NI AYS NAKE SO 30
💅💅💅
💋 *NI AYS NAKESO*💋
💅💅💅
Page 30
.
.
.
_WRITEN BY Princess Eshat Aysm_
.
.
In Dedication to *ABDULLAHI YAHYA SA'AD ZARIYA*
A.Y.S
.
.
.
Kai tsaye gidan Momi suka wuce, Aisha dai taso su sauk'a a gidansu amma bayanda ta iya dole suka bi Momin, tana shiga taji gabanta yana faɗuwa, abubuwa da yawa sun canza a gidan, angyara shi kamar sabo, a falonta ta sauk'esu, rayuwar datayi na shekaru uku yazamo mata sabo, haka kawai taji tanaso taga Faruq.
Da hanzari Momi tawuce ɗaki tana cewa "ina zuwa".
Dr Abdul ya sauk'e ajiyan zuciya a hankali ya ce "matso kiji".
Nok'ewa tayi ta ce "gulma ba kyau".
D'an murmushi yayi yana shafa kai ya ce "kamar kinsan kuwa shi zanmiki".
Murmushi kawai tayi don tasan fitinane kawai.
Ya sha'afa da kallonta Momi ta fito, wayarta ta ɗauka tafara k'ira, ana ɗauka ta ce "nadawo, amma ina tare da bak'i, a kawo musu abinci".
Dr Abdul ya mik'e yace "naga masallaci ajikin gidannan, zanje nayi Sallah".
Momi ta ce "to Dr, kaɗanyi hanzari saboda mu wuce, kaga iyayenta sun fara k'ira".
Russunawa yayi kafin yafita, da kallo Aisha tabishi har ya ɓace, wani ajiyan zuciya ta sauk'e tana murmushi, ganin komai takeyi kamar a mafarki.
Momi ta zauna kusa da ita jiki a sanyaye ta ce "wannan Doctorn kamar na taɓa ganinshi nake nagani".
Aisha ta sunkuyar dakai tace "hala ko kamane".
Shiru Momi tayi kamar me tunani...
Basu ankara ba sukaji an shigo da gudu cike da murna, kai tasaye kan Momi ta faɗa tana "Oyoyo momina".
ita sam bata lura da wacce take zaune ba, baki sake Aisha ta mik'e cike da mamaki, da Sauri ta ce SADIYA".
Itama Sadiyar da sauri ta juyo jin muryan Aisha, tana ganinta ta sake Momi ta k'ank'ame Aisha, rungume juna sukayi suna dariya, wani gefen zuciyar Aisha ya cika da mamaki, itakam Sadiya farinciki fal ranta ta ce "Aunty munyi missn ɗinki wallahi, Allah yasa kin warke muci gabada rayuwar mu, me zakici na kawo miki".
Daidai lokacin Faruq ya shigo, baki a zunɓure ya fara magana, "Mom shina da kika dawo baki k'irani ba kika k'irata ko, ni inaganin wariya a gidannan".
shi baima lura da Aisha ba, a hankali Aisha ta zame jikinta ana Sadiya, ko ba'a faɗa ba tasan Sadiya ta zama matar Faruq, mamakinta k'aruwa yayi tana tunanin taya akayi haka ta faru, duk sunsha jinin jikinsu sun dawo hankalinsu, Faruq baki buɗe yake kallon Aisha ko k!yaftawa bayayi, Abdul ne ya shigo da sallamarsa, ganinsu cirko cirko yasa yabisu da kallo, ganin kallon da Faruq yakewa Aisha yasa kishin nasa ta motsa, a zafafe yaja hanunta suka bar falon.
Ajiyan zuciya Mom ta sauk'e ta ɗauko mayafinta ta ce "zamu k'arasa, saina dawo".
jikin Faruq duk yayi sanyi yakasa cewa komai, Sadiyace tafara borin zata bita tace tabari sai gobe.
bataso ba haka ta hak'ura.
Abdul daya jata suka fita ko nisa basuyi da falon ba ta fashe da kuka, tsayawa yayi yana kallonta, ranshi a ɓace ya ce "saboda kinga tsohon mijinki kike ɓare baki, sai ki koma kiyi ta kallonshi".
hanunta ya zare ya fara tafiya ya nufi wajenda ya ajiye motarsa, zuciyar shi har k'una takeyi, baiyi tunanin komaiba yanufi motar zai shiga, da gudu ta k'arasa ta rungume shi ta baya ta saki kuka mara sauti, runtse ido yayi yana faɗin Innalillahi, duk wani tsikan jikinshi saida suka tashi, a hankali ya jiyo da ita tagabanshi yafara share mata hawayen, ganin bazasu k'areba yasa ya zuba mata ido, shi haushin gidanma yafara ji...
Momi ce ta nufosu da saurinta, yana hangota ya janye Aisha a jikinsa ya koma gefe, ko kallonsu batayi ba tashiga sit ɗin baya tana cewa muje ko".
haka suka shiga suka nufi anguwarsu Aisha kowa da abunda yake sak'awa a ranshi.
lokacin k'arfe 8 saura na dare, duk duhun daya rufe garin bai hana Abdul gane wannan anguwar ba, bugun zuciyarsa bai tsaya ba har suka isa k'ofar gidansu Aisha, da matsanancin mamaki yabita da kallo, ji yake kamar ya fito da zuciyarshi waje ko zata daina harbawa, jin tsayuwar mota yasa Abbah yafito rik'e da carbi a hannunshi, ta cikin glass Abdul yabi Abbah da kallo, da sauri ya dubi Aisha, lokacin Momi harta shige cikin gidan.
"Aisha wannan ne mahaifin naki"?
kafi ta bashi amsa Abbah ya k'araso wajen, cike da murna ya buɗe ta gefen da ya tabbatar tana wajen, itama da sauri ta rungume Abbah tana kukan Farinciki, tayi kewarsu sosai.
Comments
Post a Comment