NI AYS NAKE SO 36
💅💅💅
💋 *NI AYS NAKESO*💋
💅💅💅
Page 36
.
.
.
_WRITEN BY Princess Eshat Aysm_
.
.
In Dedication to *ABDULLAHI YAHYA SA'AD ZARIYA*
A.Y.S
.
Na sadauk'ar da wannan shafin gareku
*MARYAM ƁBINTU*
*ZUBY ONE*
*UMMIY KISHIYATA*😜
*SADIYA BICHIKI*
*HALEERMA*
* *AEESHA*
*UMMEE*
*HALEEMAR*
*TEEMAR*
*NAFISA LAWAL..*
Washh kunada yawa, duk ina sane daku.
.
.
.
irin budirin da akeyi a bikin faɗanshi ɓata lokacine, Ranar Laraba akayi Dinner da daddare a SOGIJI HOTEL, Alhamis akayi Doctors Day, wanda ya halarci dubban likitoci daga garurruka da dama, duk wani kyautar da za'a bayar sai kaga serchet na Peracitamol aciki, dukkan wanda yake wajen zakaga farin kayane ajikinsa, bikin ya k'ayatar Amarya da k'awayenta sunyi kyau har sun gaji, ko ina kaga Amarya sai kaga Abdul a mak'ale da ita, yazamo kamar wani ɗan jagora saboda tsaro.
Ranar Juma'a da Safe 'yan Zariya suka iso,
Bayan Sallar Juma'a aka Ɗɗaura Auren Abdullahi Yahya Sa'ad Zaria da Aishat Muhammad Mesaje, auren da ya halarci dubban mutane, Aure me cike da ɗunbin tarihi.
Koda aka ɗaura saida zuciyar Faruq tayi kusan bugawa don sai a lokacin ya gane AYS ɗin da Unaisa tafaɗa masa shine Abdul ɗin, bin wajenda Abdul yake yayi da kallo yana sanye cikin Farin shadda wanda yasha aiki ba k'arya, sai gaisawa da mutane yakeyi fuskarsa a sake, kallo ɗaya zakayi masa kagane irin farincikin dayake ciki, duk da yaji wani iri a ranshi amma yaji Abdul ɗin ya burgeshi sosai, ko ba'a tambaya ba yasan zai rik'e Aisha sosai, cikin Sanyin jiki ya k'arasa kusa dashi suka gaisa, kallo ɗaya Abdul yayi masa ya ganesa, juya kai yayi da sauri zai bar wajen, saboda shi Allah yayishi da masifar kishin tsiya, haushi yakeji idan yatuna wanine ya fara auren Aisha bashi ba.
Murmushi kawai Faruq yayi ya nufi motar sa yabar wajen, duk bak'in da sukazo Maza a ranar suka koma, mata kuma suka zauna sai dare su tafi da Amarya.
Tunda aka ɗaura auren Aisha taketa kuka, anyi rarrashin har angaji, Abbah da kanshi yazo ya tafi da ita ɗakinshi.
har yazaunar da ita bata daina kuka ba, kamar yarinya harda su hawaye, Shi kanshi Abbah k'arfin hali yakeyi saboda zata musu nisa.
"mamana kukan menene haka yak'i k'arewa, masu kukan ma kaɗan sukeyi ai".
Kamar ya tunzura tasake sake sabon kukan, a hankali tace "Abbah nafasa auren".
Waro ido yayi ya ce "kinfasa kuma, saida aka ɗaura, kinsan dai zaɓinkine ba nawaba".
"Abbah Allah nafasa bazan iya komawa wani gari da zama ba".
tafaɗa tana jan majina, Abu kamar Wasa babu inda Abbah baiyi ba tak'i tayi shiru, ita lallai saidai idan zai ajiyeta a Bauchi, nasiha babu wanda baiyi ba amma tak'i shiru, dabara yayi mata yace "to kiyi shiru, yanzu kici abincinnan kinga anfara k'iran Sallar magriba, idan nayi sallah zan faɗa wa shi Abdul ɗin sai yabarki anan ko".
gyaɗa mishi kai tayi, yayi murmushi yace "yauwa mamana Allah ya miki albarka".
murmushi tayi ta ce "Ameen Abbahna".
Ammi tana ganin fitarshi ta shiga da sauri, matsawa tayi daf da ita tace "taso muje kiyi wanka kada lokaci ya k'ure".
ɗan zunɓura baki tayi kafin ta mik'e suka fita, Ammi da kanta tayi mata wanka da ruwan MIHA, ruwane me ɗan karen k'amshi yana ɗauke da wasu sinadari, tanayi tana mata faɗa me ɗauke da Nasiha, suna fitowa ta haɗata da Bagana tace ta shiryata, kwalliya ta zauna tayi mata irin dai wanda akewa Amare, sannan tasaka material yadin bashida nauyi sai laushi, ta kanannaɗa mata ɗauri me kaman goggoro, tasha kyau basai na rubuta irin kyawun ba, kowa yasan irin kyawun da amare sukeyi musamman wanda sukasha gyara, mayafi ta yafa mata me ɗan girma sannan tace taje tayi Sallah tunda tayi alwala, zunɓura baki tayi ta ce "Aɗakin Abbah zanyi".
Jakarta ta mik'a mata tace "kedai kinfiye fitina wallahi, sai ki koma ɗakin da zama ai".
Baki ta turo zata fara kuka Bagana tayi saurin cewa "kirufamun asiri kiyi shiru da kukannan naki, nazauna na ɓata lokaci zaki fara sana'ar taki".
Janta tayi tana cewa "badai ɗakin Abbah bane gaki gashi".
Ammi tana ganin fitarsu tayi murmushi aranta tana dariyar fitina irin ta 'yarta.
A bakin k'ofa sukaci karo da kaka, sai ɓaɓatu takeyi, wai anɓoye amarya bata ganta ba, ga bak'i sunfara cewa zasu tafi da ita yanzu, Sadiya da Hajara ne sukayi saurin fitowa acikin mutane suka fara tsokanar Kaka, "kaka angon yana jiranki a waje wai ke ake jira".
Washe baki tayi ta nufi hanyar waje su kuma sukasa dariya, hanun Aisha sukaja suka shige ɗakin Abbah.
Ana idar da Sallah Abbah yace a nemo masa Abdul, jerin motoci ne sunfi 30 a k'ofar gidan, da k'yar aka samoshi a cikin dandazon abokanshi.
Gaban Abbah yaje ya tsuguna har k'asa, Abbah ya ce "kashiga gidan ta k'ofar baya, Aisha tanason magana dakai tana ɗakina, nasan tanata faman kuka ka saurareta, idan akwai abunda zakayi akai kafaɗamun".
russunawa yayi cikin Ladabi yace "To Abbah".
binshi Abbah yayi da kallo harya ɓace, har ranshi yakejin daɗi Allah yabashi surakai nagari.
ta baya yashiga kamar yadda ya faɗa mishi, babu wanda yaganshi har ya isa babban Falon Abbahn, tundaga k'ofa yakejin dariyar Hajara harda k'yak'yatawa, a hankali yasa kai yashiga, da sauri Aisha ta mik'e tana kallonshi, shima ita yake kallo cike da shauk'i dashi kaɗai yasan yanda yakeji, Murmushi tasakar mishi kafin ta zauna, cikin takunnan nasa ya k'arasa gabanta ya tsuguna, hanunta ya rik'o kamar me raɗa ya ce "meyasa kika zubarda hawaye bana kusa"?
Hajara da sadiya suka kalli juna suka murmusa, Bagana harda gyaran murya.
sunkuyar dakai tayi cike da kunya ta ɓoye cikin mayafinta, Murmushi yayi yace "muje ki rakani".
da sauri Hajara tace "ina kuma muda zamu tafi a yanzu".
Maganarta ya kwaikwaya yana dariya saboda k'aramin muryarta..
a hankali Aisha ta fara rera musu kuka, da mamaki ya ce "meyafaru"?
daɗa cusa fuska tayi a mayafin tace "ni babu inda zanje anan zan zauna".
murmushi yayi ya ce "da auren nawa".
kai ta ɗaga mishi, ya ce "Sadiya ta ce "Aunty nanfa kike ɗaga mana hankali ke *AYS KIKESO*.
Amma yanzu zakice anan zaki zauna".
hanu yasa a baki shhhhhh alamar Sadiya tayi shiru.
tashi yayi tareda alama wa Hajara tazo taji, a hankali yace "kice wa Ammi anfara gaba da amarya, saiku taho daga baya".
jinjina kai tayi ta nufi wajen Ammi.
Sadiya da Bagana da sauri suka bi bayan Hajara suma, mayafin yaɗan janye har lokacin kuka takeyi mara sauti, ya lek'a fuskarta ya ce "muje wajen Abbah yana jiranki a waje".
Ai kuwa ta mik'e da sauri, jakarta ya ɗaka ya rik'e sannan ya kama hannunta da ɗayan hanun, ganin tarin motoci saida ta razana, sun ɗanyi tafiya me nisa suka isa wajen wani mota, duk tafi motocin wajen shek'i, kallonshi tayi ta ce "ina Abbahn".
Hancinta yaja yace "kishiga mana, ko kinaso mushiga cikin mutane a haka aganemun kyawunki ne".
Shiga tayi harda bismillanta kafin ta zauna, sannan shima ya zagaya ya shiga, yana tada motar taji gabanta yafara dukan uku2, innalillahi kawai take furtawa, a hankali ya ratsa motocin yabi ta gefe yabar wajen.
Yanashan kwana k'iran Mansur ya shigo "Abdul lafiya naga ka fita da mota, kasan yanzu zamu tafi".
Dariya yayi ya ce "mufa mun tafi, ku taho kawai".
Mansur cikin Dariya ya ce "kai iskancin naka gababa yakeyi, kace kasace Amarya kawai".
Dariya yayi ya kashe wayar, yanaji sunata dariya.
Aisha data gama ganeshi ta fashe da kuka, wuta yayi wa motar sosai yaɗau hanya, iya k'arfin gudun da yakeyi iya k'arfin kukanta.
Wani iri yakeji, kallonta yayi ya ce "meyasa kika fiye yawan kuka Aisha, ko kinmanta nine fa AYS ɗinki, banason kukan nan naki shiyasa na ɗaukoki".
harara ta watsa mishi taci gaba da kukanta, Murmushi yayi yace "shikenan, zan mayar dake, dama wannan k'amshin naki yafara mun illah".
Shiru tayi tana kallonshi, ya gyaɗa kai ya ce "bada wasaba, zaiyi wahala na iya kaiwa bansamu matsalaba".
Tsayar da motar yayi a gefen hanya ya ce "Aisha me yasa ke kaɗai kike irin wannan k'amshin, ranarfa ko bacci banyi ba".
tsuru tayi da ido, ita tunaninta ma yatafi wata duniyar, wai dagaske Abdul yazama mijinta, kodai mafarkine, shikenan tadaina ganin su Ammi, batasan lokacinda kukan ya sake dawowa ba.
Matsawa kusa da ita yayi yabar sit ɗinshi, fuskar tata ya tallafo yana ganin hawayen, shiru tayi ta daina kukan, ta runtse ido tace "mu tafi na daina kukan".
Lumshe ido yayi kafin ya buɗesu "ina zamu tafi, kinsan bazan tafi dake kina kuka ba".
Wani kallo ta watsa mishi ta ce "ai nayi shiru".
Kissin bakinta yayi ya ce "banyadda ba, buɗe bakinki nagani".
Buɗewa tayi harda 'yar murmushin ta, da sauri ya jefa harcensa cikin bakin ya rufe yafara juyashi, wani dogon numfashi yaja da k'arfi dayasa numfashin ta tafiya naɗan lokaci, tureshi ta farayi amma ko gezau beyiba, bakinta yakesha sosai har wani ɓari yakeyi, bai taɓa Tsintan kanshi a wannan yanayin ba, haka itama duk yagama ruɗata, saida yagaji ya saketa yana maida numfashi, jingina bayanshi yayi yana binta da kallo, a hankali ya furta "Bazan iya tuk'iba Aisha".
juya fuskanta tayi ta gefe".
Wayarshi ya ciro ya k'ira Safwan ya tambayeshi sun tasone, Safwan yace wasu dai sunyi gaba, yace "yauwa, zaka ganmu a hanya ka tsaya kajamu bazan iya tuk'i ba".
"meyafaru, lafiya dai ko, kunyi nisane"?
Lumshe ido yayi ya ce bamuyi nisa ba, amma kuyi sauri.
Comments
Post a Comment