BENZEMA 6

��������������������
*BENZEMA*
��������������������
Page 6
.
.


I must say thanks 2 dis wndrful people, u guys ar awesome, Ilysm u made me happy tnkieh much again sisters
*KAIRIYYA & MUFIDA*

.
.

writen by *PRINCESS ESHAT AYSM*
(AISHA BICHIKI)

.
.

DEDICATED TO
*SADIQ ABDULLAHI BENZEMA*

.
.





gmail: Eshataysm@gmail.com
��

Eshataysm.tk
my blog��

.

.





Sai kusan azahar suka bar asibitin, har sun manta da wata wai kuluwa, a kwance suka sameta tana sharar baccin ta, murmushi kwance a fuskar Sadeeq yace "kana nufin bakasan inda zaka kaita ba"?
kallon ka rainamun hankali Saif yayi masa, "dayake ni na aureta ko, ka saketa yanzu kaga idan ban mayar da ita inda tafito ba".
Girgiza Kai Sadiq yayi yace "zan saketa! amma sai tasamu 'yanci, mata ba'abun wulak'antawa bane, zanyi k'okari naga ta fita acikin maraicinnan, matsalata d'aya Ummina".
Saif baice komaiba yaja motar, saida suka d'au hanya kafin yace "zamu bari gobe idan Allah yakaimu mu mik'a takaddunnan, yau lokaci ya tafi".
b'ata rai sadiq yayi yace "Allah yakaimu".
bawanda yasake magana har suka isa, kowa da abunda yake sakawa aranshi, Saif ne yafara fitowa yace "ja matarka ku tafi".
dariya Sadiq Yayi yace "wai mata, kafa fara rainani". dariya shima yayi ya shige cikin gidan yana k'walawa Ummi k'ira.
kallonta yayi for a scnds ya kauda kai, har ranshi yakejin zafin auren amma kuma yana tausayin ta, k'afarta
yad'an buga ta mik'e da sauri tana zare ido, had'e rai yayi yace "fito".
da sauri ta fito tana kallonshi, gaba yayi tabishi a baya har suka shiga, dai dai lokacin ta fito tana cewa "wannan k'ira haka Saif, dama abun arzikine".
ganin sunyi cirko2 awajen yasa tace "yau kuma".
susa k'eya Sadiq Yayi Yace "mundawo Ummi".
Ta fad'ad'a fara'arta tace " Allah yasa andace, amma naganku tare da bak'uwa ku bata wajen zama mana".
kallon kallo sukayi sannan yadubi kuluwa, kana ganinta kasan a razane take, harara ya watsa mata yace "mahaifiyata ce".
da sauri ta tsuguna tagaisheta, cikin zuciyarta tana mamaki, ta d'auka d'an gidan wani shahararren me kud'ine ganin yanda yakeda kyauta, uwa uba fatar jikinsa kamar ka tab'a jini ya fito, kallon kyakkyawan fuskarsa tayi, cikin zuciyarta tana harbawa batasan daliliba, cikin nutsuwa Ummi tace "atsaye zakuyi ta tsayuwane, wacece ita".
da sauri Saif Yace "ni Natafi dama akan hanya nake".
hararar shi Sadiq yayi yace "baka isabafa malam, ni kad'ai zanyi bayani ne"?
dariya Saif yayi yace "wlh sauri nakeyi tun a hanya kana gani Mom tana k'irana kaima kasan da matsala idan nakai minti 2 banjeba".
yana fad'in haka ya fice da sauri yana dariya, shima sadiq d'in binshi yayi harda d'an gudunshi kada Ummi tak'irashi, kama baki ummi tayi tace "yarannan anya sunada gaskiya". kallon kuluwa tayi tace daga ina?
zare ido tahauyi can tace "anjuma zantafi".
duk da bata fahimci inda amsar ta dosa ba tayi murmushi tace "zauna to".
abinci takawo mata sannan ta buk'aci tanaso tayi sallah.
sukam suna fita sukayi ta kwasan dariya, a hanya Saif yace "kamata yayifa kafad'a mata gaskiya kawani biyoni".
"a'a kai yakamata kamata bayani, ba lallai ta yadda daniba".
kad'a kai Saif yayi yace "wlh sai yanzu nahango matsala, ta ina zamu fara bayanin to, me yakaimu gidansu"? shiru sadiq yayi kamar me nazari, can yace "kaine kajawomun, amma zan rama". dariya Saif yayi yace "kwanannan zaka haifa fa ko, dama wuyanta aurene, gaskiya kayimun wayo". duka yakaimishi yanajan Allah ya'isa.
a falo suka tarar da
Mom kamar kullum, ko kallonsu batayi ba ta amsa gaisuwar su, irin wannan halayyar tata yasa Saif yakejin inama Ummi Itace ta haifeshi.
shigewa ciki sukayi, suka nufi inda zai sadaka da part d'in Saif, ko zama Sadiq baiyiba yace "yau khadija na batanan, gidan bako dad'i".
tsaki Saif yayi yace "saika bita ai".
wasa wasa sai dare yamayar da Sadiq gida, d'akinshi ya wuce harda sand'a, baccinma kasa zuwa tayi, da asuba kuwa yagama shirinsa tsaf, k'arfe 6 ya lek'a d'akin Ummi, Tana zaune tana jan carbi, kafin tayi magana yace " Ummiey sauri nakeyi da wuri akace mukoma, saina dawo zamuyi magana".
harya fita yasake dawowa yad'an lek'a kansa yace "ki kula da yarinyarnan fa kada ki bari ta fita".
da gudu ya fice yabar Ummi da salallami, a gidansu Saif Ya karya sannan suka nufi inda zasuje.
Babban wajene sosai kana gani kasan ma'aikatan bana wasa bane, wani katafaren office suka shiga, yanada girma sosai, matane guda biyu sai namiji d'aya, da alama suma aiki suke nema, sunanan zaune har mutuminda suke jira ya iso
Da Sauri wata ta mik'e ta shiga, ba'a jumaba tafito fuskarta fal farinciki da alama tasamu, sauran biyunne suka shiga, a hirar dasukeyine yagane sud'in 'yan uwan mutuminne.
basu juma da shigaba wani k'amshi ya gauraye wajen, k'arar takalmi kawai kakeji kmar zai fasa wajen, d'agowa Saif yayi da sauri, da sauri ya tab'a Sadiq "wannan ba yarinyar jiyannan ba?".
kallonsu Sadiq yayi a fakaice, su biyune sun had'u sosai, yana ganinta ya ganeta, sam basu burgeshi ba, yadai san bai tab'a ganin kyakkyawa irinta ba, tab'e baki yayi, ya mik'e ganin wa'inda suke ciki sunfito, kallo d'aya yayiwa mutumin yagane bashida mutunci, addua yayi akan Allah yad'aurashi akansa yasamu aikinnan.
takaddun sunyi kwau sosai, shi kanshi mutumin yaji dad'i ganin inda ya amsa duk tambayar daya masa, hanu yamik'a masa sukayi musabaha, kamar daga sama aka bud'e k'ofar, wacce suka shigo yanzune, cike da mad'e ta kalli mutumin tace "barka da aiki, wlh sauri mukeyi ina fata Dad yamaka bayani"?
shiru mutumin yayi can yace "don Allah kiyi hakuri
bakizo ba tun jiya yanzu kuma kinga wannan ne nak'arshe angama d'iba". wani kallo ta watsa masa, da sauri yace "imm malam Sadiq kaje za'a nemeka wani lokaci, kaga yanzu angama d'iba".
cikin b'acin rai yace "kasan me kakecewa kuwa".
watsa mai takaddun hannunta tayi tace "ni natafi, kayi hanzarin soke sunan wannan kasaka nawa".
binta da kallo sadiq yayi cikeda tsana, halayyarta da maganarta bana mutanen arziki bane, ita kuma wacce suke taren akwai tsananin tausayi a tare da ita, dukda baisanta ba yayi imanin da itace da bazatayi hakaba, ganin zai b'ata lokaci yasa yamik'e da sauri ya fice, hangosu yayi harsun fara gangarawa akan step d'in, cikin zafi yadaga musu tsawa, cikin sakwanni ta ganeshi, da dariya tace "ashe ka warke, nakoma bansamekuba, sadiq ko? ni sunana Elham, me kukazoyi anan..."
katseta yayi dacewa nagode sosai elham.
Saif ne ya iso wajen yace "baka fad'an komaiba kazo nan, ashe kaganeta".
tsaki yayi yace "yanzudai naganeta, na biyo wannan kidahumanne, me kike nufi da'a soke sunana"?
Elham takama
baki don tasan halin Nusiey batada adalci a rayuwar ta, musamman idan tanason abu, Saif yadafashi yace "kayi hak'uri yanzu nagane me tayi, kasan halin k'asar tamu, komai saidai su d'aura nasu akai ko kuma subi son zuciyarsu, basu duba wanda ya cancanta, shiyasa zakaga masu ilimi suna zaune jahilai suna sama, wannan bashi zaisa mu karayaba, indai ina raye kaima kana raye sai ka cimma burinka na taimakon al'ummah, saika zamo wani abu, sai kazamo jagoran dubban al'ummah".
share hawayen da yad'an gangaro masa yayi na tausayin abokin nashi.
jikin Elham duk yayi sanyi, a hankali tace "idan bazaku damuba zan had'aku da Dadyna".
Wani Kallo Nusy tayi mata tace "to me dady, mezai masa".
ta kalli Sadiq tace "yanzu nagane kai k'aramin mutum.. bata k'arasaba Saif ya wanka mata mari.
baki don tasan halin Nusiey batada adalci a rayuwar ta, musamman idan tanason abu, Saif yadafashi yace "kayi hak'uri yanzu nagane me tayi, kasan halin k'asar tamu, komai saidai su d'aura nasu akai ko kuma subi son zuciyarsu, basu duba wanda ya cancanta, shiyasa zakaga masu ilimi suna zaune jahilai suna sama, wannan bashi zaisa mu karayaba, indai ina raye kaima kana raye sai ka cimma burinka na taimakon al'ummah, saika zamo wani abu, sai kazamo jagoran dubban al'ummah".
share hawayen da yad'an gangaro masa yayi na tausayin abokin nashi.
jikin Elham duk yayi sanyi, a hankali tace "idan bazaku damuba zan had'aku da Dadyna".
Wani Kallo Nusy tayi mata tace "to me dady, mezai masa".
ta kalli Sadiq tace "yanzu nagane kai k'aramin mutum.. bata k'arasaba Saif ya wanka mata mari..

Comments

Popular posts from this blog

Australian Visa Application information: Visa Types & Requirements

[Sunnah] What Muslim Should Observe On The Day Of Eid

Canada Immigration: How To Apply For Canada Permanent Resident Visa