NI AYS NAKE SO 38
💅💅💅
💋 *NI AYS NAKESO*💋
💅💅💅
Page 38
.
.
.
_WRITEN BY Princess Eshat Aysm_
.
.
In Dedication to *ABDULLAHI YAHYA SA'AD ZARIYA*
A.Y.S
.
.
.
*BANSAN DA WANI IRIN KALMA ZANYI AMFANI WAJEN NUNA GODIYATA BA, AMMA NAJI DAD'I MATUK'A DA IRIN K'AUNAR DA KUKEMUN, DUK WANDA YAMUN MAGANA YAGA BAN AMSA BA DON ALLAH YAYI HAK'URI, WLH SAK'ONNIN NE SUNYI YAWA DUK INA SONKU WALLAHI💋
.
.
Kunya yagama kama Aisha kamar ta zauna a bayin haka takeji, da k'yar tasamu ta zauna a cikin ruwan zafin, harda hawaye.
'yan uwanta da suke ɗaya ɓarin duk suka fito jin hayaniya da Asuba, Bagana ta kama baki tana mamakin irin wannan al'ada, Sadiya tayi dariya tace "su Aunty manya".
Hajara tace "uhm wai me aka matane"?
Buge bakin Bagana tayi sannan taja hanun Sadiya sukayi gaba, ɗakin da suka tabbatar Aisha tana ciki suka shiga, kalle kalle suka hau yi suna santin ɗakin, Sadiya tace "inagafa wanka takeyi".
Bagana bata saurareta ba ta nufi bayin, a hankali ta baɗe, hangota tayi a cikin bath idonta a lumshe, Da ɗan k'arfi tace "Idan kin gama kizo".
Firgit ta buɗe ido, lokacin har Bagana tabar wajen, tsaki tayi tana tunanin dawa zata iya haɗa ido irin wannan abun kunyar, Abdul ya cuceta.
Suna zaune Umma tashigo da flask na ruwan zafi da gwangwamayen kayan tea, turus tayi ta tsaya kallonsu, da k'yar Bagana tayi murmushi ta ce "kayanta muka kawo mata wanda zata saka".
Murmushi Umma tayi ta ce "to ai shikenan, idan ta fito ku tabbatar tasha da zafinshi".
To sukace kafin ta sake fita.
Bagana tace "uhh wannan abun kunyar har ina, ni dama daganinshi nasan bazai saurara mata ba".
Dariya kawai Sadiya tayi, a cikin ranta tana mamakin ashe da gaske Faruq bai mata komai ba.
Can Umma tasake shigowa ɗauke da flask na ferfesun naman rago dayasha kayan yaji, baki buɗe tace "har yanzu bata shigoba"?
Murmushi kawai Bagana tayi, Umma ta ce "kiyi maza ki mata magana ta fito kada sanyi ya kamata, garin damuna gashi sanyi ya sauk'a".
"to" kawai Bagana tace.
Umma tana fita tasake lek'a bayin, "Aisha kifito haka".
K'ara ta saki dayasa Bagana shiga da sauri, zanin yana ɗaure a jikinta da alama fitowa takeson yi, tsaban shagwaɓa yasa takasa daurewa, har lokacin zafin wajen takeji, hanunta Bagana ta kamo tace "ki tako a hankali, abu yasamu sarkin raki, kuna da aiki, shi ba hak'uri ke raki, inbanda haka menene na wani nok'e k'afa".
Ko k'ala Aisha batace ba sai hawaye, ita kaɗai tasan azaban da takesha.
Da k'yar tasamu tasha tea ɗin ta ɗan taɓa ferfesun sannan tayi Sallah, shigowar Abdul ne yasa gabanta yayi mummunar faɗuwa, kusa da sallayar yaje ya zauna, su Sadiya suna gaisheshi duk hankalinshi yana kan Aisha, tana Sallama tasake tada Sallah, yi kawai takeyi ta kasa idarwa, tun yana kallon ta har yafara irga raka'a nawa takeyi, ɗan murmushi yayi yashafa suman kanshi, tayi sujjadar raka'a ta goma yayi saurin mirgino da ita a hankali ta faɗa jikinshi, kuka tafarayi k'asa k'asa tana dukanshi a k'irji, kallon fuskanta kawai yakeyi ganin sun kunbura sunyi ja, rungumeta yayi sosai yanajin soyayyarta yana shiga jikinshi, a hankali yace "Sadiya ku ɗauko mata kayanta".
Kamar jira suke suka mik'e da sauri.
Yana ganin fitansu ya ce "kiyi hak'uri babe, wajen da zafi ko"?
Kuka tasakar mishi, ya ɗago da kanta yace "kiyi shiru, idan nasake yanzu zaki daina jin zafi".
Tureshi tafarayi ya rik'eta gam, kallon flask ɗin yayi yace "kinci wani abu"?
Ta gyaɗa masa kai, ya ce "ok bari naji ko kinci".
laluɓan cikin yayi ya fara shafawa, cikin a shamule kamar ba komai a ciki, jin irin shafan dayakeyi ne yasa ta fara kuka, shikam har ya fara sauk'e numfashi, lumshe ido yayi a hankali yace "zan baki magani, zaki warke kinji".
Shigowar Baganane yasashi mik'ewa, kayan ya karɓa sannan ya ɗagata kamar jaririya yayi bayin da ita, wani ruwan yasake haɗata meɗan zafi, da yak'ushi da cizo yasamu ya kunce zanin ya sakata a ciki, k'ara ta sake da k'arfi tana k'ank'ameshi, tausayinta yasa shima ya shige cikin ruwan yana share mata hawayen, da sauri Umma tashiga ɗakin, kallon Bagana tayi tace "k'aran menene haka, ina Aishar".
da hanu ta nuna mata, taɓe baki Umma tayi ta ce "Abdul ya shigo ko, ɗan nema mara kunya".
saida ya gasata sosai sannan yabata maganin dayazo dashi, dak'yar tasha, saida ya ɗura abakinshi sannan ya haɗe bakin da nata ya zuba mata, a haka tasha maganin, mai yashafa mata yayi mata kwalliya sannan ya shiryata fes, Atamface me kalan sararin samaniya, wajen ɗaurin zanine suka fafata, ita dama bawai ta iya bane, shima bai iya ba, haka ya ɗaura mata sannan ya ɗauko ta suka fito, Bagana tayi dariya ta ce "ikon Allah sai kallo, ana samun haka wai ko".
shafa kanshi yayi yana dariya, cikin lallaɓawa yace "ki kwanta kiyi bacci, anjuma zamu tafi".
kauda kai tayi, wani irin kunya takeji, zuwa lokacin ta daina jin zafin wajen sai raɗaɗi kaɗan, hut kiss ya manna mata a baki kafin yafita.
Bagana tayi saurin k'arasawa kusa da ita "tashi kisha wannan maganin".
yamutsa fuska tayi ta juya fuska, Bagana ta harareta ta ce "karfa kimun iskanci, ke zaki sake shan azaba idan baki sha ba".
Fuskar ta a haɗe ta karɓa ta shanye, wani abune a ɗan k'aramin kwalba, yana sauk'ar da santsi wanda ko yaya yayi da futuna bazata gaji ba.
Kafin wani lokaci ɗakin ya cika da mutane 'yan ganin Amarya, danginta kuma suka fara aikin jere a part ɗin ta, babban wajene sosai aka keɓe mata a cikin gidan, komai nata da aka saka kalan pink ne, waje ya tsaro saidai fatan Allah yabada zaman lafiya, kallo ɗaya zakayi wa sashin kasan 'yar gatace.
Zuwa la'asar 'yan kawo amarya suka ɗau hanyar komawa Bauchi, akabar Hajara da Bagana(k'anwar Ammi)
Sai mata 2, Sadiya kam ta koma saboda batajin daɗi donma cikin nata bamai laulayi bane.
washe gari da sassafe suka ɗau hanyar Abuja.
*UNAISA*
Har mutanen anguwa saida suka tausaya mata sukayi wa Babanta magana amma fir yace bazai zauna da mazinaciya ba, haka ta mik'e ta tafi gidan Kareema amma abun mamaki wai an saketa kwana uku kenan, koda taje gidansu a kulle ta sameshi, cikin kuka ta nufi gidan Malamin nasu, ga wahalan ciki haka ta tafi da k'afa, tun daga hanya aka cemata yayi tafiya kuma zai kwana 2 kafin yadawo, haka taci kukan ta tashi tadawo cikin gari, nadama tayishi yafi sau 1000, ta tsimewa bokaye yafi a irga, lallai boka bai isa yabiya buk'ata ba tunda gashi tagani yasata a garari, babu wan babu k'anin.
Wanke wanke da shara ta nema ta farayi, da zummar idan tasamu wani abu sai ta tafi Nigeria ta nemi gafarar Faruq da Aisha.
Comments
Post a Comment