aisha dai ta tsura mata ido, dariya ta bata sosai ganin yadda take magagin bacci, da sauri taga Lidia ta nufo wajen ta, tana mik'a mata ta ce "oga yana magana dake".
ita kanta mamaki ya gama kamata, ganin Lidia ta koma baccinta yasa tayi ajiyan zuciya tasa wayar a kunnenta, cikin wani irin kasallaliyar muryan da bazata taɓa Mantawa dashi ba taji yana k'iran sunanta, har hawaye ta farayi, yau ta daɗa yadda shine Ays ɗinta, muryanda tayi rayuwa dashi na k'ank'anin lokaci, ya zauna a zuciyarta na tsawon shekaru.
"_Aisha bakijine"
Nutsuwarta ta saita ta ɓoye mamakinta tace "bacci nakeyi".
murmushi yayi ya ce "ESHA nakasa bacci".
Da damuwa ta ce "meke damunka".
numfashi ya sauk'e a hankali kamar me raɗa ya ce "tunaninki".
waro ido waje tayi ta ce "kafaɗamun".
shiru yayi na tsawon lokaci kafin ya ce "ina zuwa yanzu".
Zatayi magana ya kashe k'iran.

Tananan zaune cike da tunani kala2, ko minti 10 ba'ayi ba ya sake k'ira, "kifito kisameni a mota".
haka kawai ya faɗa ya kashe, tsura wa wayar ido tayi, ko bakomai taji daɗi zata ganshi kamar sun juma da rabuwa, hijab ɗinta kawai tasaka ta fice, dai2 inda yake ajiye motar ta hangoshi, cikin nutsuwarta ta k'arasa, tunda ya hangota yaji wani sabon farinciki, tabbas rayuwarshi zata zama wani iri idan ta tafi, minti tayi bata kusa dashi yakanji duniyar tayi masa zafi, shikam yana mamakin wannan al'amari.

Murfin motar ta buɗe ta shiga, idanuwa ta zuba masa tana murmushi, kafin ta ce "Ashe lafiyarka lau".
Lumshe ido yayi ya ce "haka kika gani, inaso ki nutsu sosai, duk maganar dazamuyi yanzu babu wasa aciki, inaso nasan ke wacece, sannan nafi matsuwa nasan waye FARUQ a rayuwarki, naso barin komai a cikina amma bazan iya ba, inaso zumuncinmu ya ɗaure na har abada".
Taji daɗin magar tasa, wannan ya nuna alamar tana cikin rayuwarsa kuma baya fata ta fita, a hankali tashiga kwararo masa labarin Aurenta da Faruq, amma ko kaɗan batayi gigin sanar dashi tayi rayuwa da wani AYS ba, tadai faɗa mishi bata wani sonshi aka aura mata wani takeso, sannan tafaɗa mishi irin dukan daya mata da sakin daya mata, ajiyan zuciya ya sauk'e me k'arfi, da lumsassun idanuwanshi yake kallonta sannan yace "wanene wanda kike so ɗin, a ina yake".
Shiru tayi can tace "yayi mun nisa, a halin yanzu na manta dashi".
Hancinta yaja ya ce "ashe ke bazawara ce"?
Sunkuyar dakai tayi tana murmushi a ranta tanajin haushin sunan.

D'aure fuska yayi alamar babu wasa, da wani irin yanayi ya ce "ɗago ki kalli cikin idona, wani irin k'warjini yayi mata, ta sunkuyar dakanta da sauri, ɗago haɓarta yayi da hannunshi ya ce "ki kalleni Aisha, inaso ki ganemun menene a ciki"?
A hankali ta kalleshi, runtse ido tayi da sauri wani abu na mata yawo a kanta, a hankali ya ce "zaki rayu dani"?
Dukda tambayar ta daki zuciyar ta, ta daure ta ce "wani irin rayuwa kuma"?
hancinta yaja ya ce "rayuwar da kika sani".
Kallon rashin fahimta tayi mishi, ya ce "Aisha, inasonki, inaso na rayu dake, nasan so, nasan shi nake miki, a yanzu bana gane komai sai ina tare dake, idan naganki a kusa dani kuwa, nakanji zuciyata kamar zata fashe, saboda tsan2 so, nasan masifar so tun akan ESHATA, haka nake jinki a raina, zaki rayu dani".
Tunda yafara maganar take kallonshi bako k'yaftawa, ji takeyi kamar mafarki takeyi, ganin shima ya tsura mata idone yasa ta sunkuyar da ƙkanta, jan hancinta yayi yace "kallonnan naki yana tsumani".
daɗa sunkuyar dakai tayi tanajin sanyi a ranta, ganin bazatayi maganaba yasa ya ce "Babu wani lokaci Aisha, kidaina tunanin komai ni nasan zan zame miki gata a rayuwarki, ni nadace dake, ina tunanin iyayenki suzo a jibi su rabani dake ban faɗa miki abunda yake raina ba, idan kin amince, idan sunzo tare dani zamu tafi ayi maganar aurenmu".

Daɗine ya ratsata jin maganarsa, fuskarta ta ɓoye cikin hijabi ta ce "nifa bazawara ne".
Wani irin faɗuwar gaba yaji har cikin kanshi, bayaso ya tuna cewa wani ya taɓa raɓarta, wani kallo yayi mata dukda kanta na cikin hijabi ya ce "to menene, abunda nasani kawai shine inasonki, bazan iya rayuwa babu ke ba, ki manta da cewa kin taɓa aure, nima zan manta da haka, banaso na sakejin kin faɗa".
ɗaga mishi kai tayi, yayi murmushi ya ce "nagode".

Ranar dukkaninsu kwanan cikin farinciki sukayi, musamman da Abdul daya kwana yana adduar Allah yasa ta zamto alkairi a gareshi, koda yafaɗawa Mansur yayi masa fatan alkairi, a ramshi ya ce "gara da banyi katoɓara ba, don farkon ganinta yaji ta kwanta masa arai, Aisha irin matannan ne da kallo ɗaya namiji zai musu yaji yana sonsu saboda k'warjini bawai tsantsan kyau ba, Mamsur ya tayashi murna sosai, suka tsayarda magana akan idan iyayenta sunzo zai bisu su tafi tare.

.
.
.
.

Anyi Auren Faruq da Sadiya satin da yagabata, zuwa yanzu son juna sukeyi sosai, sai a lokacin Faruq yasan menene auren, a baya soyayyar Aisha ta hanashi gane menene fari menene bak'i, rayuwa sukeyi me cike da kulawa, dukkansu jefi2 sukan tuna Aisha daga baya su rarrashi juna, itakam momi kullum takan godewa Muhammad mesaje bisa karamcimsa garesu, don haka ta rik'e Sadiyar kamar 'yarta, dukda wani gefe na zuciyarta tafi k'aunar Aisha, tanason yarinyar sosai, to Sadiyar ma batada laifi, tafi Aisha sakewa da wayewa, idan tana zuba mata hira kai kace ba surkuwarta bane, hakan yana burge Faruq matuk'a, kullum sai momi tayi sadaka Allah ya baiwa Aisha Lafiya.

Comments

Popular posts from this blog

Australian Visa Application information: Visa Types & Requirements

[Sunnah] What Muslim Should Observe On The Day Of Eid

Canada Immigration: How To Apply For Canada Permanent Resident Visa