NI AYS NAKE SO 40


       *NI AYS NAKESO*
                 
Page 40
.
.
.

_WRITEN BY Princess Eshat Aysm_
.
.
In Dedication to *ABDULLAHI YAHYA SA'AD ZARIYA*
A.Y.S





.


.
.


Wani irin k'ank'ameta yayi yanajin wani irin sonta a cikin jikinshi, bakinshi yana ɓari yace "Aisha, nagode da Allah yasamun soyayyarki a raina, ban taɓa nadamar sonki ba, keɗin alkairice agareni, bansan da wani kalma zan furta wajen bayyana miki irin tsananin k'aunar da nake miki ba, saidai zan kula dake fiye da komai a rayuwata, zan soki ke kaɗai, bazan taɓa son wata ba, wannan shine tukuicin ajiye soyayyata a ranki da kikayi, zamu kasance tare daga mu sai yaranmu".
Ya k'arasa haɗe da kashe mata ido yana murmushi, kanta ta cusa jikinshi tana dariya zuciyarta fal farinciki, ya ɗan ɗago kanta yace "kiss me".
Rufe idon tayi tana dariya, ya sake marairaicewa yace "kiss me mana babe".
a hankali ta buɗe idonta ta zubasu akanshi, hancinta ya lakuce yace "ko namiki kyau ne..."
Bai rufe bakinba ta ida nata a ciki, cikin wani irin salo tafara juya bakin acikin nashi, numfashi yafara sauk'ewa da sauri da sauri, ji yake kamar numfashinsa zai fita, gaba ɗaya ta gama ruɗashi, ya gama fita a hankalinshi, cikin zak'ewa yafara k'ok'arin zare kayan jikinta, ta kama hanunshi da sauri ta ce " *AY* bacci nakeji".
idanuwansa a kaɗe yace "kinma isa Esha,, bazan miki komaiba, taso kiga".
mik'ewa yayi tabishi, caraf ya rik'ota ya matseta ajikinshi, kayan jikin nata yacire, kamar zatayi kuka ta ɓoye cikin kirjinshi, nan yasamu daman wasa da ita son ranshi, dak'yar suka iya kwanciya saboda duk sun kashewa juna jiki, ya rikitata da salonshi, burinta kaɗai ya kusanceta duk da tana tsoron azabar datasha ranar farko, daren Ranar yazamto daren tarihi agaresu, darenda yakasance me tarin ni'ima agaresu, su biyun sun ɗanɗani zuman juna kamar kada gari yawaye jikinsu ya rabu sukeji, ririta kam tagani kamar bawacce ta taɓa sa'an miji kamarta haka takeji, dab asuba yayi musu wanka sukayi Nafila tareda godiya ga Allah, sun daɗe suna karatu sannan suka kwanta bacci me nauyi ya ɗaukesu.
.
.
.
Watanni biyu Unaisa tana wankau a gidan da take ganin tsangwama, haka ta daure harta tara kuɗin dazai kaita Nigeria, ranar Lahadi kuwa ana bata na watan ta haɗa da sauran da take tarawa ta nufi Nigeria da k'aton cikinta, ko gidansu bata nufa ba, dukda taji labarin iyayenta suna nemanta.
isarta gidansu Faruq saida yasauk'ar mata da wani sanyi aranta, kai tsaye falon Momi ta nufa, babu kowa aciki sai Sadiya tana shan kankana hankalinta yanakan film ɗin datake kalla, Sallamar Unaisa yasa ta ɗago tareda amsawa, Unaisa ta zauna a ɗaya daga cikin kujerun mamaki k'arara a fuskanta, idan bata mantaba wannan Sadiya ce k'anwar Aisha, tana ganin suna zuwa lokacin da take gidan, gashi yanzu ta ganta harda ɗan cikinta dayafara ɓullowa, ko kallonta Sadiya bata sakeyi ba, Unaisa tace "ina masu gidan"?
kallon ko inkula Sadiya tayi mata tace "akwai wata kuwa bayan ni".
da mamaki Unaisa tace "ke ba k'anwar Aisha bace, matar yaya Faruq"?
da sauri Sadiya ta ɗago tana kallonta, har lokacin bata ganeta ba, ta yamutsa fuska ta ce "ashe kin sanni ma".
shiru Unaisa tayi baki buɗe tana kallon Sadiya.
bawanda yasake magana, Faruk ne yashigo da alama daga masallaci yake, hankalinshi nakan Sadiya, baima lura akwai wata a wajenba, kusa da ita yazauna yana kallonta, yace "babyna yayi kukan raahina ko".
jikinshi ta shige kamar zatayi kuka tace "nima nayi".
Ya shafa fuskarta zaiyi magana Unaisa tace "Yaya ina wuni"!

Comments

Popular posts from this blog

Australian Visa Application information: Visa Types & Requirements

[Sunnah] What Muslim Should Observe On The Day Of Eid

Canada Immigration: How To Apply For Canada Permanent Resident Visa