NI AYS NAKE SO 33

💅💅💅
      💋 *NI AYS NAKESO*💋
                 💅💅💅
Page 33

.

.

*🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀DON ALLAH KUYI HAK'URI BAZAN IYA ZAMA A WANI K'UNGIYA BA HAR INA AMFANI DASHI, PLXXXXXXXX*






.

.



_WRITEN BY Princess Eshat Aysm_

.

.

In Dedication to *ABDULLAHI YAHYA SA'AD ZARIYA*
A.Y.S







.




.

.





Lokacinda sak'on ya isa wajen Aisha tayi murna sosai haɗe da mamakin kodai ya gane itace.
Saboda tsaban gudun dayakeyi da wuri ya isa Zariya, lokacin aka shiga Sallar isha, tun daga tsayuwar motar tasa aka fara ihu AYS yazo, bai saurari kowa kamar yadda ya saba ba ya wuce wajen ummansa, da farinciki ta tare shi, ɗan rungumota yayi ya mata pick a goshi ya wuce masallaci.

A can suka haɗu da Abbahn shi, sun juma suna gaisawa kafin suka taho gida, Raliya tafi kowa murnar ganinshi, Umma ta haɗa musu abinci Tuwon gero miyar kuɓewa tasha manshanu, irin abincin da yafi so kenan amma baya samu tun komawarsa Abuja.
"Abdul ka shammace mu tahowa babu sanarwa".
Baban yafaɗa yana kai loma, Abdul ya susa kai yace "zuwana yanzu akwai dalili ne".
Kallon Umman nashi yayi kafin yace Umma albishir".
Kallonshi tayi ta ce "goro fari".
Yayi k'asa da murya yace "Na haɗu da Aisha...
Shiru yayi ganin duk sun tsareshi da ido, Umma ta ce "wai kai kanada lafiya kuwa, wace kuma bayan wa'inda sukayi Aure".
Kai yaɗan sake sosawa yana murmushi ya ce "Auren ta ya k'are".
Kama baki Umma tayi ta ce "kana nufin bazawara zaka aura, kabar wannan maganar, naɗau kasamo abun arzikine har kake wani ɓaɓatu".
Murmushi Baban nashi yayi ya ce




"mata dangin kuruciya, menene a auren bazawara, shekaru nawa muna fama dashi yanzu yazo da wannan maganar bazaki yimasa fatan alkairi ba".
Ajiyan zuciya ta sauk'e kafin tace "Allah yasanya alkairi".
Murmushi yayi ya ce "ameen".
Shi kam Abdul cin tuwonshi yakeyi don yasan mahaifinshi bashida matsala, itama Umman tanason shi bazata iya hanashi ba, farincikin dayake ciki ma bazai bari yagane abunda ake faɗa na aibu ba.
K'asa k'asa suka fara magana da Abbahn shi, ganin batajin me suke faɗa yasa ta mik'e ta tattara kwanukan tayi gaba abunta.
"a'a Baba don Allah kuje gobe kada na rasata".
"to naji, amma kasani matuk'ar aka samu matsala bazan kuma tura kowa ba, gaggawa ai aikin sheɗanne".
Murmushi yayi yace "idan kun nace bawani matsalar da za'a samu, wannan fa ba gaggawa bane, tsawon shekaru...
Fitowar Raliya ce tasa yayi shiru yana washe mata baki.





Zunɓura baki tayi ta ce "ko nemana bakayi ba".
Waro ido yayi ya ce "ba yanzu kika bar kusa dani ba".
Murmushi tayi ta ce "naɗau ɗoki yasa baka gane...
Binta yayi da gudu ta shige ɗaki tana masa dariya, murmushi kawai Baban nashi yayi ganin walwalan ɗanshi ya dawo.
Washegari tunda akayi Sallar Asuba ya tisa Baban da zancen tafiya, dole ba yanda ya iya yak'ira wansa da abokinsa yashaida musu zasuje neman aure wa Abdul a garin Bauchi, cikin k'ank'anin lokaci suka tafi cike da Farinciki, don dama kowa ya matsu yayi auren, da address ɗin daya basu sukayi




Amfani, sun samu kyakkyawan tarɓa, basu ɓata lokaciba suka shaida abunda ya kawosu, Abbah shima ya nuna musu yayi Farinciki da haka, cikin lokaci kaɗan suka shirya komai, a take suka bada sadaki.
5 na yamma suka ɗau hanyar komawa Zaria.
Tun tafiyarsu Abbah Ays yake cike da Farinciki, cikin hanzari yayi wanka ya tafi wajen abokin shi SAFWAN, Umma ta ce "lallai yau kadawo asalin Abdul ɗinka harda ziyara, rabonka da zuwa wajen wani tun lokacin da kazama likitannan".
Shidai murmushi kawai yayi y tafi, a hankali yake tuk'i shi kaɗai yanata murmushi, duk motsinshi Aisha yake yagani, fargabar sa ɗaya kada mahaifinta ya kwafsa, yayi murmushi a ranshi ya ce "wannan karan ko anhanani ita saina sace ta ne".
dai dai lokacin ya iso ma'aikatan su Safwan, kai tsaye office ɗinshi ya wuce, yana tsaka da aiki yaji knckn, ganin Abdul ne mamaki ya kamashi, lokaci guda ya mik'e ya taro shi, "wa nake gani kamar bokan turai, ba'a ganinka kwata2 saika manta damu haka akeyi, ɗazu su Nabil suke tambayarka ai".
nuna masa sit yayi kafin yaci gaba da surutun, Abdul yayi dariya ya ce "kaima ka kasa canzawa, magana kamar mace".
Safwan yayi dariya ya ce "kaima bazaka canza ba".
Su duka sukayi dariya, Safwan ya ce "kasan nayi aure ko, watanni huɗu kenan".
da mamaki Abdul ya ce "Aure kuma Safwan, shine ko labari babu, ko Raliya bata faɗa munba kuwa".
"to tayaya zakasani kaida baka zuwa, ko kazo baka neman mutane".
Abdul ya shafa suman kanshi ya ce "kasan aikin namu ba sauk'i, bamuda wani lokaci, yanzuma daliline ya kawoni, Aure nazo Abbah ya nemarmun".
Safwan ya ware ido cike da mamaki ya ce "Aure? ka hak'ura ka manta da aljanar taka da ta hanaka aurenne"?
Murmushi Abdul yayi ya ce "Ai bazan iya hak'ura ba, ita zan aura".
wani tsalle Safwan yayi kamar yaro ya ce "wai dagaske kakei, babu wanda baisan irin halinda kashiga lokacin da karasata ba, amma abokina garin yaya kuma zaka aure ta".
labari yabashi Safwan ya cika da mamakin ikon Allah, tsaban murnar daya tayashi haka ya jingine aiyu kanshi yaja Abdul suka
tafi wajen sauran abokanansu.



Sai dare su Abbah suka dawo, lokacin yana ɗakin Ummah suna hira jefi2, duk hankalinshi yana kan lokaci.
Sallamar Abbah yaji ya tashi da sauri ya zauna, Ummah ta ce "ohh ni nataɓa ganin irin wannan al'amarin kuwa, Allah ya kyauta".
Abbah da yake k'ok'arin shigowa yace "ameen".
Cikin susa kai Abdul yaɗan zame yamasa sannu da dawowa, ko zama  baiyi ba yace "Abbah andace kuwa".
Harara Jmma ta watsa masa tace "ai kabar mun miji ya huta kafin ko".
Murmushi yayi ya ce "Umma yafa riga ya tsufa, kiɓarshi yabani amsa saina baku waje".
Baki ta taɓe ta ce "neman aurenne yasa kamaida ni kakanka ko".
Abbah yace "je kayi baccinka angama komai, har sadakin mun basuk.
Ai bai san lokacinda ya rungume Abbah ba yana mishi godiya.
Kwanciya yayi amma babu alamar jin bacci a tare dashi, haushi ne ya kamashi da ya tuna Aisha bata da waya, wani dogon tsuka yayi yana zunɓura baki, k'iran Mansur ne ya shigo wayarsa, yana ɗagawa yace "shege haka akeyi bazaka k'irani ba, yanzu kana ina, Bauchi ko Zaria"?
Taɓe baki yayi kafin yace "shine saika zageni don ka k'irani, to ka kashe saina k'ira".
Dariya Mansur yayi ya ce "kana kan tsininka kenan, me yake k'asa ne, kasanfa bana iya jure aiki sosai yakamata kadawo".
Dariya Abdul yayi ya ce "idan ka ganni to anɗaura Aurena da Eshat, yau ɗinnan Abbah yakai Sadaki".
mamaki yakama Mansur "abdul bakada dama, har anzo wajen kenan, kace dai nafara shirin tahowa".
"gaskiya kafara shiri don yau zan haɗa komai akai kayan aure asa mana rana, zan rok'esu kada yafi kwana goma".
sunyi ta tsara inda zasu gudanar da bikin kafin sukayi Sallama yana cike da murna.

.
.
.

"Ammi wai gaskiyane iyayen Abdul sunzo gidannan"?
Aisha ta tambaya suna karyawa, Sallamar Sadiya ne ya katsesu, da gudu



Suka rungume juna, gaishe da Ammi ta farayi sannan tagaida Aisha, Hajara dake can gefe tana game da wayar Ammi ta gaisheta, Aisha sai binta da kallo takeyi, tayi wani masifar kyau kamar ancanzata, ita kanta Ammi ta yaba da irin murjewar da tayi, Aisha ta ce "Sadiya wai kinganki kuwa, kodai ba'a k'asarnan kuka zauna ba".




Sunkuyar dakai tayi tana dariya, ita kunyar Aishar takeji har cikin ranta, Aisha tayi dariya ta ce "ikon Allah, yau kuma kunyata kikeji kenan....
Faruq ne yashiga Falon Ammi da Sallamar sa, bayan sun gaisa Aisha tace "sannunku 'yan k'annena".
Har Ammi saida tayi dariya, Faruq kunya kamar ya nitse, murmusawa kawai yakeyi, Aisha taci gaba dacewa "kunga na huta da zuwa yi muku faɗa a matsayina na babba, tunda gaku a gabana, da farko kaga kai namijine, yakamata kazamto me hak'uri dakai zuciya nesa, sannan zato yana jawo mummunan zunubi, duk abunda zata maka kayi hanzarin faɗa mata koda faɗane hakan zaisa ku fahimci juna sosai, ɗaukar maganar mutane akan matarka duk ba naka bane, kazamto namiji dai dayasan fari da bak'i".
"ke kuma kece mace, a k'ark'ashinsa kike, shine shugabanki har gaban *ABADAN*_SAFIYYA HUGUMA_.
idan kikayi biyayya kika rik'e mahaifiyarsa tamkar taki zakiji daɗin rayuwarki, ki zamto me kauda kai kedai naki biyayya kawai, yi nayi bari na bari, Aljannarki tana k'ark'ashin k'afarshi, ki kuyi hak'uri ba komai zaiyi miki ki ɓata raiba, Allah yayi muku albarka".
Dariyar Abbah ne yasasu juyawa dukansu, Ammi ma murmushi fal ranta, Faruq kam mamaki yasashi sake baki yana kallonta ko k'yaftawa bayayi, shikam har gobe baisan ranarda zata daina burgeshi ba, gashi yanaji yanagani tazama Auntynsa, wani huci ya furzar sannan yayi murmushi ya ce "mungode Aunty".
wani irin k'ara Sadiya ta saki jin cikinta yana murɗawa, da sauri Faruq yarik'ota du ya gama ruɗewa yana tambayarta lafiya, kafin tayi magana ta kece da amai ajikinsa, saida tagama ya rungumeta sosai yana shafa bayanta, shi yamanta da mutanen da suke kanta ma, kowa ya ruɗe yana tinanin lafiya kuwa, Aisha ne ta ɗago ta a hankali tace mata sannu, sannan ta ɗago tafin hannunta ta ɗan matsa sannan ta zuba ma hanun ido, can tace "Congratilation k'anina Faruq, matarka tana ɗauke da juna biyu".
sai a sannan suka tuna abunda ta karanta, Abbah ya k'arasa shigowa, Hajara ta taso suka rufu suna murna.

Comments

Popular posts from this blog

Australian Visa Application information: Visa Types & Requirements

[Sunnah] What Muslim Should Observe On The Day Of Eid

Canada Immigration: How To Apply For Canada Permanent Resident Visa