BENZEMA 3

📨📨📨📨📨📨📨📨📨📨
*BENZEMA*
📨📨📨📨📨📨📨📨📨📨
.
.
writen by *PRINCESS ESHAT AYSM*
(AISHA BICHIKI)
.
.
DEDICATED TO
*SADIQ ABDULLAHI BENZEMA*
3
.
.



gmail: Eshataysm@gmail.com
📨
07014612958 for cmmnt.
Eshataysm.tk
my blog😍
.
.
page3
Bayan sun tashi daga makaranta kamar kullum Saif yana bi ya karɓi aikan Mom ɗinshi a gidan k'awarta, a ɗan nesa da gidan yayi prkn, shima Sadiq fitowa yayi yana ɗan kalle kalle, kamar daga sama yaji ana cewa, "kanbu, kema kinsan Innah wlh naira babu sai tayi k'asa k'asa dani".
"uhmm saiki hak'ura tunda hakane".
Juyawa yayi a hankali, yarinyar nan ne me tallen doya, fuskar nan tata tasha buɗa jaka kamar zata dandali, wai duk acikin kwalliyar fita tallene.
ɗayar ce ta zungureta tace "wannan fa mutumin jiyannan ne, muje kiyi masa godiya".
Yanajin haka ya haɗe rai ya shige cikin mota, har jikin motar suka k'arasa amma glass ɗin a zuge take ba halin jinsu ma.
Juyawa sukayi da niyyar idan sun sake ganinshi zasu mishi godiya, Rai a ɓace Saif yazo ya sameshi, ya girgiza kai yace "badai yauma kaga wani abunba"?
Murmushi yayi yace "banga komai ba, ina tunanin hanyar dazanyi na hana yarannan talle ne, tausayi suke bani".
Sai yayi murmushi yace "kayi tunanin rayuwarka kafin".
Baice komaiba ya buɗe murfin motar ya fita, ai kuwa da sauri ta taso ta ce "yallaɓoi nagode sosai, jiya Innah har abinci me yawa tabani naci ganin kuɗin tallen ya k'aru".
Nurmushi yayi gamida shafa sajen shi, yaciro ɗari biyar ɗin da Ummi ta bashi dazai fito ya mik'a mata, baki ta ɓuɗe tace "yallaɓoi doya za'a baka"?
Ya kaɗa kai yace "ɗazo naji kina faɗawa k'awarki akwai abunda kikeson siya, ki saya dashi".
tsalle ta hauyi tana murna haɗida godiya, shikam barin wajen yayi ya shige mota, Saif dake kallonsu yayi dariya yace "Abokina kana wutafa".
dariya yayi yace "inajin daɗi naga nasharewa wani hawaye, inajin daɗi naga wani cikin farinciki ta sanadina, inajin daɗi idan natuna cewa Sadeeq bashi da wani buri daya wuce yazama wani a duniya mutane suji daɗin rayuwa, nasan Ummi na zatayi matuk'ar alfahari da haka, hakan zai tabbatar mata da lallai nayi gadon mahaifina".
cikin murmushi Saif yace "Allah ya ida nufi, ina tare dakai har kacika wannan kyakkyawan burin naka, saidai meyasa aduk lokacinda zan baka abu sai kak'i karɓa, Umminka kaɗai ke baka ka karɓa meyasa".
juya kai yayi yace "daina wannan maganar, mu wuce kawai".
Saif ya taɓe baki yaja motar suka tafi, yau gidan su Saif suka fara bi, lokacin k'arfe 3 dai dai, daga fitowarsu Khadija ta nufosu da gudu, jikin Sadeeq ta faɗa tana dariya, "Uncle nayi fushi tun jiya banganka ba".
tafaɗa tana zunɓura baki, ya kama kunnenshi yace "afwan little, ko za'amun hukunci kafin a huce"?
kaɗa kai tayi tace "na huce".
ya ɗagata sama suna dariya, murmushi kaɗai Saif yayi yawuce yana cewa "shi kaɗai kika gani ai".
da sauri ta dira tabi bayanshi tana cewa Yaya "sorry".
yatsa ya ɗaga mata ya wuce abunshi, me aikinsu ne tashiga hidima dasu, Saif yashige ɗaki sashinsa yace "idan kagama ina ciki".
taɓe baki Sadeeq yayi yace "naji".
shikam tsaban surutun khadija baisan sanda yayi ta cin abincin ba, duk wani taɗin nata akan iyayen tane, sai kwasan dariya yakeyi Mom ta fito, cikin wani shiga ta alfarma hannunta rik'e da keys, k'amshi kuwa sai tashi yakeyi, ɗauke kai tayi zata wuce ya russuna ya gaisheta, a hankali ta amsa sannan taɗan zubawa Khadeeja ido tace "ki kula da gida".
kai kawai khadija ta ɗaga mata, tana fita Sadeeq ya kama kunnen ta ya murɗa yace "haka kike amsa magana wa mahaifiyarki".
cikin jin zafi ta ce "nadaina Uncle".
ya haɗe rai yace "mahaifiyarki tafi kowa muhimmanci a rayuwarki, girmane da ita, aduk lokacin da kika
ga tana miki magana nutsuwa zakiyi koda maganar batada muhimmanci, kuma ba'a kaɗa musu kai to zaki ce, kuma bakice mata Allah yadawo da ita lafiya ba".
jikinta yayi sanyi tace "Zan gyara Uncle, Insha Allah".
dariya yayi ya mik'e yace "good, zanyi wanka na wuce gidanmu".
"kai Uncle kabari sai dare".
ya waro ido yace "Ummiey na fa, tananan tanason ganina".
murmushi tayi tace "kai kam Mominka tana sonka".
tafaɗa kamar zatayi kuka, cikin dake fuska yace "kada kibari hawayennan ya zubo".
daga haka ya shige part ɗin Saif, ganinshi yana bacci yasa ya taɓe baki yashige yayi wankansa, kaya ya canza sannan ya tasheshi, "malam a tashi a kaini gida".
Saif ya murtuk'e fuska yace "har wanka kayi kakecewa nafita haka, kalan kafini kasuwa dama gaka fari".
Sadiq yayi dariya ya ce "nima bazanso nafika kasuwa ba, je kayi wankar ka k'ure adaka kafin nayi Sallah".
Dariya sukayi duka.

Comments

Popular posts from this blog

Australian Visa Application information: Visa Types & Requirements

[Sunnah] What Muslim Should Observe On The Day Of Eid

Canada Immigration: How To Apply For Canada Permanent Resident Visa