BENZEMA 5
*BENZEMA*
.
.
writen by *PRINCESS ESHAT AYSM*
(AISHA BICHIKI)
.
.
DEDICATED TO
*SADIQ ABDULLAHI BENZEMA*
Page 5
.
.
gmail: Eshataysm@gmail.com
07014612958 for cmmnt.
Eshataysm.tk
my blog
.
.
Ina kukene masoyan wannan book na *BENZEMA*
Sak'onnin ku duk sun sameni, insha Allah gaisuwarku zai iza gareshi.
.
.
_inayinku sosai one love forever my sisters_
*SMASHER & NA'IKKE*
Allah yabarmu tare.
.
.
*my bintu*
Kina raina koda yaushe.
Up
Up
Up
*BENZEMA, ZAMU TOSHE KUNNUWANMU AKAN MASU KAWO MANA TSAIKU SUNAN BOOK D'IN, MUNA BIYE DAKE ESHAT, ALLAH YAKARA BASIRA DA D'AUKAKA*
SAKO DAGA HAJARA S ADAM.
.
.
_sak'one ga masoyina, ka dad'e acikin zuciyata, narasa yadda zanyi ka fahimta, tun farkon had'uwarmu dakai soyayya nakamu dashi, nauyin baki yahani....._
_Tunani kullum babu sake, hawaye idona yajik'e ko wani sa'i sai kamini gizo, yazam cuta gareni kagani, kaine kad'ai magani, tallafa kayo magani, kabani sonka inshigo gari, banjin dad'in labari idan ba nakaba babu tsari...._
Wannan wak'ar sadauk'arwane ga dukkan masoya ta duniya.
.
.
.
✍ Sosai Saif yake dariya kamar Allah ne ya aikoshi, ganin yanda Sadiq ya rikice yasa yad'an tsagaita da dariyar, kallon Innah yayi da taketa koro bayani wa mutane, a hankali yace "kifa iya bakinki muna ganin mutuncin manyane da baki furta kalmarnan tacewa ya lalata miki 'ya ba, mezaiyi da watsattsiyar yarinyarda babu komai a tare da ita sai tarin k'idahumanci da jahilci, Allah yabaki rik'onta don ki kare mata mutunci a matsayinta na mace amma sam bakiji tsoron Allah ba kin watsar da ita wai tana nema miki kud'i ko".
kama baki Inna tayi tana kallon Saif can tafashe da kuka, wani dattijo makwabcinsu yace "ku rabu da ita kuyi tafiyarku".
aikuwa kuluwa tanajin haka ta k'ank'ame Sadiq, cikin kuka tace "kumun rai, idan kun tafi yau kasheni zatayi".
kallonta kawai Sadiq yakeyi, fuskarsa cikeda tausayi kamar zaiyi kuka ya kalli Saif yace "na aminci zan aureta yanzu".
Da sauri Saif yace "kasan me kake fad'a kuwa, ina zaka kaita"?
cikin raunin murya Sadiq yajanye Kuluwa ajikinshi yace "kada kadamu abokina, zan aureta".
ita kanta kuluwa kallon mamaki take mishi wai cewa yakeyi zai aureta, Innah tayi dariyan mugunta tace "dayafi maka ai, yanzu ka yadda kaine ka lalata mun yarinya".
da sauri yace "nayadda".
wajen ya kaure da surutu kowa ta aibata Innah da irin mungun halinta, wasu suna alawadarai da Sadeeq, wasu kuma suna taya Kuluwa murna zata daina shan azaba a wajen Innah.
atak'aice a take aka d'aura auren da baima san wacece Kuluwar ba, tsaban bak'in ciki baiko tsaya a wajenba Saif shine yayi masa komai, abu kamar wasan yara wai anyi aure, yanacikin Mota yakifa kanshi kamar kukama yakeyi, Saif yazaga ya bud'ewa kuluwa sit d'in baya, ita kanta kuka takeyi sosai tana danasanin irin wannan rayuwar, batasan ko d'an yankan kai bane ta had'ata dashi kamar ita takawo maraici duniya, abunda taketa riyawa kenan, sit d'in driva Saif yabud'e yace "matsa kabani wani waje".
Sadiq yad'ago rinannun idanuwanshi yace "zauna can kawai zanja".
Saif ya tab'e baki aranshi yace "ba kayi haukaba, zaka auri wannan yarinyar".
d'ayan sit d'in yakoma yazauna, saida suka d'au hanya ya kalli Saif ta gefen ido yace "ina muka nufa"?
wani harara Saif ya watsa mishi yace "inda zaka ajiye wannan yarinyar don tacikamun kunne".
had'a rai Sadiq yayi yace "abunda yafito damu kenan? Kafad'amun".
Saif kamar bazaiyi maganaba, candai ya fad'a masa, jan motar kawai yakeyi yana tunanin Ummien shi, idan taji maganar baisan yaya zata d'au abunba, koda sauk'i ko akasin haka, yama manta da jan mota yakeyi sai muryar Saif yaji yana cewa "me kakeyi haka Sadiq, tsayah mana...".
cikin amo yayi maganar, kafin yataka burki sunyi gware da wata mota.
Da sauri ya sake siteriyan motar jin kanshi yayi mummunan buguwa, da sauri Saif ya rik'e kan motar ya taka burki, d'ago da kanshi Saif yayi amma yasuma saboda ba k'aramin buguwa yayi ba, a rud'e Kuluwa ta fara jerowa Saif tambayoyi, hararar ta yayi aranshi yace "duk ke kika jawo".
Shareta yayi yana shafa fuskan Sadiq yana d'an fesa masa ruwa, had'add'iyar motar da sukayi gwarenne ta matso daf da tasu motar, wata santaleliyar yarinyace ta fito a ciki, tana sanye da material maroon, fuskarta kawai Saif yatsaya yana kallo, ganin ta nufo motar yasa ya zuge glass d'in, d'an lek'awa tayi tace "Kuyi hak'uri".
murmushi yayi yace "babu komai".
Kallonta takai ga Sadeeq, fuskarta cike da tausayi tace "Ya bugune, ina zuwa".
Sake baki Kuluwa tayi tana kallonta, bata tab'a ganin k'yakk'yawa irin wannan yarinyar ba, ko minti d'aya bata kaiba sai gata da wasu maza a bayanta, ji kawai Saif yayi tana cewa kuyi hanzarin kaishi asibiti ya bugune".
Saif zaiyi magana ta d'aga masa hanu cikeda isa tace "kuyi hanzari".
D'aya yazaga ta b'angaren Sadeeq d'in yafara k'ok'arin ciroshi Saif ya daka mishi tsawa, murmushi tayi tace "Baka yadda damu bane".
ta kallesu tace ku koma mota, kallon Saif tayi tace "muje to, kayi hak'uri mukaishi asibiti kaga yanacikin wani hali".
kai kawai ya gyad'a mata kafin ya tada motar, kallon Kuluwa yayi ta madubi yaga yanda taketa faman hura hanci tana muzurai, dagani a tsorace take, baisan lokacinda yafara kwasan dariya ba.
Bin motar su yarinyar yayi yana tunanin tabbas yasan fuskar amma baisan a ina bane, hankalinshi nakan Sadeeq har suka faka a wani babban asibiti, idan baka sanibama zakace gidan wani me kud'ine, taimakom gaggawa aka bashi yayinda suka bar Kuluwa a mota, cikin lokaci kad'an ya farfad'o, ji yayi kanshi yayi mishi nauyi, ya runtse ido yana kallon Saif, a hankali yace "mutuwa mukayi ko, dama nasan tunda na auri yarinyar nan dole na mutu, mutuwar ma yafimun da wannan rayuwar".
Saif ya gintse dariyarshi yace "tare kuka mutu da ita ai, itace matarka ananma".
Wani b'ata rai yayi yace "kai kajamun, ina zaune a jikin Ummiena kajamun masifa"
dariya Saif yayi yace "dallah kamun shiru, wayace ka amsa..?"
nuna masa yarinyar yayi yace "idan ka warware kafad'a kana b'atawa 'yar mutane lokacine".
kanta yana sunkuye akan wayarta, da alama batama san mesuke fad'aba, kallonta Sadiq yakeyi babu ko k'yaftawa, a hankali yace MASHA'ALLAH,
bakinshine kawai ya motsa babu wanda yaji me yace, dubansa yakai ga Saif yace "ka mayar dani gida na warware".
ficewa Saif yayi zai k'ira likita, cikin nutsuwa ta zare siririn glass d'in idonta ta matsa daf dashi, hanunta takai kan goshinshi ta d'an tab'a, cikin tausayawa tace "kanka babu zafi, ka warke ko"?
lumshe ido yarufe idon gam, wayartane ta hau ruri, da sauri ta kara a kunne, da muryarta me sanyi tace "Dad ina zuwa yanzu".
shiru tayi tana sauraran magana, kamar zatayi kuka a shagwab'e tace "Haba mana Dad yanzu zan dawo ku jirani".
kallon Sadeeq tayi kamar zatayi kuka, saikuma taciro wani card a handbag d'inta tare da kud'i, a wajen ta ajiye masa batace komaiba tafice da sauri, bin bayanta yayi da kallo, yad'an lashi leb'enshi tunowa dayayi da abunda ya faru dashi yanzu.
Comments
Post a Comment