NI AYS NAKE SO 39

💅💅💅
      💋 *NI AYS NAKESO*💋
                 💅💅💅
Page 39

.


.

.



_WRITEN BY Princess Eshat Aysm_

.

.

In Dedication to *ABDULLAHI YAHYA SA'AD ZARIYA*
A.Y.S







.

Wannan shafin na zallan masoyana ne, faɗan kalmar godiya bazai faɗuba a rubuce, sai nace ina masifar yinku a raina.
*'YAR GIDAN NA'IKKE*
ALLAH YA K'ARA MIKI BASIRA YASA KIFI HAKA, ALLAH YA RAYA MANA YARANMU, INA SONKI IRIN SOSAI D'INNAN, ALLAH YABAR ZUMUNCI DA SO DA K'AUNA, NAGODE SOSAI DA SADAUK'ARMUN DA LITTAFI GUDA, I HEART U SO MUCH💋

"UMMIEY AHMAD (UMMIEY AYSM) KISHIYATA, HHH INASONKI AMMAFA DAGANI BABU K'ARI, *AYS* MIJON MACE D'AYANE".
LOLX

.

*ZAN RAYU DAKU HAR ABADA MASOYANA, KUNADA YAWA DANA LISSAFOKU, ILYSM@ALL*

.
.
.
.






Fentin gidan gaba ɗayanta Ash ne  sai pop maroon, tyls ɗin k'asan kuwa me ruwan Hadari, duk abubuwan da akayi amfani dashi a cikin gidan kalanshi Ash ne, Abdul yayi mata bazata da yawa, Allah ya barsu tare har gaban Abadan.

Tym ta kalla taga 6 saura, da hanzari ta mik'e tashige ɗaki don gidan yafara bata tsoro, kayan jikin ta tacire ta ɗaura towel tashiga wanka, saida ta haɗa duk abunda tasan zai sakata nishaɗi acikin ruwan kafin ta shiga, durza jikinta tayi sosai kamar bazata daina wankan ba, ɗan motsi taji ta tashi da gudu ta fara lek'a ɗakin, daɗa buɗe bayin tayi yanda zataji daɗin daina jin tsoron, a haka ta koma taci gaba da wankanta, gefen zuciyarta yana ayyanata mata irin kulawar da zata baiwa sabon angonta, kuma masoyinta har a lahira, ɗan murmushi tayi ta lumshe ido tana tunano fuskanshi.
Tundaga bakin k'ofar falon farko yafara watsa mata k'ira, "my Eshat!"
harya shige ɗakin bai daina ba, k'amshin ɗakin yadaki hancinshi ya lumshe ido yana tasbihi, a hankali ya buɗe idon ya sauk'a akan toilet ɗin, da alamun wanka takeyi amma kuma k'ofar a wangale, k'arasawa yayi cikin sanɗa ya lek'a, idonta yana lumshe sai facal2 da ruwa takeyi kamar yarinya, murmushi ya sauk'a akan fuskan shi, ya shafa gefen fuskanshi yana tanɗe baki, a hankali ya isa ciki, har lokacin idonta na kulle, dai dai kunnenta yaje yace "kada mura ta kamamun ke".
firgit ta buɗe ido zata fara ihu ya tsareta da idanuwanshi, da sauri ta sunkuyar da kai tafara kukan shagwaɓa, "ni kafuta nasa kaya tukun".
hancin ta yaja yace "kin barmun a buɗe dole nabaiwa idanuwana abinci, waya faɗa miki ana wanka k'ofa a buɗe".
Zunɓura baki tayi tana kare k'irjin ta dataga yana bi da kallo, sauran jikin ta duk kunfa ya rufe, matsawa daf da ita yayi harda tsugunawa a wajen, yasa hanu ya fara kaɗe kunfar yana dariya, idonshi yana kanta, sai ɓata rai takeyi, cikin wani irin murya ya ce "nashigo muyi wankan"?



Mik'ewa tayi zata gudu, duk tagama ruɗewa kunya kamar ta nitse, yayi saurin kama hanunta, kuka ta sakar masa ta ruk'unk'umeshi tana ɓoye jikin ta a jikinshi, binta da kallo yayi da lumsassun idanuwanshi, tuni ya gama fita a burki, daɗa rik'eta yayi murya a shak'e yace "baki ɗauraye jikin ba".
ko ɗagowa batayi ba, sai kuka take zuba mishi, kukanma data tsumashi yakeyi, a hankali yajanye ta yamayar da ita bayanshi, ya rik'eta da hanu ɗaya, sannan yatari ruwa meɗan ɗumi, tanaji tana gani ya mayar da ita ciki, jikin nata ya ɗauraye kafin ya cirota a ciki, towel ya ɗauka ya ɗaura mata yana wani shu'umin murmushi, harara ta watsa masa ta ce "nima saina rama".
Tayi maganar kamar zatayi kuka, gira ya ɗaga mata yana dariya, "me zaki rama"?
Kallonshi tashiga yi, ba k'aramin kyau yayi mata ba, tsohon soyayyar ta motsa, kallan dayake narkar dashi taci gaba dayi, ko k'yafta ido batayi, a hankali ya rungumeta kaɗan, lafewa tayi a jikinshi tana sauk'e ajiyan zuciya, tsananin so da k'auna ne yafara zagayesu, sun ɗau lokaci a haka sannan ta zame a hankali, Alwala tayi tabar cikin bayin, ya bita da kallo cike da so, wanka shima yayi sannan yayi alwala, mai kawai suka shafa suka tada Sallah, yana gaba tana gefen bayanshi ta dama.

Ba k'aramin jumawa sukayi suna Addua ba, tarin godiyar da sukeyiwa Allah yafi yawa a ciki, Allah ya rabasu da sharrin mutane da Aljanu kuma, Sallar isha suka gabatar sannan sukayi Nafila raka'a 2.
Shi dakanshi ya bata abinci taci sosai, sannan shima yaci, ganin take taken bacci a tare da ita ysa ya waro ido ya ce "me kikeji wai, bake ba bacci sai kin gama amarci ai".
Dariya tayi ta ce "haka kaga akeyi ko, me akeyi dayafi baccin"?
Bakinshi yakai kan nata ya lashi leɓenta yace "baki sani ba"?
Gyaɗa mishi kai tayi cike da fargaba, yayi murmushi yace "yanzu zanmiki kiji".
Yafaɗa yana k'asa da murya, nok'e kafaɗa tayi ta ce "koma menene banaso, bacci zanyi ni".
Ta faɗa tana zunɓura baki, kallon k'aramin bakin ta yayi ya ce "Baki faɗamunba".
"mene"?
Ta tambaya tana kallonshi, ya susa kai yace "soyayyata a zuciyar ki".
Rufe fuska tayi da hannayenta ta ce "ai bana sonka"!
ware ido yayi, yakamota ya ce "sake faɗa naji".
da murmushi ta ce "ni bana sonka".
Murmushi yayi ya ce "Allah sai kince *NI AYS NAKESO*
zatayi magana yayi saurin cafko leɓenta, a hankali yafara zagayeshi da harcen shi, cike da maitan ta ya ce "Faɗamun Aisha, Soyayyata zaki faɗamun a ranki yanda kikejina, ki faɗamun wani irin so kikewa *AYS"*


Kallonshi takeyi sosai, lokaci guda ta fara hawaye, a ruɗe yace "ya isa haka, kada ki fara kuka plz Babe, a shimfiɗa ta kaɗai nakeso naga hawayenki ba'a karin banza ba, ko baki faɗa ba nasan kina sona, soyayyar da bazan taɓa mantashi ba, amma yaya akayi kika zamto budurwa alhalin kinyi aure har na tsawon shekaru"?

kwantar da kanta tayi a jikinshi, ta ce "kabarni nayi kuka Abdul, farincikine fal raina, ina mamakin irin k'aunar dana daɗe ina maka, nasoka tun sanda nafara ganin sunanka, naci gaba da sonka a lokacinda na tabbatar na rasaka,
wani k'arin mamakin shine, tun lokacin danaga photon Dr Abdul narasa nutsuwata, ko bacci tare nakeyi dashi a jikina, ranarda naganka a gabana, kuma na gane kaine Ays ɗina, nayi farincikin da ban taɓa tunanin anayinshi ba a rayuwata, a ranar na tabbatar lallai asalin so a zuciya da jini yake ba'a fuska ko a fatan baki ba, Allah yayi mu ne kawai don mukasance tare, ina fatan kada shaiɗan yayi mana illa a rayuwarmu, Ina sonka  Abdul, Ina Sonka kamar raina, ina sonka fiyeda yadda zaka gani a idona, Insha Allahu tare zamu rayu, kuma tare zamu mutu".

Comments

Popular posts from this blog

Australian Visa Application information: Visa Types & Requirements

[Sunnah] What Muslim Should Observe On The Day Of Eid

Canada Immigration: How To Apply For Canada Permanent Resident Visa