NI AYS NAKE SO 35
💅💅💅
💋 *NI AYS NAKESO*💋
💅💅💅
Page 35
.
.
.
_WRITEN BY Princess Eshat Aysm_
.
..
in dedication to *ABDULLAHI YAHYA SA'AD ZARIA*
.
.
.
*MASU TAMBAYATA KO AYS MIJINANE, "AYS BA MIJINA BANE, BUT TSAWON SHEKARU 5 MUNA TARE, BAMU TAB'A HAD'UWA BA, A TAK'AICEMA SHINE MUTUM NA FARKO DANA FARA SO A RAYUWATA".*
_ba kuma baizo bane kawai haɗuwar ne ta gagara._
.
.
MASU NEMAN CONTACT NASHI DON ALLAH KUYI HAK'URI🤦♀👌🙏🏻
.
.
*Masu nunamun k'auna wlh inasonku kamar raina, Allah ya haɗa fuskokinmu koda a Aljannah ne, lov u all.*
.
.
.
Wasa wasa nesa yanata matsowa kusa, ankawo kayan lefe daya zarce tunanin mutane, kowa yagani sai yayi san barka, ita kanta Aysha saida ta razana da kayan, an tsayar da ranar Aure Sati biyu.
farincikin da mutanen biyu suke ciki baya misaltuwa, tako wani fanni shirye shiryen biki akeyi, gaba ɗaya garin Zaria ko ina kataka sai ansanar dakai maganar Auren *AYS* da *ESHAT.*
Ranar TALATA ta kasance saura kwana uku a ɗaura Aure, wani yadine a jikin shi me ɗan karen shek'i kalar maroon, fuskanshi yayi sayau saboda ɗan ramar dayayi, agogo yake ɗaurawa a hannunshi k'irar Fugh, Ummanshi tana zaune daga gefe, "Abdul kana nufin tun yau zaku tafi Auren"?
Murmushi yayi me cike da annuri ya ce "Umma ba mun gama maganaba, akwai abubuwan daza'ayi a can kuma kinga dole angawaye suna can".
Ya faɗa yana kanne ido, murmushi tayi ta ce "sai yaushe kuma kudawo".
Suman kanshi ya baza yana dariya haɗe da sunkuyawa, taɓe baki Umma tayi ta ce "uhh ni 'yasu".
Murmushi yayi ya ce "Nifa daga yau bazaki ganni ba sai tare da matata".
Salati tayi "zama zakaje kayi a gidan sarakan ko me"?
"a'a tare fa da abokaina zamu tafi, kinga sunata jirana Umma, kimun addua".
Addua tafara kwarara masa kamar ba gobe, cike da farinciki ya tafi wajenda abokansa suke jiranshi, duk wani abunda zasu buk'ata sun tafi dashi, sun kai su 8 kai kace ɗaura auren zasuje.
sai dare suka isa garin Bauchi, kai tsaye Hotel suka kama ɗakuna uku, saida suka gama komai suka ci abinci suka zauna huta gajiya.
Abdul daya gaji lik'is ya kwanta tare da lumshe ido, Aisha kawai yakeson gani ko hankalinshi zai kwanta, juyi yaketa yi FAISAL ya ce "mutumin wai duk gajiyane"?
Iska ya furzar ya ce "Aisha nakeson gani, amma banajin zan iya tuk'i nagaji".
Shiru Faisal yayi kafin ya ce "muje na kaika mana".
Zuba mishi ido yayi kamar bazai tashi ba, "muje to, ganinta kawai zanyi mudawo bacci nakeji sosai".
Shidai Faisal baice komaiba ya ɗau key yafita, Safwan ne kawai ya iya cemusu a dawo lafiya duk da baisan ina zasu je ba.
A hankali yakejan motar, Abdul idonshi yana lumshe, ji yake kamar ma anyi auren daya ganshi a Bauchi.
Dayake bikin akeyi gidan cike da mutane, bakace dare yayi bama, hatta k'ofar gidan 'yanmata ne suketa shawagi, harɗe hannayenshi yayi ya ce "Faisal bazan iya shiga cikin mutanennan ba, mu koma kawai".
Harararsa Faisal yayi ya ce "kafa rainamun hankali Abdul, infito a gajiye kace bazakaje ba, dole ciki zaka shigane"?
Tsaki yaja ya ci gaba da cewa "kajirani infito da ita".
shidai binshi yayi da kallo harya fita a motar, sannan ya sauk'e ajiyan zuciya, wata farar yarinya yagani bazata wuce 14 ba, da sauri ya isa gabanta ganin zata shiga gidan, Murmushi yayi mata ya ce "ɗan tsaya ki taimaka mun, Amarya nake ki k'iramun".
Da sauri ta kalleshi tace "Aunty Aishar"?
Gyaɗa mata kai yayi alamar Eh".
"to ince mata waye".
murmushi yayi ya ce "kice mata mijinta ke magana".
Zaro ido tayi ta ce "kaine Ays ɗin".
Bai bata amsa ba ta runtuma da gudu tayi ciki tana cewa Aunty Ays yazo".
wata tsohuwa ce tace "kunfara shiririrantan naku ko".
rantsuwa ta shigayi tana cewa wlh shine.
Aisha tana ɗaki ana shafa mata dilke saida gabanta ya faɗi.
Yana tsaye a jikin Motar Faisal yana masa dariya wai ashe har yara sun san Aisha da Ays, guɗa suka fara ji tun daga soron gidan, basuyi mamaki ba sai ganin tsofin da suka fito suna guɗa sun nufosu, yarinyar da Faisal ya tura tana gaba, da sauri Abdul ya buɗe mota zai shiga Faisal ya fizgoshi, "ina zakaje ka barni bacin kai akewa guɗa".
Muryar tsuhowar sukaji tana cewa "ina Ays ɗin namu a cikinku".
Dariya Faisal yayi yanuna Abdul, aikuwa suka rufu akanshi suna fesa mishi turare, tsawon mintina kafin tsohuwar ta ce "tunda kazaɓi tsohuwa kabarni ai saika zo ka ganta don bata futa".
shidai don sun ja shine kawai amma da gudu zaiyi, shikam Faisal dariya yayi tayi don yasan mutumin nashi baya son hargowa.
Tunda suka shiga dashi gidan ya runtume da ihu, ɗakin Ammi suka Fara kaishi suka gaisa a mutunce, sai a sannan yaɗan samu sa'ida kamar kada ya fita, jin tsohuwar ta sake jan hanunshi saida yaji kamar ya kurma ihu, suna barin ɗakin Ammi tafito ta ce "kada wani ya sake cika mata kunne".
Sai a lokacin kowa ya nutsu, ita Ammi ta ɗauka waje kaka tayi da Ays shiyasa bata sauraresu ba ta koma ciki, itakam kaka kai tsaye ɗakin da akeyiwa Aisha Dilke ta turashi, "kuna gaisawa ka fito don dani za'ayi aurennan".
Murmushi kawai yayi ya kaɗa kai ganin tabar wajen, a ranshi yace "ita kuma wacece oho".
murɗa k'ofar ɗakin yayi a hankali kamar me tsoron ganin wani abu, ganin falon wayam yasa ya nufi ɗakin, angama shafa mata kenan ana murza mata na fuskarta ya shiga, K'amshinsa kawai taji k'irjinta ya fara dukan uku uku, kaddai shigowa yayi... Bata ankare tunanin ba taji me diken tana cewa kaɗan jira a wanke mata, wani ihu Aisha tafasa dayasa me dilken tayi waje da gudu, tasowa tayi idonta a rufe tana cewa "waye ya shigo Bagana"?.
Jin tayi karo da mutum yasa tasake fasa ihu, rungumota jikinsa yayi a hankali ya ce "ihun me kikeyi, kada kibari haukarki ta dawo sai anɗaura mana aure fa".
Dukanshi ta shiga yi tana cewa "yafita".
binta kawai yakeyi da kallo, towel ne kawai a jikinta k'arami shima, tunani ya farayi "to menene ake shafa mata haka".
jin tanata dukanshi yasa ya rik'e hanun ya ce "Aisha, kidaina fa kada ya shiga miki ido, muje na wanke miki".
wani tsalle ta buga tana neman hanyar guduwa, dariya yayi ya ce "menene wannan ake shafa miki".
me dilken ne taɗan lek'o ta ce "ciwon ya lafa ne"?
Haushine ya kama Aisha ta ce "haba bagana, ni kizo ki wankemun".
Saketa Abdul yayi yana dariya acan k'asan zuciyarsa, neman waje yayi ya zauna yana binta da kallo kamar maye, Bagana ta kamata tace muje na wanke miki.
fuskar ta fara wanke mata, Aisha ta ɗago da sauri ta ce "don Allah meyasa kuka bar mutuminnan ya shigo".
Bagana tayi k'asa da murya ta ce "Allah yasoki kin taɓa Aure da kinsha fitina daga ganinshi".
waro ido Aisha tayi tace "wani irin fitina Bagana".
harararta tayi ta ce "kinfini sani tunda ke ba budurwa bace".
shiru Aisha tayi tana tunanin me take nufi.
yana zaune idonshi yana kan toilet ɗin da suka shiga, santala santalan cinyoyin ta yake gani a idonshi, har wani lumshe ido yakeyi, bai taɓa jin fellings irin nayauba tunda yake a rayuwarshi, kasala ne yasauk'a mishi, shi sam ya manta da wani Faisal, yananan zaune Bagana ta fito daga bayin ta fita, kamar ya tashi ya shiga bayin haka yakeji, ko minti ɗaya batayi ba tadawo tauke da dogon riga da hijabi, bayin ta shige takaiwa Aisha,
Rigar kawai ta zura tasaka hijabin, ta dubi Bagana ta ce "kunyar ganinshi nakeyi".
Bagana ta taɓe baki tace "kefa kinfiye iya shege, wani irin kunya kuma".
Kallo ta bita dashi kamin ta ce "a hakafa yaganni ko kaya babu".
Ta faɗa kamar zatayi kuka, Bagana tace "ke ko felek'en zaurawan baki iyaba kuma hardasu jin kunya, yau aka fara ganinki".
Shiru Aisha tayi kafin tayi narai narai da ido ta ce "nifa auren danayi ko k'afata bana tsammanin ya taɓa gani balle yaganni a haka".
Kama baki Bagana tayi ta ce "dagaske kikeyi".
"Allah dagaskene Bagana".
Jinjina kai tayi ta ce "gara da kika faɗamun, zan san abunda zanyi akai".
Kafin tayi magana tajata tace "yana jiranki".
saida suka fito yaga bala'in canzawar da tayi, fuskarta har wani k'yalk'yali yakeyi, a hankali ta nemi waje a gefenshi ta zauna ta juya fuska, Bagana ta wucesu tayi tafiyarta, murmushi yayi ganin yanda ta juya fuska, "Bakiyi murnar ganina ba kenan".
Ya faɗa yana lek'a fuskarta, ɓoye fuskar tayi a hijabi ta ce "shine zaka shigo ka ganni".
"menene idan naganki, gobe saura 2 fa".
Dukda baya ganinta saida ta dara, ta kuma kasa magana.
A hankali ya ce "ganinki nazoyi amma kinata ɓoye fuska, a gajiye nake".
Sai lokacin ta ɗago ta ce "yaya hanya".
Murmushi yayi ya ce "ni zan tafi, gobe kada ku ɓata mana lokaci, nasan kinga komai a jikin katin, ina fata kuɗin da naturo zai isa".
Kai ta ɗaga masa, yaja hancin ya ce "magana zakiyi".
"eh".
tace masa tana murmushi, zuba mata ido, kamar me raɗa ya ce "har yanzu gani nake kamar mafarki nakeyi Aisha".
Murmushi kawai tayi masa, "to kifaɗamun menene aka shafa miki".
hancinshi ta ɗan ja tace "kafiye gulma".
baisan lokacin da yayi dariya ba.
Da sauri ya mik'e ya ce "muje ku gaisa da Faisal, yana waje".
zunɓuro baki tayi ta ce "ni katafi kawai".
kallon mitsitsin bakinta yayi, wani yawu ya haɗiye yace "wasu tsofi ɗazu sun samun ciwon kai".
dariya tayi ta ce Kaka ce da 'kannanta da k'awayenta, kullum basuda taɗi saina lissafin ranar zuwanka, tunda Abbah ya basu labarinka suka samu suna me daɗi".
wani murmushi yayi, "Abbah dakanshi"?
murmushin ta me tsumashi ta watsa masa dayasa kanshi ya fara kuncewa, rungumota yayi da sauri yana sauk'e numfashi, duk yadda taso ta k'wace haka ta kasa, saida yagama numfashinsa ya sake ta, pickn goshin ta yayi sannan yayi mata a kumatu.
ganin idonta a lumshe yasa yayi murmushi ya ce "na tafi, ki kula dakanki, inason k'amshinnan"
Murmushi tayi masa kafin ya fic
Tunda suka ɗau hanya Faisal yake kallonshi, yana mamakin irin k'amshin da yake tashi a jikinshi me shegen k'amshi da daɗi, ga wani taɓare taɓare da ya mammane ajikin sa, shidai kasa hak'ura yayi ya ce "Abdul menene ke k'amshi a jikinka ne, kaga yanda ka ɓata kayanka kuwa".
lumshe ido yayi yana murmushi, tunowa dayayi dilkan jikin Aisha ne yaɓatashi, girgiza kai kawai Faisal yayi.
Comments
Post a Comment