BENZEMA 4

📨📨📨📨📨📨📨📨📨📨
*BENZEMA*
📨📨📨📨📨📨📨📨📨📨
Page 4
.
.
writen by *PRINCESS ESHAT AYSM*
(AISHA BICHIKI)
.
.
DEDICATED TO
*SADIQ ABDULLAHI BENZEMA*
.
.



gmail: Eshataysm@gmail.com
📨
07014612958 for cmmnt.
Eshataysm.tk
my blog😍
.
.

✍ Cikin kulawa Ummi tace "ya kabaro su Khadijan".
Murmushi yayi yace "tana gaisheki".
zatayi magana yace Ummi naci abinci sosai".
Yafaɗa fuskanshi cike da murmushi, dariya tayi tace "Naga alama, ina Saif ɗin yake".
"yak'i shigowa, nima nazo faɗa miki zan rakashi wani wajene".
Yafaɗa yana kallonta.
"tou adawo lafiya, amma ka kula banda kai dare".
ɗan rungumota yayi yace "Ummi na girmafa yanzu, kinamun kallon yaro".
Murmushi kawai tayi tace "adawo lafiya".
Dai fita suka ci karo da me aikin Umminshi, da sauri ta tsuguna tace "saika dawo".
Da manyan idanuwansa yaɗan kalleta tacikin glass yace "menene wannan a hanunki"?
Kallon hanun nata tayi kafin tace "sak'a nakeso nakoya".
Wani kallo yamata yace "dama ana koya batareda an koyarba".
Sunkuyar dakai tayi tana muzurai, shi abunma dariya yabashi, yace "me ake sak'awa dashi"?
tace "riga, wando da yawa dai".
Shiru yayi kamar me nazari, can yace "shikenan, jeki kawai".
Cike da tunani yabar gidan, Saif ya taɓe baki yace "kaifa idan kasamu Umminka baka sanin akwai wani a gefe".
Dariya yayi yace "abun naka harda sharri fa".

Bayan shekaru 4 lokacin sungama Dgree ɗinsu na farko, babu abunda ya canza a halin Benzema saidai yasake cika ya k'ara kyau sosai, yazama matashi me cikekken kamala, wan mahaifinsa shi yaɗau nauyin karatunsa har ya kamalla, zuwa lokacin yarinyar nan me tallen doya ta girma sosai, har lokacin bata daina ɗaukan talle ba, saidai lokacin ba kasa mata akeyiba zubawa takeyi dakanta, kullum yaɗan samu kuɗiita yake tunawa, haka yake kaimata duk abunda yasamu  a sunan tausayawa a matsayinta na marainiya, gama karatunshi komai yafara kunce masa, neman aiki yakeyi sosai amma tsawon lokaci shiru, wani lokacin har interview yakeyi amma sai amasa maguɗi asaka mace a gurbinsa, gashi kullum burinsa na taimakon mata yana ransa,  Saif yayi yayi su fara aiki a kamfanin mahaifinshi tare amma sam yak'i, har faɗa sukayi akan yana k'yamar dukiyar gidansu kafin daga baya suka canza.
Wataranan Alhamis yana kwance a cinyar Ummi Saif ya shigo da farincikin sa, kana ganinshi kasan akwai magana, cikin zumuɗi yagaida Ummi sannan yajuya dubansa ga Sadiq, "mutumin kullum yaro kake zamowa ajikin Ummi".
murmushi yayi haɗi da mik'ewa yace "daga shigowarka nasan yau muna cikin farinciki, ko akwai bayanine".
Saif da murnarsa yak'i ɓoyewa yace "kataso muje Insha Allah yau zaka samu aiki".
cuno baki yayi kamar yaro yace "haka kullum kake cewa, ni na hak'ura".
Saif yasake baki zaiyi magana Ummi tace "tashi maza kuje, Allah yabada sa'a, kada ka karaya komai lokacine, kasani ko lokacinne yazo".
A kasalance ya mik'e ya tattaro takaddunsa, a hanya Saif sai so yake yasashi dariya amma fuskan a ɗaure, ta gefen ido yadubeshi yace "ɓata ran na menene".
kamar zaiyi kuka yace "Duniyarnan babu adalci".
Saif yace "uhm k'asar tamu dai babu adalci, kaidai kayi addu'a kawai, inaso kasaki ranka ko Allah zai kawo mana rahma".
daɗa tamke fuska yayi ya kauda kai, Saif yayi dariya yace "nasan abunda zaisaka dariya ai".
karya kan motar yayi yabi ta wani hanya, duk wasu mabarata da masu rauni haka yayi ta raba musu kuɗi, shidai baice komaiba duk da yaji daɗi a ranshi, har Saif yagama yadawo motar baice komaiba, taɓe baki Saif yayi yace "naganoka".
wata hanyar yabi daban, Sadiq yaɗan dubeshi yace "ina muka nufane".
Shima Saif ɗaure fuska yayi yace "inata magana kana shareni".
ɗauke kai yayi bai ce komaiba, ganin wajenda yatsayane yasa ya kalleshi da sauri, kafin yayi magana Saif yabar cikin motar, taɓe baki yayi yafara rarraba ido yana tunanin ta ina zai hangota, har yagama dube dubensa baiga me tallen doyannan ba, da sauri yafito yanufi wajen Saif ganin suna magana da wata kamar kwatance ake masa, da zummar tambayarta yafito amma ya wayince yace "malam ya zaka shanyani a mota"?
agogon hanunshi Saif yaduba yaga akwai sauran time, ɗaga masa ido yayi yace "saika fitone to, idan nashigo sai kayi tambayarka ai".
kwafa yayi sannan yabi bayanshi suka shiga, saida yaɗau hanya yace "idan iskancinka suka motsa kowa kakeyiwa, nasan yarinyarnan kaɗai ke saka dariya shiyasa nakawoka wajenta, abun haushima wai batada lafiya".
a k'ufule Sadeq yace "Amma ka cuceni, kaga kamayar dani wajen Ummina tunda rashin mutunci zakamun".
Saif yayi dariya yace "aifa".
tsaban ranshi yaɓaci kasa magana yayi, wai yarasa wacce zaice tana sashi dariya sai me tallen doyar dako sunanta bai saniba, dama k'anwarsa Khadija yace zai yadda, wani tsuka yaja dayasa Saif sake tuntsirewa da dariya, gidanda da aka masa kwatance yayi prkn, ginin lakane gidan kana gani kasan talakawane sosai, da sauri Saif yafita a motar tun kafin su fara faɗa, shikam Sadeeq hawayene yaji yafara sauk'ar masa, yana masifar tausayin na k'asa dashi dukda bashida komai, a hankali yakama murfin motar ya fito kamar me tsoron wani abu, hakanan yaji zuciyarshi ta fara bugawa, daga ɗan nesa yana hango Saif yana aika yaro, ko minti biyu ba'ayi ta fito sanye da wani koɗaɗɗen dogon riga, yau babu wannan kwalliyar tallen, fuskarta fayau da alama kukama takeyi, sai yau yagane ashe farace domin idan tayi kwalliyar sam batada alk'ibla, tana ganin Saif tawashe baki tana gaisheshi, bayan sun gaisa yamata yaya jiki, bata amsaba tace "ɗan fari me kirkirkinnan".
murmushi Saif yayi yace gashican, yanuna mata da yatsa, ya harɗe hanneyensa ya zuba musu ido dukda bayajin me suke faɗa, zata nufi wajenshi yayi saurin ciro dubu biyu a jikinshi ya mik'a mata yace "gashi yace a baki".
kamar me tsoro ta waru ido tace "Nagode amma bazan karɓaba, kaga yau babu talle yanzu Innah saita naɗa mun duka".
da tausayawa yace "ɓoyewa zakiyi ai, idan kinason wani abu saiki siya".
baki a washe ta amsa, tayi wajen Sadeeq da sauri cikin tafiyarsu irinna 'yan talle babu ko tsari, gaisheshi tayi, ya tamke fuska wai kada Saif yaga yayi dariya da ya ganta, shi kanshi Saif tamke fuskar tayi bala'in sakaahi dariya, "a tsawace yace wuce ki tafi gida to".
harta juya suka jiyo muryar Innah tana salallami, "Ashe karuwanci kikeyi dagaske Kuluwa, yau nashiga uku".
kafin kace me ta tara musu mutane awajen, Kulawa sai ɓoya takeyi a bayan Sadeeq tana kuka kamar ranta zai fita, shikam duk yagama ruɗewa sai daɗa ɓoyeta yakeyi, Innah kuwa sai bada bayani takeyi wai yagama lalata mata yarinya dole ya aureta.

Comments

Popular posts from this blog

Australian Visa Application information: Visa Types & Requirements

[Sunnah] What Muslim Should Observe On The Day Of Eid

Canada Immigration: How To Apply For Canada Permanent Resident Visa