NI AYS NAKE SO 32
💅💅💅
💋 *NI AYS NAKESO*💋
💅💅💅
Page 32
.
.
.
_WRITEN BY Princess Eshat Aysm_
.
.
In Dedication to *ABDULLAHI YAHYA SA'AD ZARIYA*
A.Y.S
.
.
.
*NASADAUK'AR DA WANNAN SHAFIN GABA D'AYANTA GA IYALAN MUHAMMAD MUHAMMAD MESAJE, HAR ABADA INA SONKU*.
.
.
*HALIMA S BICHIKI*
*HAJARA S BICHIKI*
MARYAM S BICHIKI
da dukkan *SABBASON FAMILY DVLPMNT GRUP*
_INA MATUK'AR ALFAHARI DAKU_
.
.
ESHAT AYSM NOVELS
*ESHAT HAUSA NOVELS*
BICHIKI FANS
_JINJINA TARE DA YABAWA GAREKU, HAR KULLUM ESHAT TANA TARE DAKU_
.
.
.
_SAMI BUNS_
da _Chip potatoes_
sukayi sai kunun gyaɗa wanda babu shinkafa aciki, Ammi sai farinciki takeyi ganin inda Aisha tak'ara kyau, wanke kwanikan da suka ɓata sukeyi, Hajara tace "Aunty yanzu keda wa kuka zauna acan, ko duk marasa lafiyar a ɗaki ɗaya kuke kamar na TH"?
kallon Ammi Aisha tayi kafin tace "kowa da nashi É—akin, idan macece sukan haÉ—ata mace wacce zata rik'a kula da ita, namiji kuma akan haÉ—ashi da É—an uwanshi namiji, asibitin badai tsaruwaba kam, da wata aka haÉ—ani sunanta Lidia, tanada kirki sosai, da zan taho saida tayi kuka".
Ajiyar zuciya Hajara ta sauk'e ta ce "jiya kamar mafarki nakeyi naji kinacewa wannan bak'on Ays ne".
Ammi ta ce "to sarkin gulma, zakiyi sauri ki gamane ko kuwa".
"haba Ammi, rabona da Aunty fa na manta, don nasan matsalarta shine gulma"?
Tashi Ammi tayi tace "zan gyara É—aki kuyi sauri ku kaiwa bak'on abinci".
Da murmushi suka rakata Hajara tana cewa "to" Ammi.
matsowa kusa da Aisha tayi ta ce "Aunty dagaske Ays ne, bayanin danaji kinayi wa Ammi ba mafarki bane".
Murmushi Aisha tayi, ta murÉ—a kunnenta ta ce "bazaki canzaba Hajara, dagaskene ba mafarki bane".
Tsalle Hajara tayi sannan ta fara taka rawa, sai juyi takeyi tana cewa "Allah mai iko ga Ays a gidanmu".
Abbah ta hango tayi saurin saita nutsuwarta, da mamaki a fuskarsa ya k'araso wajen, da sauri Aisha ta rungumeshi tana cemasa ina kwana Abbah, murmushi yayi me É—auke da farinciki yace "kin tashi lapiya Mamana".
gyaÉ—a mishi kai tayi, ya ce "kunje kun gaida bak'on"?
Hajara tayi caraf ta ce "yanzu zamuje".
Abbah ya ce "inafata dai lafiyarki law, naga kina rawa".
dariya dukansu sukayi, Jafar ne yazo da gudu ya rungume Aisha yana tambaya yaushe ta dawo, su Al'amin da Abdu ma sai murna sukeyi, cikin Farinciki suka gama komai suka juye a inda zasu juye, wanka suka shiga suna gamawa ta É—au riga da wandonta tasaka sannan tasa afterdrees asaman ta yafa É—ankwalin, trey ta É—auka ta jera komai akai tacewa Hajara biyoni da abincinnan mukai mishi.
kallo suka samu yanayi amma idonshi a lumshe da alamar baima san me akeyi a tv n ba, Sallamarsu ne yasa yaɗan ɗago, zuba mata ido yayi kamar bai taɓa ganinta ba, yanda yakeji a zuciyarsa har gani yake gaba ɗaya ta canza, Hajara sai mamakin irin kallon takeyi, har k'asa ta tsuguna ta gaisheshi sannan tajuya ta fita, ɗan nesa dashi Aisha ta zauna ta ce masa "ina kwana bak'o"?
murmushi yayi ya É—an susa kanshi ya ce "nine bak'on, zanramane, meyasa baki zo tunda asuba naganki ba"?
waro ido tayi ta ce "kaima faÉ—a kakeyi".
murmusawa yayi ya ce "tun barinki nan na matsu gari ya waye, kumafa duk zumuÉ—innan ganinki kawai nakeson yi, inaso zan tafi zaria da wurine, akwai muhimmin abunda zai kaini, da nasake kwana anan".
"uhm".
kawai tace tana murmushi, langaɓar dakai yayi yace "yunwa nakeji".
da hanzari ta mik'e ta zuzzuba mishi, jin k'amshin kunun saida yawunshi ya tsink'e, rabonshi da ganin kunu harya manta, ajiyewa tayi agabanshi ta ce "gashi".
ɓata rai yayi ya ce "me zanyi wai, kice dai kinaso na tafi da yunwa kawai".
zuba mishi ido tati ta ce "bakacin irin wannan ne".
kamo hanunta yayi, zata k'wace ya damk'e da k'arfi, ya ce "abaki zaki bani, ance bak'onka annabinka".
harara ta watsa masa ta ce "kaifa kacika fitina, yaushe zan iya baka abinci kana kato dakai".
dariyane ya kufce masa yace "haka kika ce ko, to na k'oshi".
yafaɗa tare da yin kalan tausayi, zunɓura baki tayi tana guna guni tafara bashi, ba kunya yayita ci, har wanda ta zuba ya k'are, ta ɗauko Sami buns ɗin tafara bashi, kaɗan yaci sannan tafara bashi kunun gyaɗar, saida yaji cikinshi yana neman fashewa yace mata ya k'oshi, ta ɓata rai tace "Allah sai ka shanye kunun".
haka tayi ta É—ura mishi, harda k'wallanshi ita kuma tana ta k'yalk'yale dariya, k'ak'arin amai taji yafara tayi saurin ajiyewa tafara bubbuga bayanshi, lumshe ido yayi yanajin masifeffen sonta inda yafara tasowa, É—an janyeta yayi gefe yace "zanyi wanka".
taɓe baki tayi tace "gacan bayi saika faɗamun".
da gudu tabar É—akin tana dariya, ganin irin kallon da yake mata, shikuma mamaki yakeyi wai yau shine tare da Esha a gidansu, tana fita ya runtse ido yanajin inda numfashin shi ya fara harbawa, ko yaya ya fara tunanin ta sai yaji bugun zuciya, dak'yar ya mik'e yayi wankan ya shirya yaÉ—au wayarshi da É—an jakarsa ya fita, da Jafar sukaci karo ya ce "zo abokina".
da sauri Jafar yazo ya ce "wajen Abbah zanje yakaini makaranta, kuma yau Abba zai sayamin keke nayi naÉ—aya a makaranta, malaminmu fa baya dukana yace inada k'okari, ranarma...
Abdu dage gefe yaja tsaki yace "faÉ—i ba'a tambayeka ba, harma ka iya k'arya, yaushe kayi na É—aya".
Murmushi Abdul yayi ya ce "Abokina baya k'arya, menene sunanshi".
yace JAFAR MUHAMMAD".
yajuya kan Abdu yace kaifa, yace "sunana ABDU".
shafa kanshi yayi yace ashe inada takwara, abokina kaini wajen Ammi mu gaisa, "Ammi tana falon Abbah saidai nakaika wajen".
murmushi yayi ya ce "muje ka kaini".
a mutunce suka gaisa da Ammi sannan suka gaisa da Abah, kallo É—aya Ammi tayi masa ta gamsu da kamalarsa, yayi mata 100%.
kanshi na sunkuye yacewa Abbah "ni zan wuce".
da fara'a Abbah yace kaci abinci kuwa".
murmushi yayi ya ce "naci Abbah".
godiya Abbah yayi masa sosai sannan ya ɗauko kuɗi masu tarin yawa ya bashi amma fir yak'i karɓa, haka suka barshi, yana fitowa yaja hanun Abdu da Jafar ya ce "Abbah baishirya ba muje nakaika makarantar, da murna jafar yabishi, saida suka ɗau hanya yacewa Abdu ata ina kasuwa yake"?.
kwatance yayi ta masa har suka isa, keke yasaima jafar da wasu tarkace sannan ya jibgawa su Abdu siyayya kamar ba kuÉ—i yake kashewa ba, makarata suka ajiye Jafar wanda yacika da murna da son Abdul aranshi, sannan yakai Abdul gida, suna gama fito da kayan ya mik'a masa wani letter yace kabaiwa Auntyn ka, daganan yaja motarsa yabara wuta da k'arfi yaÉ—au hanyar zaria.
Shiru Abbah yayi yana kallon Ammi can yace Amina nifa gani nake kamar nasan yaronnan amma nakasa tuna a ina naganshi".
Ajiyar zuciya Ammi tayi ta ce "dama inaso na tambayeka, ranarda aka É—aura auren Aisha kamar kace yaronnan Ays yazo harya suma muku".
Kafin yabada amsa Abdu yashigo da gudu yana murna, Abbah yaci "ungo naka, menene haka kuma"?
Shiya mantama lettern hanunshi ya mik'awa Abbah ya ce "muje kagani Abbah, wannan bak'onne ya tafi damu kasuwa harda keke yasaiwa Jafar".
Baki buÉ—e Abbah ya ce "to muje nagani".
Momi tace "kayi shirin sai su shigo dashi kasan su damaida k'arami babbah".
Shikam fita yayi a É—akin, Abbah ya warware takaddan da Abdu ya bashi yafara karantawa.
_SAK'ONE GAREKI MASOYIYA TA, NARASA TAYAYA ZANYI NA FAHIMTAR DAKE, AMMA DAI INASO KI SANI, LOKACINDA NARASAKI A FARKO NASHA WAHALA, YA ZAMTO BANA GANE KOWA DA KOMAI, KINSHIGA RAINA KIN ZAMTO TAMKAR FITILA A RAYUWATA, BANASO NASAKE RASAKI AISHA, KECE KAD'AI MAGANI NA, NATAFI ZARIA ZAN TURO IYAYENA AYI MAGANAR AURENMU, BAZAN SAKE YADDA SONKI YA ZAMTO CUTA A ZUCIYATA BA, BAZAN SAKE KUKAN RASHINKI BA AISHA TA_
*Abdullahi AYS, Nasan bazaki taɓa manta sunanba, sai na dawo Eshat*
ware ido Abbah yayi da ya gama karantawa, cillawa Momi takaddar yayi ya ce "ikon Allah, me nake gani haka"?
Murmushi Ammi tayi ta ce "atoh, kaga na huta da bayani, sai kasan nayi".
murmushi Abbah yayi ya ce "ai yanzu kome yace zan masa, balle irin soyayyar dayakeyi wa 'yata nima naji inasonshi".
Dariya kawai Ammi takeyi tana jinjina lamari na Allah.
Comments
Post a Comment