NI AYS NAKE SO 34
💅💅💅
💋 *NI AYS NAKESO*💋
💅💅💅
Page 34
.
.
.
_WRITEN BY Princess Eshat Aysm_
.
.
In Dedication to *ABDULLAHI YAHYA SA'AD ZARIYA*
A.Y.S
.
.
.
Ranar wuni sukayi suna murnar ganin juna ga murnar cikin da Sadiya tasamu, sai yanzu Aisha ta tuna mafarkinda takeyi a baya, koda yaushe idan ta biyo faruq zatasa shi a rami Sadiya ce da wasu yara suke tareshi, wannan ya nuna shine uban 'ya'yanta, a hankali ta share hawayen da ya sauk'o mata batasan na menene ba.
Kallon Sadiya tayi ta ce "bani wayar hannunki na gani".
Da sauri ta mik'a mata, tashi tayi tsam ta nufi ɗaki, jakarta ta ɗauko ta fito da wani card, numbobin jiki ta jera kamar zata k'ira ta fasa, text ta tura.
_Ni takace har abada, farinciki na fatan ka isa gida lafiya._
Ko minti ɗaya batayi da turawa ba ya k'ira, jin sallamar ta yayi har tsakiyan kanshi, wani lumshe ido yayi kafin yace "wayar waye kika samu"?
Shiru tayi naɗan dak'ik'u sannan ta ce "yaya su Ummana"?
Taɓe baki yayi ya ce "Umma tana gaisheki, amma fa sai kinbani amsata".
murmushi tayi meɗan sauti tace "wayar Sadiya ce".
Dariya yayi dagaji najin daɗine, "naji daɗi, bannaso naji kince wayar wani ne".
Murmushi tayi tana jinjina kishi irin nashi, mezai kaita karɓar wayar wani kuma oho.
"kinyi shiru Aisha, kuma baki tayani farinciki Sadakina yana kanki ba, kuma baki cemun komai akan lettern dana baki ranarda zan tafi ba".
ajiyar zauciya ta sauke ta ce "Ina taya mijina murnar fara jin k'amshin angonci, tuzuron da ya girma ba aure...
Wani lumshe ido yayi yakasa buɗewa, "Aisha ina tausaya miki ranar da nakamaki, ɗan yaro dani kice tuzuru".
Dariya ta k'yalk'yale dashi ta ce "wani tausayi kuma, ko kamanta ni naji komai".
runtse ido yayi ya ce "Aisha kidaina tunamun kinyi aure plx banason ji, baki da damuwa akan haka ko"?
Murmushi tayi ta ce "banida wani damuwa sai tsantsan shauk'i, damuwar me zanyi ina tare da abunda yake sakani nishaɗi, nasan zanyi alfahari da kai a gidan aure na".
cikin sanyin murya ya ce "Aisha, wani irin so kike mun, kinajin zuciyanki yana bugawa idan muna taɗi"?
sassanyar ajiyan zuciya tayi takasa magana, kiran sunanta yasakeyi da wani irin murya dayasa tsikan jikinta tashi, ta lumshe ido ta ce "yaushe zan ganka, kazo gobe".
murmushi yayi Yace "Angama Uwargida".
Zunɓura baki tayi kamar yana ganin ta ta ce "kana nufin zakamun amarya ne"?
dariya yayi ya ce "ehmana ko kina nufin zan zauna dake ke kaɗaine"?
kuka tasakar masa datasa yagama ruɗewa, "wallahi wasa nake miki, ni ke kaɗaice Uwargida kuma amaryata, har Abada zanrik'e ki, Dake kaɗai zanyi alfahari har k'arshen rayuwata".
tsagaita kukan tayi tana sauraronshi, sai lumshe ido takeyi.
saida ya tabbatar ta fara dariya sukayi sallama, ɗagowa tayi taga Sadiya tsaye akanta fuskarta cike da mamaki.
"Aunty wai wa kika samune".
murmushi tayi ta ce Ays mana".
ɗan zaro ido tayi tace "wai dama lavarin da Ammi tabani gaskiyane".
kamo hanunta tayi ta zauna kusa da ita ta ce "gaskiya ne Sadiya, ina alfahari da haka".
da haka tayi ta shan cikin Sadiya ko zata gane tana cikin matsala amma babu alamar haka, daɗi taji sosai.
wunin ranar haka sukayi suna tsokanarta, motsi kaɗan sai suce *NI AYS NAKESO*
Saida Ammi ta ɓata rai suka daina.
Sai dare Faruq yazo yaɗauki Sadiya, kamar kada ta tafi.
Washe gari kuwa da rana tana kwance a ɗaki kamar me bacci taji hayaniya, lek'a window tayi tana tunanin wasu irin bak'i sukayi haka, waro ido tayi ganin ana shigo da akwatina, da sauri ta koma ta kwanta tana dariya, watau da gaske duk abunda Ays yafaɗa mata ba k'arya bane, dariya tashiga yi tana murna, burinta ya kusa cika a rayuwa.
.
.
.
.
"malam katayani ganin cikin Unaisa dayake ta girma, anya laulayin da tayi bana ciki bane"?.
Shiru yayi zuciyarshi na tafarfasa, dama ya daɗe yana ayyana hakan kuma abokanshi sun faɗa mishi, wani k'aton katako ya ɗauko ya nufi kanta, wani ihu ta kurma tana Baba kayimun rai wallahi ba iskanci nayi nasamu ba, ko kallonta baiyu ba ya hau jibgarta, ihu take tana cewa "Mama ki ceceni".
ɗan share hawaye maman tayi tace "meyasa haka Unaisa, an taɓa samun ciki ba'ayi komaiba ne"?
Dak'yar take magana saboda raɗaɗin duka, dak'yar uban ya saketa, a wahalce ta ce "don Allah Baba katausayamun, Kareema ce takaini wajen wani wai don na auri Faruq, shine yamun cikin".
Wani shak'a da uban yayi matane yasa tayi shiru, janta yayi har waje yace "idan kika kuskura kika shigomun gida ALLAH YA ISAH".
Comments
Post a Comment