NI AYS NAKE SO 31

💅💅💅
      💋 *NI AYS NAKESO*💋
                 💅💅💅
Page 31

.

.

.

_WRITEN BY Princess Eshat Aysm_

.

.

In Dedication to *ABDULLAHI YAHYA SA'AD ZARIYA*
A.Y.S

.

.

*CLASSIC WRITERS ASSOCIATION*
C.W.A

.
.
.

Su Hajara suna ganin Momi sukayo waje da gudu, suka zo suka ruk'unk'ume Aisha, dak'yar Abbah yajanyeta suka shiga, ɗakin Ammi yakaita, Ammi tana ganinta farinciki ya kamata, kowa murna sunajin ranar kamar daren sallah, Abbah waje ya koma don yayi tsammanin da Faruq suka taho, hango Abdul yayi jingine ajikin motar ya harɗe hannayensa a k'irji, shi kanshi bazai iya misalta halinda yake ciki ba, jinshi yake kamar yana yawo a sararin samaniya, dayake darene kuma Abdul ɗin ya k'ara girma sosai, shiyasa Abbah bai ganeshi ba, hasken lantarkin dake haska wajen shi yadaɗa taimakawa wajen ɓoye kamanninsa, hanu Abbah ya mik'a masa suka gaisa a mutunce, tambayarsa yayi tare suke ko, Abdul yace "Nine Doctorn Aisha, akwai bayani ne shiyasa muka taho tare".
Abbah ya faɗaɗa fara'arsa yace "atohh tohh mushiga daga ciki".
Cikin takunsa yabi Abbah abaya.
ɗakin bak'i yakaishi sannan yasa aka haɗa masa kayan abinci, har Ammi saida tazo suka gaisa, tayi masa godiya sosai, murmushi kawai yabita dashi, mutanen sunyi masa.
Da wuri Momi ta koma gida tace da safe zata dawo, tunda 'yarta tadawo babu zama, godiya sosai Abbah yayi mata.
Ranar Aisha saida suka raba dare suna hira da Ammi, Hajarama a ɗakin ta kwana, kusan k'arfe 2 nadare ta zabura ta tashi zata fita, Ammi ta ce "ke lafiyarki kuwa, ina zakije muna cikin magana".
ɗan sunkuyar dakai tayi kamar zatayi kuka tace "zan duba Dr ne".
Zaro ido Ammi tayi tace "kin kalli lokaci kuwa, me zaki masa idan kin dubashi".
Shiru tayi babu amsa, Ammi ta ce "dawo ki kwanta kiyi barci".
zunɓura baki tayi tace "Ammi to ki rakani, dubashi kawai zanyi ko yayi bacci".
Da mamaki Ammi tace "idan baiyi ba kumafa".
abu kamar wasa tasa wa Ammi rigima ita dole sai taje ta dubashi, jikinta yana bata idonshi 2, tun Ammi tana masifa harta fara lallaɓata amma k'arshe tafashe mata da kuka, Hajara data fara bacci tace "Ammi don Allah ki rakata taje, kinsanta da naci, yanzu saita hanamu bacci, ajiyan zuciya Ammi ta sauk'e ta ce "muje to".
zuciyar fal mamaki, daga nesa da ɗakin Ammi ta tsaya ta ce "ki lek'a ta window kizo yanzunnan, "to".
kawai tace tayi gaba.
Kamar daga sama yaganta tana tahowa, lokacin yana tsaye jikin k'ofa don bazai iya bacci ba, burinsa gari ya yawe yatabbatar da ba mafarki yakeyi ba, da sauri ya fito shima suka ci karo a bakin k'ofar, ba k'aramin razana tayi ba, tayi baya da gudu zata koma ya fizgota, saura kaɗan ta faɗa jikinsa, Murmushi yasakar mata ya ce "me kike nema"?
itama murmushin tayi ta ce "nazo duba ajiyata, nasan ya kasa bacci".
hancinta yaja ya ce "taya za'ayi yayi bacci bayan yashiga haske da duhu a tare, Esha, nan gidanku kuma mahaifinki ne ba mafarki nakeyi ba"?
kallon mamaki tayi masa ta ce "eh".
janyo ta yayi zai rungumeta tayi saurin ja da baya, numfashi yafara sauk'ewa har yakasa magana, juyawa tayi bayanta, ganin Ammi tana tsaye ta ce "kayi bacci don Allah, Ammi tana jirana".
batajira me zaice ba tayi gaba, da kallo yabita cike da tsananin so fiyeda ko yaushe, kamar yasace ta ya gudu haka yakeji, dayake darene duk abuda suka faɗa a kunnen Ammi, bin Aisha tayi da kallo har suka shiga ɗaki, harta kwanta Ammi tace "tashi Aisha".
ba musu ta tashi ta zauna, Ammi ta ce "anya wannan doctorn ne kuwa, menene alak'arku dashi da bazaki iya bacci ba sai kin dubashi, ni nakaraya da wannan jinyar gaskiya, dama k'attin mazane ke gadinki...
rufe bakin Ammi tayi ta ce "tun tasowata bansaba ɓoye miki komai ba Ammi, kada kizargi komai, wannan sunanshi Abdul, kuma shine AYS ɗina Ammi".

Ammi ta kama baki ta ce "a ina kika haɗu dashi, ke haukar taki tanananma ashe, sunan Ays har yanzu bai bar bakinki ba ohh ni Amina na banu".
Murmushi Aisha tayi ta ce "Ammi niɗinne ban warke ba, wlh Ammi dagaske nake miki, kuma banma nuna mishi na ganeshi ba".
Ganin Ammi tak'i yadda yasa ta kwashe labarin shi ta faɗa mata, harda rayuwarsu acan, sosai abun al'ajabin ya taɓa Ammi, ta ce "wannan wani ikon Allah ne babbah, shiyasa idan anga yaro ya mak'ale wa abu kamata yayi aduba abun, yanzu gashi auren naki baije ko ina ba, kuma wancan ɗin da ake gudu hanunshi kika faɗa, da wannan nakeso ki gane komai a rubuce yake, Allah yayi Faruq ba mijinki bane, don ya faɗa mana iya zamanku tare bai ɗaura miki iddah ba, kuma bincike ya nuna asiri akayi masa don a rabaku, wannan dalilin yasa ana ɗaura auren sa da Sadiya, banaso ko na misk'ala zarratin ki nuna damuwarki akan haka tunda asalima ba sonshi kikeyi ba, Allah yayi muku albarka gaba ɗaya yasa hakan yazamto alkairi a rayuwarku".
jiki a sanyaye Aisha ta ce "Ameen Ammi, amma waye yayi asirin to"?
kaɗa kai ammi tayi tace "baruwanki da sanin wannan, shiyasa kullum nake nusar daku ku rik'e addua, babu abunda yakaishi a duniya, kana naka mutane suna shiga rayuwarka ta inda bakayi tsammani ba, yanzune ma zama bai kamaki ba, duk inda aka samu tsantsan so sai ansamu tsantsan k'iyayya daga gefe, Allah yadaɗa karemun ku aduk inda kuke".
Kwantar da kanta tayi ajikin Ammi tace Ammi, gani nake kamar baniba, wai harda hauka nayifa Ammi".
"ba hauka kikayi ba, kinɗan samu matsala ne, kuma bagashi yazamomiki alkairiba, dama hakane ai, idan ancutar dakai sai kaga Allah ya musanya maka yazamo alkairi agareka matuk'ar ka rik'e addua".
basu runtsa ba har aka k'ira asuba sukayi Sallah suka shiga kitchen, farinciki takeji, rayuwar gidansu yafi mata na no'ina daɗi, donma babu Sadiya.

.
.
.
.
.
.

Zuwa yanzu cikin Unaisa harya fara fitowa, kullum cikin hijabi take, tazan duk ranarda aka gane saidai wata ba ita ba, duk k'ok'arinta cikin yak'i zubewa, Malam kuwa yaɗau son duniya ya ɗaurawa cikin amma bai taɓa nuna mata haka, kullum lallaɓata yakeyi akan cikin yayi kusan zubewa, aduk lokacinda yaga daman hutawarsa da ita saiya murɗa kanbunsa da kanta take zuwa, wani lokacin har kwanaki takeyi agidanshi yana abu ɗaya, sai ta dawo taci kukanta babu me rarrashinta, tayi danasani yafi a irga, ita yanzu Faruq ɗinma bashi gabanta, wannan k'addararren cikin yafi komai k'ona mata rai, wannan shine biyu babu.

Allah yasa mudace

Comments

Popular posts from this blog

Australian Visa Application information: Visa Types & Requirements

[Sunnah] What Muslim Should Observe On The Day Of Eid

Canada Immigration: How To Apply For Canada Permanent Resident Visa