NI AYS NAKESO 27

������
      �� *NI AYS NAKESO*��
                 ������
Page 27

.


.

.



_WRITEN BY Princess Eshat Aysm_

.

.

In Dedication to *ABDULLAHI YAHYA SA'AD ZARIYA*
A.Y.S







.




.

*INUWA MUHAMMAD (HAASKE SHADOW)*

_Naga sak'onka thouth in gmail, nagode sosai_

.

.

.





Wasa2 Dr Abdul yayi nisa a soyayyar Aisha duk tunaninshi ɗan zaman da sukayi ne yasa suka shak'u, tana ɗebe masa kewar Raliya k'anwarsa, musamman wajen neman faɗanta, kullum cikin lissafin kwanakin da yarage mata yakeyi, babu wani hujjar dazaisa ta ci gaba da zama a wajen, tana zaune a gabanshi tanashan maganin da yabata, sai yamutsa fuska takeyi, idonshi nakanta yana murmushi k'asa2, wayarshi ne tahau ruri ya ɗauka, Dr Mansur yagani, yayi dariya ya ɗaga, kafin yayi magana Dr Mansur ya ce "kazo kaɗaukeni mun iso".
Kashe wayar kawai yayi, mik'ewa yayi tare da faɗin "kina gama sha ki tabbatar kinci abinci".
ɓata rai tayi ta ce "zanbika".
"ba nisa zanyi ba".
Kuka zata farayi ya ce "ke kuma, kuka?
taso mutafi".
Da sauri ta tashi suka tafi.
Dr Mansur yana zaune ata gefe ya hango motar Abdul, da hanzari ya mik'e ya nufi wajen, da tsananin farinciki Abdul ya fita suka rungume juna, Abdul ya ce "ina shirin bada cikiyarka kenan".
Duka Mansur ya kai mishi ya ce "na daɗe da dawowa ina zaria".
Murmushi sukayi suka nufi motar, mamaki ne ya kama Mansur ganin Aisha, ya sake baki ya ce "wacece wannan yau a motarka".
Haɗe rai Abdul yayi ya ce "idon matambayi ne".
Taɓe baki yayi ya ce "kai kasani".
Dole baya yashiga yana mamaki, ɗan satan kallon Mansur tayi ta mudubi tayi masa sannu da dawowa, a dak'ile ya amsa ya kauda kai, hakan ya tabbatar masa da ta warke, tunani yafara yi, wani irin abune a tsak'aninsu haka, yasan Abdul baya yadda yayi ko magana da wata a wajen balle shiga wajenda yake, Addu'a yafarayi a ranshi Allah yasa ba soyayya suka fara ba.
Bawanda yayi magana har suka isa gidan nasu, ganin sunfita yasa itama tasa k'afa zata fita, sunkuyawa yayi dai dai kunnenta ya ce "ina zakije, gidan da babu mata a ciki".
murmushi tayi kawai ta koma ta zauna, shima murmushin yayi yaja hancinta sukayi dariya, Mansur ya taɓe baki yashige da sauri, bin bayanshi yayi yana ɗaga mata hanu, ajiyar zuciya ta sauk'e me k'arfi, "Allah kabani Abdul yazamto abokin rayuwata ta har abada".
ta faɗa a ranta.

Suna shiga Mansur ya ce "yaushe kazama haka"?
cikin ko inkula ya ce "rayuwace ta canza, zan kaita, kasameni acan, idan ka huta saimu gaisa".
Mansur yayi shek'ek'e ya ce "wai kana nufin ta warkene".
ɗaga mishi kai yayi ya ce "ina tunanin haka".
"shine saboda iskanci kake yawo da ita".
runtse ido yayi ya ce "nifa banson tambaya, cewa tayi zata biyo ni".
da mamaki Mansur yace "dama tasaba binka kenan"?
tsaki yayi ya ce "ko kotu naje iya tambayoyin da zasuyi kenan".



Binshi da harara Mansur yayi ya ce "mutum kamar mutum amma...
Shiru yayi ganin ya fita bai saurareshi ba.

Wani irin faɗuwar gaba yaji ganin murfin motar a buɗe kuma bata ciki, lek'a ko ina yayi babu alamarta, da sauri ya koma ciki yana k'walawa Mansur k'ira, har yafara wanka yasa riga ya fito, a kiɗime shima yashiga tambayar sa lafiya yake masa irin wannan k'ira,
"Banganta ba".
abunda ya iya faɗa kenan yana zare ido, Dr Mansur yayi tsaki ya ce "shine kabi ka futa a hankalinka".
wani kallo ya watsa masa ya ce "idan ta ɓata wa za'a kama"?
shiru yayi yanufi hanyar futa, da sauri ya bishi a baya, duba gidan suka shigayi amma babu ko alamunta, shi kanshi Mansur har wani zufa yakeyi, da sauri ya nufi Gate ɗin gidan, a zaune a jikin bishiyar kwakwan dake k'ofar gidan ya hangota, wani farin mutum dogo yana  zaune kusa da ita, da gani tanajin daɗin maganar tasa, fuskarta cike da murmushi tana kaɗa wayarsa a hannun ta, wani malolon bak'inciki ne ya tsikari Abdul, idanuwanshi har wani canza kala sukayi lokaci guda, Mansur kam tsayawa yayi yana dariya, ya ce "tasa hankalinmu ya tashi a banza, kaɗauke ta kutafi tun kafin taja mana magana".
ko kallonshi Abdul baiyi ba ya nufeta, wani irin zafi zuciyarshi takeyi, da iya k'arfinshi ya fizgo ta, wayar dake hannunta ya karɓa ya kwaɗa da k'asa, cikin tsantsan isa ya ce "wani irin iskanci ne daga zuwa waje zaki jajiɓo wani".
mamaki ya kamata, bawai maganar ne yabata mamaki ba, yanda ya canzane ya bata mamaki, sunkuyar dakai tayi zata fara kuka mutumin dayayi mutuwar tsaye ya k'araso, a hankali ya ce "bai kamata...
wani uban harara ya watsa masa dayasa yaja bakinsa yayi shiru, jawota yayi da k'arfi yayi cikin gidan da ita, har lokacin zuciyarshi bai daina tafasa ba, jefata cikin motar yayi yazaga zai shiga Mansur yayi saurin tareshi, cikin kunnensa yayi masa magana "nasanka da kishi akan abunda kakeso, ina umurtarka dakayi a hankali akan 'yar mutane kada kayi mata illah, tamkar amana take a wajenka, watak'ilma zurfincikin ka bai bari kafaɗa mata kana sonta ba amma kake nuna irin wannan kishin, kayi a hankali".
Binshi da kallo Abdul yayi harya shige, dawo da kallonsa kan Aisha yayi lokacin har tafara kukannan nata, kauda kai yayi yashiga ya tada motar, maganar Mansur  sai yawo yake masa a kunne.
ya lumshe da ido yana kallonta ta gefen ido, zuciyarshi ce tafara faɗa mishi zafinda kaji a zuciyarka lallai shine SO, Runtse ido yayi yafara girgiza kai, wata zuciyar ta ce "tunda ka rasa ESHA bazaka sake son wata ba".




Haka yayi ta tunani, kukanta ne yadawo dashi, tsaida motar yayi ya kifa kanshi, wani sabon kukan tasake ɓarkewa dashi, a hankali ya k'ira sunan ta, jin tak'i ta amsa yace "zamuyi ta zama anan har sai kinyi shiru, kukannan naki sam banason ji, kiyi hak'uri ki daina".




Kamar k'ara mata yayi, Ɗwani iri yakeji har cikin kanshi, hannunshi yasa ya kamo nata batareda ya ɗago ba, wani irin abune ya tsikaresu, zata janye hanun yasake matsewa, cikin kuka ta ce kasakeni ba kyau fa".
Murmushi ne ya suɓuce mishi ya ce "to kidaina kukan".
Dainawa tayi tana sauk'e ajiyar zuciya, ya ce "meyasa kika zauna da wani har kina masa dariya"?
Zunɓuro bakin tayi


Ta ce "cemun yayi Dr Abdul mutumin kirki ne shine naji daɗi".
ɗagowa yayi yana kallonta, wani gefen yaɗanji kunya meyasa ma yayi haka, ya ce "meyasa kikaji daɗi"?
Kallonshi tayi kafin ta ce "haka kawai".
Kamar me raɗa yace "Zaki iya rayuwa dani Aisha"?
Waro ido tayi tana mamaki, shi kanshi baisan yayi maganarba, "na rayu dakai tayaya".
Tayi tambayar yayinda ta tsareshi da ido, suman kanshi ya baza ya ce "kiyi hak'uri, mantawa nayi".
Batace mishi komai ba ta kauda kai, "bazan taɓa nuna maka nice Aisharka ba, dole nasan zaka soni, saboda don ni akayi ka, nima saboda kai akayi ni, a duk inda numfashin mu ya haɗu sai munji alama ajikinmu".
Ita kaɗai take magana a ranta, kallonshi tashiga yi tana murmushi, murmushin nata ba k'aramin tsumashi yakeyi ba, a kasalance yaja motar suka tafi.


.
.
.

Momi tayi matuk'ar farinciki jin cewa Abbah ya ce yanemi Sadiya, ta jinjina wa Abba sosai da karamci irin nashi, ita kanta saida taja Allah ya isa mawanda yashiga tsak'aninshi da Aisha, k'warin gwiwa ta bashi akan ko bayason Sadiya ya tilastawa ranshi sonta, bazaiyiyu ya watsa musu k'asa a gwiwa ba.

Shidai harga Allah baya wani sonta, amma a hankali suka fara sabawa, tun tana ganin rashin dacewar abun har tazo tafara sonshi, dama suna sonshi tun a dama, soyayyah suka fara sosai da yasanya iyayensu samun kwanciyar hankali, tunaninsu ɗaya Aisha, Ammi tana tsoron Aisha tadawo ta tadda wannan abun, saidai sun tanadi uzurin da zasu ɗaurata akai.

Aure nufine na Allah, kana naka Allah yana nashi, matar mutum tabbas itace kabarinsa.

Sati biyu akasa bikin Faruq da Sadiya.

Fatan Allah yakaimu lokacin.

Comments

Popular posts from this blog

Australian Visa Application information: Visa Types & Requirements

[Sunnah] What Muslim Should Observe On The Day Of Eid

Canada Immigration: How To Apply For Canada Permanent Resident Visa