NI AYS NAKE SO 29

💅💅💅
      💋 *NI AYS NAKESO*💋
                 💅💅💅
Page 29

.

.

.

_WRITEN BY Princess Eshat Aysm_

.

.

In Dedication to *ABDULLAHI YAHYA SA'AD ZARIYA*
A.Y.S

.

.

.

Ohhh *Abunda yafi k'arfin kuka sai salati, don Allah waye ya buɗe account da sunana a fcbk🙆🏻😢, Princess Eshat Aysm biyu ne a fcbk kuma duk nice, yanzu kuma naga sun zama uku🤔😡😡😡*

*Grup ɗin da ake buɗewa da sunana a wtsp sam baya damuna, amma wannan kam naji haushi😡😡😡😡😡 don Allah wacce ta buɗe ko ya buɗe kumin magana🙏🏻*

.
.
.
.

Momin Faruq tunda taji ranar Juma'a za'aje duba Aisha ta ce "ita zataje, da kanta taje ta samu Abbah ta ce "ita zataje, shima bai matsa sai yajeba saboda Dr daya turasu ya k'irashi ya faɗa mishi ta warke idan sunje tare zasu taho, Farinciki a wajensu baya misaltuwa, hatta k'awayenta saida Hajara ta tarosu ta faɗa musu Yau Aisha zatawo, gida kam ya cika fal tun kafin lokaci yayi nisa, dayake jirgin safe tabi zuwa 10 ta isa, address ɗin da Abbah ya bata dashi tayi amfani yakaita har asibitin da Aisha take.

Tana zaune a gefen Dr Abdul yana duba wata duk yagama gajiya, dak'yar yasamu yashawo kan lamarin, lumshe ido yayi yajingina yana kallon Aisha, murmushi tayi masa tace "sannu".
Shima murmushin yayi yace "banyadda da wannan sannun ba".
ɗan shagwaɓe fuska tayi ta ce "zanyi wanka na shirya, katashi mutafi".
"waye ya faɗa miki zaki tafi, sai kincika wata shida".
Da wasa yayi maganar itakam ta ɗauka da gaskene, wani irin kuka ta fashe dashi tana bubbuga k'afa, kama baki yayi yana kallonta, can kuma yafara mata dariya, kukan tafara da iya k'arfinta, tsagaita dariyar yayi ya ce "kin kasa gane kin girma yarinyarnan, abu kaɗan sai kuka".
Cuno bakin tayi ta ce "nadai ji, katashi mutafi".
a gajiye ya mik'e yanufi kusa da ita, ɗan sunkuyawa yayi ya sumbaci goshin ta ya ce "har murna kikeyi zaki daina ganina ko, to bazan yadda ba tare zamu tafi".
wani irin murmushi tayi masa dayasa tsik'an jikinsa tashi, ta ce "inaso naga kowa da kowa, koda naɗan lokacine, kai kuma nafiso nazauna dakai na tsawon rayuwata".
waro ido yayi yana kallon ta, yaji daɗin kalamin nata, a hankali ya ce "abunda kika faɗa gaskiya"?
Cike da kunya ta ce "Eh".
murmushi yayi yaja hanunta suka tafi.

A gaggauce tayi wanka ta shirya cikin wata dogon riga milk colour, ruɓi biyune ɗayan ruɓin bak'ine da wani zanen flower me kalan golden ajiki, kwalliya tayi sosai, mayafin nashi me ɗan girma ta yafa, Lidia ta sake baki da hanci ta ce "yau kinfi kullum kyau, ina zuwa yau kuma"?

Murmushi tayi mata kafin ta ce "inasa ran zuwan iyayena yau, kuma tare zamu tafi".
Sosai Lidia taji babu daɗi, jiki a sanyaye ta ce "inaso muyi wata magana kuwa....
Sallamar da akayi shi ya katsesu, Momi ce tashigo tare da Dr Mansur, fuskarta ɗauke da Farinciki, da saurari Aisha ta faɗa jikin ta, sai kuma ta fashe da kuka, ɗan buga bayanta Momi tashigayi tana rarrashinta duk da batasan dalilin kukan ba, ɗan tsawon lokaci ta saketa suka zauna, tanata jira taga ta ina Ammi da Abba zasu ɓullo amma shiru, jiki a sanyaye suka gaisa da Momi ta tambaye ta ya jikin, sai binta da kallo Momi takeyi ganin ta murmure sosai tafi da cika da kyau, kamar ba jinya aka kawota ba, Dr Mansur ya ce "yau dai zaki koma gida, fitina ya k'are".
ya k'arasa yana dariya, zunɓura baki tayi batace komai ba, ita jira takeyi taga ta ina Abbah zasu shigo.

Wani gefen zuciyarta tana jiran Abdul, ɗan abun taɓawa Lidia ta kawo wa Momi, kaɗan taci, ta kalli Aisha taga tayi kicin kicin da fuska, saura kaɗan ta fara kuka, Murmushi Momi tayi kamar tasan abunda yake ranta ta ce "matso kusa dani 'yata, ni dakaina na rok'i alfarmar a barni naje na taho da ɗiyata, idan kin shirya ki taso mu wuce".
daɗine ya kamata, kaya ko kala ɗaya bata ɗauka ba, duk tabarwa Lidia su, jiki a sanyaye ta ce "ina Dr Abdul".
Cikin zolaya Mansur ya ce "yatafi zaria ɗazu...
Bai k'arasa ba tafashe da kuka, Momi tayi shek'ek'e tana ganin ikon Allah, a ranta tace "anya ta warke kuwa".
Kuka takeyi sosai, Lidia ta jinjina kai tana dariya, ganin da gaske take kukan Mansur ya ce "Momi ko zaki barmana ita ina tunanin bata gama warkewa ba".
Murmushi Momi tayi don tagane tsokanarta yakeyi.
Sallamar sa ne yasa ta sauk'e ajiyar zuciya me k'arfi, da sauri ya k'arasa cikin ɗakin, fuskarsa a ɗaure yafara tambayar waya sata kuka.

Nuna mishi Mansur tayi da baki, cike da Masifa ya juya, sai asannan yaga Momi, da sauri ya tsuguna ya gaishe ta fuska a sake, tace "ina fata zamu iya tafiya da ita"?
Kallon Aishar yayi yaga itama shi take kallo, tun a lokacin kewarta ta fara kamashi, ya susa kai ya ce "bari nadubata, idan babu wata matsala sai ku tafi".
Kallon Aisha yayi da niɗimammun idanuwansa ya ce "muje".
ba musu tabi bayansa, har office ɗinshi suka shiga, key yasaka yajuya yana fuskantar ta, izuwa lokacin idanuwansa sunyi jaa sosai, matsawa daf da ita yayi ya ce "Aisha, inaji kamar bazan iya bari ki tafi ba, kinga ba Abbah bane yazo balƙe nayi masa bayanin kaina, don Allah kizauna wallahi zan iya shiga wani hali idan kika barni".
Waro ido tayi ta ce "gaskiya na matsu naga iyayena, karka damu, kabimu mutafi kamar yadda muka tsara".
tsura mata ido yayi kafin ya rik'o hannunta, yaɗan matsa yatsunta ya ce "idan naje bazan dawo ba sai an auramun ke".
Murmushi tayi ta sunkuyar dakai, yaja hancinta ya ce "wacece wannan ɗin, jikina bai bani Ammi bace".
ɗago ido tayi tana kallonshi, sannan tayi murmushi ta ce "Mahaifiyar Faruq ne".
Wani kallo yayi mata cikeda kishi ya ce "ok tazo biko ko, to bazaki bita ba...
faɗa yashiga yi sosai, itadai tana mamakin kishi irin nashi, gaba ɗaya futa a burki yayi, saida yagama surutunsa sannan ta ce "ana bikon zaki uku ashe"?
susa k'asan sumanshi yayi ya ce "abu me sauk'ine ai".
dariya tayi taja hancinsa ta ce "inason wannan kishin, bawani wanda zai sake rabani da farincikina...
sai kuma tayi shiru,

Ido ya lumshe yanajin inda sonta yake ratsashi, abun har tsoro yake bashi, idonshi yana ƙlumshe yajawo ta da k'arfi ta faɗa jikin shi, hannuwa yasa zai rungumeta tayi saurin bige hanun ta matsa gefe, numfashi ya sauk'e a hankali ya ce "Ina sonki Esha, haɗuwata dake tayimun daɗi, zan rik'eki da amana, murmushin ki shiya fara tsumani naji ina ra'ayinki...

Buga k'ofar dayaji anayi ne yasashi yin shiru, ko ba'a faɗa ba yasan waye zai masa wannan iskancin, daɗa mik'ewa yayi ya kwanta idonshi na lumshe, itakam inbanda ido babu abunda ta zuba mishi, a hankali ta isa ta buɗe k'ofar, tun kafin yashiga ya fara binsu da kallo, baki Ya taɓe ya ce "wannan kuma wani salon iskancine, ni nasan babu wani abunda zaka bincika, idan zaka bata yarinya su tafi ka bata".
Ko buɗe ido baiyi ba balle yayi magana, yanaji Mansur yanata ɓaɓatu k'arshema yadaina sauraran me yake faɗa.
Jiki a sanyaye Aisha ta nufi k'ofa da niyyar fita, wani tsawa ya daka mata yace "ina zakije"?
Baki buɗe ta tsaya tana kallonshi, tsaki yaja ya watsawa Mansur harara sannan yajata suka fita, taɓe baki Mansur yayi ya ce "kaji dashi, mutum sam bayabin So a hankali, wataran sai kanka ya kunce".
Ko kallonshi Abdul beyi ba suka tafi.

Cewa Momi yayi akwai abunda zaifaɗawa Abbah dole su tafi tare..

Sai yamma lis suka isa garin Bauchi..

Sai kunjini anjuma...

Comments

Popular posts from this blog

Australian Visa Application information: Visa Types & Requirements

[Sunnah] What Muslim Should Observe On The Day Of Eid

Canada Immigration: How To Apply For Canada Permanent Resident Visa